P7

596 43 1
                                    

💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)

By
*Salmerh MD*

 

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *7*

Watan Sani uku da 3weeks sannan ya samu daman dawowa Bauchi.. ganin mahaifin sa ya samu sau'ki sosai ya warware.

   Shi kansa Sani a rame ya dawo duk ya fita hayyacin sa, gashi dama asali ba jikin kirki ne da shi ba, yaro ne matashi 'dan shekara ashirin da uku (23yrs) amma yanda mahaifiyar sa ta sako shi gaba da batun aure ma ka'dai yafi 'daga hankalin sa.

Sam baya son maganar aure a yanzu, yanda yake jima in zaiyi auren nema to Hauwa ce yake ganin zai iya aura dan sosai yarinyar tayi masa, itan ma da ace zai samu daman ke6ewa da ita yana jin da shikenan an wuce wurin.

  Sam bai shiryawa yin aure a yanzun ba, hakan ma da 'kyar ya samu ya lo6a mahaifiyar tasa da sunan zai dawo nan da wata 'daya sai ayi maganar auren, jin hakan da ya fa'da ne yasa ta amincewa har ta barshi ya taho, Sani kuwa har cikin ransa koka'dan baida niyyan komawa Jos a kwana kusa.

Ranar da Sani ya dawo Bauchi Deen na gida dan a lokacin shima yazo Bauchi, a yanda Deen ya gansa kuwa sosai ya tausaya wa yanayin sa, dan haka sai ya bashi hutun 1week  acewar Deen idan ya huta ya nutsu sai ya fara fita aikin sa.

Godiya sosai Sani yayi masa sannan ya koma masau'kin sa dake gidan....yana murmushin jin da'di, cuz shi kansa yana yabawa da karamcin Deen agare shi, bazai ta6a mantawa ba a jinyar mahaifin sa yaci a 'kalla kusan 80 thousand daga Deen 'din da yake aika masa wanda a fa'dar sa wai salary 'din sa ne, sosai yake yaba wa da hakan hatta mahaifiyar sa lokacin da zai taho ta matu'kar jan hankalin sa akan ri'kon gaskiya da amana ta kuma ce ya dinga kula da aikin nasa da kyau saboda ta fahimci ogan nasa na da karamci matu'ka, shi kansa Sani ya san hakan kuma yana yaba masa domin ba kowa keda hali irin nasa ba a wannan zamanin da damuwar junan mu bata dame mu, kowa kansa ya sani, kowa burin sa akansa ne, ka'dan daga cikin mu ne ke damuwa da yanayin halin da wanin sa ke ciki.
(Allah kasa mu dace).


*****
B'angaren Noor kam zuwan Sani bai wani 'da'data ba balle ya dame ta, dan ko ta kansa ma bata bi ba taci gaba da kai 'yar ta school tana kuma 'dauko ta, har tsawon sati biyu bata bi takan Sani ba, duk kuwa da cewa Deen yayi mata bayanin hutawan da Sani zai yi na sati ne da ya bashi daga  a fa'dar sa sai ta bashi key amma Noor tayi banza dashi.

     A sati na uku ne shi da kansa ya 'kira Deen da batun  dan ya lura kallo ma bai ishi Noor ba a gidan, shi kuwa zama wuri 'dayan sai yaji ya ishe shi.

Deen bai yi mamaki ba dayake yasan daman ba kowani namiji bane ke juran zama wuri 'daya batare da wani abin yi ba, baya ga haka ma shi Sani yaro ne matashi tashin 'kauye mai ji da 'kuruciyar sa da wuya ya iya juran hakan.

Noor ya 'kira yayi mata bayani akan cewa Sani zai cigaba da kai Baby school itama sai ta huta ta maida hankali akan nata karatun.

Shiru Noor tayi bata bashi amsar komai ba kasantuwar wani bugu da zuciyar ta tayi da bata san silar faruwar shi ba, sai dai bata raba 'dayan biyu hakan bai rasa nasaba da jin batun sani daga bakin mijinta.

        Abu 'daya da ta sani a yanzu kawai shine bata 'kaunar Sani har cikin zuciyar ta ba kuma ta 'kaunar kusancin sa da duk wani abinda ya shafe ta.

NOORUL✔️Donde viven las historias. Descúbrelo ahora