P38

359 18 0
                                    

💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)

By
*Salmerh MD*

 

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

🤞🏻 *Dadicated my In-law( Umm Amatullah) Luv u irin sosai 'din nan* 😍 *..Allah ya raya mana Zuri'a 🙏AMEEN* 🙏

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *38*

Tana isowa ta 'kira shi yayi mata kwatance amma da 'kya ta gane gidan da yake farkon zuwan ta kenan, sai da ta ha'da da tambaya kafin nan, gashi kuma ya'ki fitowa balle ya sau'ka'ka mata abin.

Mutanen kuwa idan ta tambaye su kawai sai su bita da kallon mamaki kafin a nuna mata hanyar da zata bi...dan sun san ba 'yar garin bace zuwa tayi.

Da 'kyar ta isa gidan bayan ta ha'du da Imrana wanda ya kasance shine mutun na 'karshe da ta ha'du dashi shine kuma yayi mata jagora...Yah Deen ne ya tura shi.

Ko lokacin da zata fita daga motar sai da ya sau'ke ajiyan zuciya yana mai yabawa da halittar da Allah yayi mata...dan sosai Husnah ta ha'du iyaka ga kyan jiki gashi ko'ina zam-zam masha Allah.

Tare suka shiga Imrana da ita amma ganin yanda ta tafi ta rungume Yah Deen a gaban idanun sa ya sa shi fahimtar cewa ala'kar tasu babba ce, balle da yaga irin kallon da Yah Deen ke binta dashi..ai hikenan.

Imrana murmushi ya saki sannan ya juya ya fita yana fa'din " sai ka fito malam...ni kam nayi nan".
Yah Deen ko kula sa bai yi ba har ya 'karasa barin gidan.

Imrana kuwa fita yayi cikin ransa yake fa'din " gayen nan zai kwashi gara anan gaskiya".

Husnah bata yadda azahar ta gota tana cikin garin ba, gudun kar tayi laifi agida bacin shopping tace zataje.

A hanzarce ta kintsa ta fito taja motar ta tayi gaba zuciyar ta fes dan ta faranta ran masoyin ta.

〰〰〰
        Bayan sati biyu....abubuwa duk sun cunkushe ta 6angare na, abin duniya ne yabi ya ishe ni....musamman da ya kasance su Saif na shirin komawa makaranta, gashi kuma ayau 'din zanje shara can gidan sa, a duniya babu abinda nafi tsana kamar zuwa gidan Yah Deen sam banso koka'dan, gashi hatta Saif ban bari ya san abinda ke faruwa ba gudun kar ya sanar da Ammi Yah Deen ya yanka wuya na.

Gashi sam ba kara ce da shi ba, duk yadda ka zage kayi masa aikin abu 'kalilan sai yasa ka gaba da masifa musamman ma ni, ban kuma san dalili ba..gashi ya hana ni yi mai kuka a gida yace ko da wasa hawaye na drop 'daya nayi kuskuren da ya 'diga mai a gida to sai ya 6allani.

Idan yace 6allanin nan kuwa gani nake tamkar yadda ake 6alla kara haka zai min shiyasa tsoro ya yiwa zuciya ta 'kawanya, koda wani lokaci tsoron sa nin kuwa yake 'karayi cikin zuciya ta, saukin ma da nake samu shine da yake Ma'u na raka ni, zaki yi mamakin duk wannan tsoron nasa fa da nake ji bai ta6a 'daga hannu ya dake ni ba kalaman sa ka'dai ke firgita ni.

Duk na koma wata iri da ni, walwala ta ta ragu sosai, ko a makaranta ban fahimtar komai tsabar damuwar dake cunkushe cikin raina, gaba 'daya na fige na 'kara ramewa gani daman ba jikin kirki gare ni ba, hatta Ammi sai da ta lura da ramar tawa da kuma ta tambaye ni ko wani abu ke damuna sai nace da ita bakomai hakan yasa kawai ta 'kyale ni, yayin da Ummah ta ke tunanin ko girma ne ya sanya ni ramar.

    Yau ma kamar kullum, ta kasance ranar Lahadi ne so babu makaranta, hakan kuma yasa tun tashi na da safe abin ke ta min yawo a zuci, inata 'dawainiya da tunani, fargabar ta inda zan fara  tambayar Ammi cewa zan fita nake yi, bansan 'karyar da ya kamata inyi mata da zai sa ta barni in fita ba dan bata so in cika yawo da yawa acewar ta...shiyasa ma ta fara complaint da yawan ce mata zani gaida Ummah ta da nake yi..duk kaina sai ya kulle na rasa mafita.

NOORUL✔️Where stories live. Discover now