P80

417 46 7
                                    

💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)

By
*Salmerh MD*
 

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *80*

Rungume ni tayi tana hawaye, Anty yanzu ko dogon magana bata iya yi, ko ina ka ganta shiru zaka ganta a zaune tana tunani, sosai take jin mutuwar Baby cikin ranta.

Sati guda naji Ammi na fa'din zasu yi kafin su koma, dan haka tun daga lokacin nima na fara kimtsa kaya na a 6oye batare da na bari sun sani sani ba, tunani idan su ka san niyyata 'kila su dakatar da ni d wannan kalmar ta ha'kuri, ni kuwa a yanzun sam bazan iya ba na riga na yanke abinda nake ganin ya fimin.

  Ana gobe su Ammi zasu tafi na je na bu'de akwati guda ina jera kaya na,  'ko'karin zugewa nake yi sai ga Anty Zainab ta shigo ta same ni.
Da mamaki ta tsura min idanu tana kallo na dan ita bata san dalilin da zai sani shirya kaya ba.

Tambaya ta tayi" Me zakiyi da kaya har haka kuma?" Ina tayi maganar da alamun mamaki 'karara kan fuskar ta.

Tun lokacin da naji motsin shigowan ta sau 'daya tak na 'daga idanu na na kalle ta daga hakan ban sake ba, sai ma na fara jin hawaye na taruwa min.

Ko yanzun ma da tayi min tambayar ban 'daga kaina na dube ta ba nace" Gida zan koma Anty...tare zamu tafi da ku...".
Na 'karasa maganar da muryar kuka.

Shiru Anty Zainab tayi tana duba na jikin ta sanyi 'kalau a hankali ta mi'ke ta fita, bansan me taje ta gayawa Ammi ba sai ganin ta nayi ta shigo bayan fitan Anty Zainab bada jimawa ba.
Lokacin har na gama harha'da kayan ina tattare kayan dake kan mirror na.

Sunana Ammi ta 'kira da raunanniyar murya sai na waigo na dube ta batare da na amsa ba, 'lasa nayi da idanu na kawai wanda take naji zuciya ya fara dukan uku-uku, Addu'a nake a raina Allah yasa Ammi kar ta hanani barin wannan gidan, a hankali na 'karasa gaban ta na dur'kusa tuni idanu na sun cika da hawaye, 'kasa nayi da kaina batarexda iya duban fuskar ta ba, hawayen da suka taru min ne suka yi saurin gangarowa na kai hannu na share su, duk abinda nake yi Ammi bina kawai take da idanu bata cecda ni 'kala ba.
Hawaye na ne suka dinga gudu akai-akai ina share su na fara ro'kon ta" Dan girman Allah kar ki hanani tafiya tare da ku, Ammi ban jin zan iya sake rayuwa a garin nan  kar ki dakatar da ni dan Allah.
Ammi ban ta6a neman wani abu na rasa ba tun tasowa ta saboda baki rage ni da komai ba girma na har kuwa yau 'din nan Ammi nasan kin wadata ni da komai, amma yau ka'dai ina neman alfarmar ki Ammi, yau ka'dai ina ro'kon ki  ba wai dan kin kasa ba sai dan ki cika min buri na kawai dan Allah ki barni in tafi.
Wallahi Ammi bazan iya sake rayuwa inyi farin ciki ba matu'kar ina tare da Yah Deen...ban tsane shi ba amma na tsani rayuwa ta tare da shi, na tsani in sake gani na 'kar'kashin inuwar gidan sa, idan nace zanci gaba da zama anan wata'kila nima gawata zaki zo ki tarar Ammi...dan girman Allah badan ni ba ba dan bana son Yah Deen ba ki ce ya sake ni..Ammi".

Kuka sosai ne ya ci 'karfin ta ta kwantar da kanta kan 'kafafun Ammin tana kuka sosai.

Ita kanta Ammin ji tayi zuciyar ta ya karye sosai, ha'kika ha'kurin ta ya kai ma'kura tunda har ta iya bu'dan baki ta sanar da ita abinda ke ranta, a hankali Ammi ta dur'kusa sannan ta 'dagota ta rungume ta ajikin ta tana bata ha'kuri tace" Daina kuka kina damun kanki...da kaina ma ko baki ro'ke ni ba ba iya tafiya zan yi in sake barin ki tare da shi ba, shakka nake ji kar ki 'ki amincewa shiyasa na kasa fa'da miki amma ni na riga na yanke hukuncin raba shi da ke....domin hankali na zai fi kwanciya idan nasan cewa baki tare da auren sa, ha'kurin da kika yi masa abaya ma ka'dai ya isa bana fatan ki sake kwatanta irin wannan zaman har abada, tsananin tausayin ki ke hana ni magana 'yata shekarun ki sunyi ka'dan da wa'dannan abubuwan..."

NOORUL✔️Donde viven las historias. Descúbrelo ahora