P30

439 28 1
                                    

💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)

By
*Salmerh MD*

 

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_Ina son ku masoyana_ 😍 _...Allah ubangiji ya haskaka rayuwar ku da mafi alkhairi daga cikin alkhairai_ 👏🏻

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *30*

........'Bangaren Alhaji Baba kuwa...a yau 'din duk ya kasa sukuni, damuwar sa ta yawaita sosa...tunanin sa ta yanda Mu'een zai kar6i zancen ne, tun ranar da Yah Deen ya bashi amanar ta ya fahimci tsantsan son da yake yi mata cikin idanun sa da kalaman sa ya fahimci hakan, babban abinda yasa ya 'kara gaskata soyayyar tasa ma shine da har Yah Deen ya iya manta dangantakar da ke tsakanin su matsayin sa na mahaifi agare shi, ya iya duban tsaban idanun sa ya ha'da shi da amanar kula masa da ita, ha'ki'ka hakan ka'dai ya wadaci koma waye fahimtar tsantsan son da Mu'een ke wa marigayiya AMINA...musamman idan kasan halin sa cewa bashi da rashin kunya sam a rayuwar sa.

      Alhaji Baba lambun sa ya tafi yaje ya ke6e kansa guri guda yana tunani, sai dai daga 'karshe dole ya watsar da batun ya cigaba da harkokin sa.

        Shigan yamma Mu'een yayi dan kuwa 'karfe biyar da 'yan mintina ya shigo garin...fuskar sa cike fal da fara'a tamkar bashi ba, ya 'kara kyau da girma, dama gashi dogo ne shi ba laifi sai gaba 'daya ya juya ya koma tamkar 'dan shekara talatin da haihuwa.

   Ni kaina lokacin da na gansa tsaye a 'kofar shigowa parlourn bangane shi ba, saboda kwaftareren ba'kin gilashin dake manne a idon sa, shima kuma bai yi min magana ba tunda yayi sallama ya dire jakar sa a wurin sai ya yaja ya tsaya yayi shiru.

" saif!...Saif!!...Zaidu!!!"
Na fa'da da 'karfi cike da firgici ina 'dan jan baya dan harga Allah tsoro ya bani, ban kuma kawo akaina shi bane saboda nasan shi baya murmushi haka siddan sai da dalili 'kwak'kwara.

Ammi da Saif duk lokaci guda suka bayyana suna tambaya ta saboda jin 'karan 'kiran sunayen da nayi kuma nayi da 'karfi, sannan da tsoro nayi.
" Wai me ya faru ne?"
Saif yace yana kallo na, yayin da Ammi ta ce dani " Hudah Lafiya kike faman ihu?"

Ban bawa kowa cikin su amsa ba illa hanyar 'kofa da na nuna musu da hannu na wanda sai a lokacin suka lura da shi.
    Still yana nan tsaye with smile on his face yake duban mu da karkataccen wuya.

Saif murmushi yayi yayin da Ammi tace da shi " 'kaniyar ka Muhammad!"

Cikin marairaita yace " haba Ammi daga isowa ta ?"

" me yasa zaka yi tsaye acan to har kana firgita min yarinya?"
Murmushin sa ya 'kara fa'da'dawa sannan yace " Ni fa Ammi ke kawai nake jira ki taroni".

Ido Ammi ta 'dan zaro tare da fa'din " daga zuwan na ka zaka fara ko?"

Ganin bata da niyyan zuwa ne ya sanya shi tahowa inda take yana kwa6a fuska.

Ni kam da kallo kawai nake bin sa ina mamakin sa ayau 'din gaba 'daya ya canza min.

Saif ne ya girgiza kansa shima cike da jin dadin ganin 'dan uwan sa tare da wucewa inda jakar sa take ya 'dauka ya wuce da shi cikin 'dakin sa.

Ammi kuwa hannun sa ta kama kamar 'dan goye ta jashi zuwa kan kujera mai zaman mutun biyu ta zaunar da shi kan kujera....da yaran su na Igbo tace da shi " Sakalcin yau ya motsa kenan?...baka ganin 'kannen ka na kallon ka ne?"

NOORUL✔️Donde viven las historias. Descúbrelo ahora