P44

455 27 0
                                    

💕 *NOORUL* 💕
(Haske nah)

By
*Salmerh MD*

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

Masoya na godiya nake sosai Ubangiji Allah ya cika muku burikan ku na Alkhairi😍

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *44*

Hakan da yafarun ne ya 'kara fahimtar da shi irin 'kuncin da ya sanya Alhaji Baba ciki, gashi dai zai amsa sallamar sa da gaisuwar sa har ma wani sa'in zai 'dan ja shi da hira amma wannan fara'a da sakin fuskan sam babu su.

Tafiya yake yana tunanin abinda zai biyo baya...ya riga ya san zancen auren nan babu fashi tunda har Alhaji ya iya furtawa ga Uncle J, ya san babu mai iya dakatar da shi, cuz tun sanin da ya yiwa mahaifin nasa ya san shine akan magana 'daya tak, duk da'din da kuke da shi kuwa baka isa ka sanya shi canza ra'ayin sa ba, he is the man of his word bashi magana biyu.

Sanin haka ya sanya shi fatan Allah dai yasa ba Husnah bace Alhajin yake shirin aura masa ya kuma sa ba irinta bace ma kwata-kwata, bashi da mafita a yanzu illah komawa ga mahalicci ya ro'ke sa..ko zai tausaya masa ya canza ra'ayin mahaifin nasa.

Da isar sa gida sai ya sa6i jakar sa a kafa'dar sa ya fito tare da kulle ko'ina na gidan yayi gaba abin sa zuwa bakin titi dan samun abin hawan da zai shigar da shi Azare...sai fatan Allah ya tsare hanya kuma.

*****
Kafin cikar sha biyu na rana ya dira Jihar jigawa inda direct ya wuce gidan sa da yake zama bai tsaya 6ata lokaci a ko'ina cikin garin ba, balle ma yanda yake jin sa cikin 'kunci ya sa yafi bu'katar jin sa kawai a muhallin sa shi ka'dai inda babu hayaniyar kowa.

Gidan ya 'danyi 'kura ka'dan ba laifi dan haka bayan ya 'dan huta kafin lokacin sallar Zuhr tayi har ya 'dan kimtsa nasa 'dakin ya watsa ruwa sannan ya wuce masjid...sauran aikin ya barwa isowar Husnah ne idan ta iso sai ta 'karasa duk dama ya riga ya yanke cikin ransa cewa zaman su da ita zai cigaba tare ne bayan ya tabbatar da cewa babu wani ala'kar da taji yake shirin faruwa tsakanin sa da ita da ya danganci maganar aure, amma hakan bazai sashi hana ta kimtsa masa gidan sa ba...koma dan kar ta barshi da uban aikin da bai san yadda zai yi da shi ba.

Koda ya dawo daga masallacin ma 'dakin sa ya kuma shigewa yayi kwanciyar sa dan hutawa, bai ko nemi abinda zai sa a cikin sa ba ya bari sai zuwa yamma idan ya fita...kafin bacci ya 'dauke sa ne sai yaji 'karan Vibration na wayar sa dake gefen kansa.

Tsaki ya saki tare da 'dago wayar yana duban fuskar wayar gami da karanto sunan wanda ke 'kiran sa.

Sai a lokacin ma ya tuna ashe bai 'kira mahaifan sa ya sanar da su isowar sa ba...shaf ya sha'afa ma gaba 'daya.

Tsayawa tunanin da yayi ne ya sanya 'kiran da akayi masa yankewa nan ya ci karo da missedcall 'din da akayi masa 'dazu da yake tunanin fitar sa masallaci ne akayi 'kiran, na Ammi 3missedcall sai na Husnah kuma biyu yayin da na Is'haq kamar yanda yayi saving yake 'daya...sai dai kafin yayi wani yun'kuri take wani 'kiran Ishaq 'din ya sake shigowa while wayar na ri'ke a hannun sa.

*****
Ishaq da Imam abokan juna ne irin na 'kut da 'kut 'din nan su yan asalin jihar Borno ne haifaffun 'karamar hukumar Beinishek.

Sun kasance course mate 'din Mu'een ne dake matu'kar son ganin sun 'kulla abota dashi, musamman saboda ajin sa da kuma sanin yanda brain 'din sa ke kawo light ba da wasa ba.

NOORUL✔️Donde viven las historias. Descúbrelo ahora