P23

407 25 0
                                    

💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)

By
*Salmerh MD*

 

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *23*

Cable na cajin lanta ya rarumo ya nufo kanta da shi a fusace, bata ankara ba sai jin sau'kan sa tayi a jikin ta haka ya dinga zabga mata cable 'din cike da 6acin rai.

Sai da yayi mata lilis kafin ya barta ya zauna bakin kujera yana hawaye dafe da kansa, yayin da Rahma ta takure a gefe tana kukan ceton rai wanda ko muryar ta ma baya iya fita sosai.

"....Rahma me kika rasa a gidan nan, da me aka rage ki da har zaki biyewa wannan 'dan iskan yaron, an gaya miki ana soyayya hakane?
Ko angaya miki idan ya gama lalata rayuwar ki zai aure ki?

Shiru bata bashi amsa ba sai ya sake fa'din " wama ya baki damar kulashi?....
Yanzun ma shiru tayi tana mai cigaba da sau'ke ajiyan zuciya.....Hayat sai ya sake mi'kewa a fusace yace " tambayar ki nake yi a ina kika sanshi?"

Yanda yayi maganar da yanda taga ya taso kanta ne ya sanya ta saurin furta " wallahi Yayah a school muka ha'du.....shine fa wanda nake gaya maka yake min Assignment idan an bamu"

Hayat kansa ya dafe gami da juyawa a hankali ya fara takawa....'kuna yake ji cikin ransa ji yake tamkar yayi ta zabga ihu, me yasa sai Mu'een Rahma zata kula?
Baya tantama kan cewa Mu'een da gangan ya shiga rayuwar Rahma, kenan yau 'din nan da banzo ba da Allah ne ka'dai ya san abinda zai faru da Rahma".

Innalillahi wa inna ilaihiraji'un....ya furta a fili gami da komawa da6as ya zauna bakin kujera......hannayen sa ya ha'da wuri guda yayin da zuciyar sa ta 'dai'dai ta sam ya kasa dai-dai ta natsuwar shi.

Batare da ya kalle ta ba ya fara fa'din " Duk haukata Rahma ni bana aikata zina bana lalata yaran mutane....amma me yasa zai min haka?
nawa ma Mu'een yake da har zaki bashi dama har cikin gidan ku har 'daki yana lalumar ki Rahma?, kinsan waye shi ne...kinsan miye tsakani na da shi?

" Dan Allah Yayah kayi ha'kuri ba zan sake ba...."
Tayi maganar da 'kyar cikin kuka.
Sai ya dakatar da ita da fa'din
" Wallahi Rahma idan kika 'kara biyewa yaron nan koda wasa ko Allah zaki ga abinda zan miki zaki sha mamaki na".

Da 'kyar take kuka amma hakan bai hanata bu'den baki cikin kukan tace dashi " dan Allah kayi ha'kuri Yaya wallahi ni ina son shi sosai bazan iya rabuwa da shi ba".

" Ya ta6a ce miki zai aure ki ne?"

Shiru tayi ta cigaba da kukan ta tana tunanin yaushe ma ita kanta tasamu amsar soyayyar ta ballantana har aje ga maganar aure.....shirun da Hayat yaga tayi ne ya bashi damar cigaba da fa'din......" Mu'inuddeen ba auren ki zai yi ba Rahma gara tun wuri ki cire shi a ranki dan ko yace zai aure kin ma ni ba amincewa zanyi ba, dan haka tun wuri ki cire shi a ranki, idan har a wannan shekarun nasa ya iya ya ke6ewa da mace to kiyi tunanin gaba mai zai aikata dan haka daga yau babu ke babu shi har abada".

Yana gama fa'din hakan ya tashi ya fice daga parlourn inda ya barta tana faman sake wani sabon kukan da fa'din " dan Allah yayah kayi ha'kuri wallahi shi ka'dai nake so ni....."
Ko sauraren ta Hayat bai yi ba yayi tafiyar sa....haka bai ko sake tunawa da takaddun da yazo kar6a a wurin ta ba.

*****
A hankali yake tafiya har ya isa bakin titi shi kansa bai jin da'di har cikin ransa bai san me ya kaishi aikata irin wannan aikin ba.

Mashin ya tara ya hau zuwa gida wanda da sau'kar sa ya wuce 'dakin sa batare da yabi ta kan kowa a gidan ba, dana sani kawai yake yi na sanin Rahma da kuma abinda ya aikata sai dai koma me ya faru yafi bawa Hayat laifi domin a ganin sa duk shine sanadi dan da be sashi ya bar wancan makarantar ba ai da bazai ta6a ha'duwa da Rahma ba balle ma har hakan ya faru tsakanin su.

NOORUL✔️Donde viven las historias. Descúbrelo ahora