P83

397 39 12
                                    

💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)

By
*Salmerh MD*
 

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *83*

Noor kam dama tun washegarin 'kiran da yayi mata tace da Ammi zata gidan Ummah ta kwana biyu, tayi hakan ne dan gujewa ha'duwar su musamnan ma da yake bata san actual ranar da zai zo 'din ba.

Cikin sa'a kuwa Ammi bata hana ta ba cuz duk abinda take so shi Ammi ke yi mata bata takura ta.
Dan ita Ammi gani take tamkar duk masu laifi suke agare ta tunda su suka aura mata 'dan su.

So wannan dalilin ne yasa ko da suka zo ma basu ha'du ba, Ammi gaisuwan Safwan ka'dai ta amsa daga haka ta tashi ta shike ciki kamar wacce taje 'dauko abu amma suka ga shiru kusan mintina talatin bata ba labarin ta bata kuma le'kowa ba.

Yah Deen kam bai yi mamakin hakan ba yayin da Safwan ke tunanin 'kila Ammi ta manta da su ne ma.

Deen kam har zuciyar sa yake jin babu da'di dalilin ma kenan da yasa tun tahowar su bai 'kira su a waya ba cus yana da ya'kinin ba sauraran sa zasu yi ba....jikin sa sanyi 'kalau ya tashi ya shiga 'dakin ta..har zuciyan sa baya ganin laifin su cuz yasan koma menene shi ne ya jawa kansa.

Zaune a bakin gado ya same ta hannun ta Qur'ani ne take karanta shi, tayi hakan ne kuma  dan ta samu sau'kin abinda take ji a zuciyar ta  musamman game da shi.

Tana jin yana sallama amma bata ko 'dago ba balle ya sa ran samun amsawar ta.
Ammi kam ganin ya shigo 'din bai sa ta fasa karatun ta ba.

Tsayuwa ya cigaba da yi yana tunanin ta inda ya kamata ya fara.

Ammi kam sai da ta dire suratul Rahaman 'din da ta fara sannan ta rufe Al-qur'anin tare da kawar da kanta gefe, batare da  ta dube shi ba cikin sanyin murya tace da shi" Sakin 'yar tawa kazo ka kawo min ko kuwa rainin hankali ya kawo ka...?"

'Karasowa yayi gaban ta ya dur'kusa yana shirin kwantar da kansa saman 'kafarta tayi saurin mi'kewa tsaye tana duban sa kamar ba ta sanshi ba.

Sam bai yi mamaki ba dan ya shiryawa fiye da hakan ma idan zasu mishi matu'kar za'a bashi matar sa bazai ji ciwon komai ba.

Da raunin murya sosai yace
" Ammi na..am ur Mu'een fa...".
" Ai bani da idanu...".
" Ammi dan Allah ki yi ha'kuri ki yafe min, Ammi ni kaina ban ji da'din faruwar wasu abubuwan ba amma sun riga sun faru kuma wallahi nayi regretting komai, Ammi ki fahimce ni dan Allah, nayi miki al'kawarin hakan bazai sake faruwa ba..sam bana jin da'din wannan fushin da kuke yi da ni Ammi...da wanne zanji? Ammi duk kun guje ni har Uncle Ja'afar baya 'daga 'kira na, Anty Zainab haka, Alhaji Baba kam bama zan fara ba,  Ammi idan kowa ya guje min ai ke bai kamata ace kin goya musu baya ba...nayi ciwo kamar zan mutu amma babu kowa nawa da ya nuna min tausayawa Saif ne ka'dai, hakan ba 'karamin damuna yayi ba duk nasan shima Saif 'din kawai ne, Safwan ka'dai ke 'dawainiya da ni..wallahi da kaina kunya nake ji sosai idan na tuna ni na jawa kaina...kamata yayi ace zuwa yanzun kinfi kowa fahimtar nadama ta Ammi, ke kika haife ni kinfi kowa sanin ciwo na...Ammi fushin ku sosai yake hanani sukuni duk wayewar gari da damuwa nake sake yini ina jin babu da'di, tsoron ta yanda zan sake tunkarar ku shi ya hanani zuwa gare ku da wuri, dan Allah Ammi ku tausaya min ku yafe min laifukana.....".
Ya karashe maganar hawaye na taruwa cikin idanun sa sai ya sunkura da kansa.

NOORUL✔️Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang