P78

491 37 16
                                    

💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)

By
*Salmerh MD*
 

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *78*

Zaune ya tashi yana kallon 'dai'daikun mutane da ke wucewa lokaci zuwa lokaci wasu na shiga yayin da wasu ke fita, kowa fuskokin shi na tafiya ne da yanayin sa, idan yaga mutun na farin ciki sai yaga kamar shi bashi da damuwar komai ne, ji yake dama ace shine yake wannan farin cikin, yayi Allah wadai da rayuwar sa yafi a 'kirga, idan ya tuno Baby kawai sai ya rintse idanu, tausayin yarinyar yake ji sosai.

Yasan da ace tasan halin sa zai iya ja mata wannan abin da ko abaya ma bazai samu ko quartern 'kauna daga gare ta ba, amma yarinyar sosai take ji da shi matsayin sa na mahaifi agare ta amma bai yi wa rayuwar ta adalici ba sam...Allah sarki Mama na, ki yi ha'kuri, ki yafewa Daddyn ki ba dan ya na da wanna matsayin sa ba.

        Dishi-dishi yake gani idanun nasa zogi sosai suke yi masa, kansa ciwo ga kuma 'kirjin sa dake barazanar tarwatsewa...shi ka'dai yasan me yake ji a jikin sa...banda yafiyar Ubangiji babu abinda yake iya furtawa.

A duk lokacin da ya tuno ta'asar da ya tafka a fili zakiji ya furta _Astaghfirullah_ ...lokaci- lokaci yake furta hakan tamkar zautacce.

Ya 'dauki tsawon lokaci a ahakan kafin ya koma da kansa ya kwantar...ya cigaba da danasanin rayuwar sa kaf.


*****
      Misalin 'karfe sha 'daya da rabi su Alhaji Baba suka iso, duk neman da Safwan yayi wa Mu'een cikin asbitin amma bai gansa ba, yayin da hankalin mahaifan sa ya 'kara tashi sosai fiye da ganin Jasmine da suka yi da halin da take ciki.

Tsoron su kar wani abin ya same shi a inda babu wanda ya sani dan tun jiyan Safwan ya sanar da su halin da shima yake ciki..shiyasa hankalin su ya kasa kwanciya.
Yayin da Safwan kuma ke fargabar kar mahaifan nasa suga kamar bai ri'ke musu amana bane cuz Jiyan a hannun sa Alhaji Baba ya mi'ka ragamar komai a fa'dan sa wai kafin su iso.
Sai gashi sunzo in kuma babu Mu'een babu alamar sa.

Ammi kam kuka sosai take yi dan harga Allah hankalin ta bai kwanta ba, gashi sunzo kuma suna tarar da jikin Baby yayi tsanani, ko ganin ta da kyau ma basu samu daman yi ba aka fito da su waje likitoci biyu Safwan da wata Nurse suka tsaya akanta...shikansa hankalin rabe yake gida biyu ciz yasan duk inda Mu'een yake to cikin wani matsanancin hali yake.

Jikin Baby sai rawa yake yi ga wani zazzafan zazza6i da ya taso mata lokaci guda, takan 'dan fizgi jikin ta lokaci zuwa lokaci kamar mai razana da wani abu.

Noor ma kuka kamar ranta zai fita, haka ma Ammi da abin ya zame mata biyu ga rashin ganin Mu'een ga kuma jikin Baby da yayi tsanani, tasan jinyan Baby ne ya tashi hankalin Mu'een shiyasa yayi nesa da inda suke, dayake tasan irin 'kaunar da yake mata, duk wanda yasan Mu'een to yasan irin soyyayar dake tsakanin sa da Jasmine ba na wasa bane, wanda ko wani irin hali ya shiga saboda ita ba abin ayi mamaki bane, gashi tasan yanda yake fama da ciwon sa idan ya motsa masa sosai hankalin ta ya tashi ta kasa natsuwa, Alhaji Baba ka'dai da Mummyn Safwan sune masu 'dan natsuwa har ma suke iya basu ha'kuri...Noor ma ba'a cewa komai.

Safwan na gamawa da Baby ya fito ya 'kara kwantar musu da hankali da tabbacin komai zai daidaita da iznin Allah sannan yayi gaba dan shima zuwa lokacin hankalin sa ya tashi sosai, har gida yaje ya duba amma bai tarar da Yah Deen ba, sam ya rasa ina ya tafi a ina zai same shi, gashi kuma motar na nacan a Parking space cikin asbitin inda ya ajiye tun jiya anan take bata motsa ba.

NOORUL✔️Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang