P42

522 30 1
                                    

💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)

By
*Salmerh MD*

 

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

🤞🏻
~KE TA DABANCE NUSEE TA, ALLAH YA 'KARA DAN'KON 'KAUNA...SOSAI NAKE JI DAKE HAR CIKIN JINI NA....~
🤞🏻
~MASOYIYA NANAH INA GODIYA SOSAI,  'KAUNAR KI A KULLUM SAKE YA'DUWA  YAKE YI CIKIN ZUCIYA TA~ 😍

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *42*

  Yana isa gida ya sanya wayar sa a caji tare da kunna ta, nan take kuwa sa'konni suka dinga shigowa amma ko bi ta kansu bai ba balle ya karanta abinda suke 'kunshe da shi.

Cajin awa 'daya wayar tayi sai ya cire ta, number Unlce Ja'afar ya fara dialling inda ringing 'daya ya 'daga kamar dama can zaman jiran 'kiran yake yi.

Ko amsa sallamar da Yah Deen ke yi masa ma bai yi ba kawai ya fara zazzaga masa masifar kashe waya da yayi tsawon kwanaki.

Yah Deen kam ha'kuri ya dinga bashi cikin kwantar da murya tare da shirga masa 'karyar baida lafiya ne shiyasa, burin sa kawai yaji ko Uncle Ja'afar na da masaniya akan abinda ya farun tare da son sanin ko yasan 6oyayyen shirin Alhaji akan sa....yayin da a masifance Uncle Ja'afar yace da shi " Da baka da lafiyan kuma ka sanar da ni ne?"
" So sorry bazan sake ba Uncle".
'Karamin tsaki yaja tare da fa'din ya jikin to?"
" Ai ina jin muryar ka na warke kamar ba ni ba".
Cewar Yah Deen yana 'dan smilling da bai wuce kan fuskar sa ba.
" 'Karyar banza sai kace ban san halin ka ba Mu'een".
Yah Deen 'yar dariya kawai yayi batare da ya 'kara fa'din komai ba.
Uncle Ja'afar ne ya sake fa'din"...ya batun school kuma, hutu ya 'kare ko?"

" Erh mun kusa komawa Insha Allahu 'karshen week 'din nan ma...ina Aunty na?"
Ya 'karashe da tambayar sa Anty Zainab.
Ja'afar kam yana shirin yanke 'kiran yace" Hala manta sunan da kayi saving number 'din ta a wayar kayi".
Bai sake sauraran jin komai daga gareshi ba kawai ya yanke 'kiran yayin da Mu'een ya bi wayar da kallo da mamakin rashin jin wani abu daga bakin sa da ya danganci damuwar da ke damun sa.

Ga dukkan alamu Uncle J bai san komai kan lamarin ba tunda baiga alamun hakan ko cikin kalaman sa ba.

Murmushi ya saki na jin da'din rashin sanar da Uncle J da Alhaji bai yi ba, nan take yana murmushin ya 'kira layin Antyn sa Zainab inda suka gaisa cikin sakin fuska da walwala itama tana mai mitan rashin samun wayar sa cikin kwanakin.

      'Karyar da yayiwa Uncle Ja'afar itama shi yai mata sai dai ita kam cewa tayi" Ya Ammi bata sanar da ni batun rashin lafiyar ba kuma?"
Ai da sauri ya bata amsa da fa'din" May be mantawa tayi Anty".
" Ammin ce zata manta da batun jinyar ka Mu'een?"
Anty Zainab ta tambaya mamaki bayyane cikin kalaman ta haka ma kan fuskar ta.
Sai yace
" Gashi kuwa, Anty ai babu mamaki...kinsan Ammi tunda ta samu wannan yarinyar ta daina so na, kullum masifa take min ban isa ko aikan yarinyar nayi ba sai ta tsigale ni".

Dariya Anty Zainab tayi tace" k'ilan kana muzguna mata ne shiyasa Ammi take yima haka amma ai yarinyar bata da matsala a yadda na fahimce ta".
Yace
" Ke de Anty kiyi shiru kawai amma ni da nake tare da su ni zan bada labari...".
Taran sa tayi da fa'din
"....Ai gaskiya ne Mu'een...ni dama nake cewa zan ro'ki Ammi ta bamu aron yarinyar danni fa tayi min gaskiya ina son ta sai mu zauna tare dukkan mu idan mun dawo Bauchi".
'Dan 6ata rai yayi yace " Anty ni kuma fa?"
" Har da kai ai sai kazama yayanta inda rabo kuma watarana da iznin Allah sai ka zamo mijin ta na har abada".
Da wuri ya furta " God forbid...Allah ya sawwa'ka Anty ina zan kai ta ni kuma?"
Zaro idanu Anty Zainab tayi tace masa" Inda ya dace da ita mana, jimin yaro da shiririta, har haka zaka ce Mu'een an gaya ma ana gayawa Allah yadda zaiyi ne?"
" Ni dai please Anty ki bar zancen nan...shima Allah zai kiyaye bazai bar hakan ya faru ba".
Anty cewa tayi " Ni dai da za'a ban za6i Allah ita zan za6a ka maka dan nasan ba 'karamin sa'a zakayi ba da samun ta".
" Hasara dai".
Ya fa'di 'kasan ma'koshi amma Anty sai da ta jiyo shi.
"...Hmm...Fatana ni dai a kullum inga ranar da za'a ce wannan yaron nawa na fama da zuciyar sa akanta..."

NOORUL✔️Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang