P89

361 41 17
                                    

💕 *NOORUL* 💕
(Haske nah)

By
*Salmerh MD*

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *89*

Baya yin cikakken wata biyu bai zo gida ba..haka zai zo yayi weekend 'din sa ya koma lafiya lau, duk yanda zai ji ciwon sa na damun sa baya bari kowa ya fahimta sai dai in abin yafi 'karfin sa ne.

Sai dai ko a fahimta ta yanayin 'karfin jikin sa ko kuma rashin walwalar sa amma da kansa kam baya furtawa ga kowa cuz gani yake kamar shine ya jawa kansa da kansa...

'Bangaren Jiddah kuwa ta riga ta sanyawa ranta ha'kuri yanzu, tayi kuka, kuka sosai fiye da zaton mai karatu har sai da ta raaa mai lallashin ta ma, da 'kyar ta daure ta fara rage damuwar dake cikin zuciyar ta akan Mu'een.

'Ko'kari sosai tayi wajen ganin ta cire shi cikin zuciyar ta domin ta fahimci tana son wanda ba zai ta6a zama mallakin ta bane, 'kila 'kaddarar ta kenan shine 'dumbin 'kaunar sa da tayi tasan har abada bazata iya ta6a son wani kamar yadda ta so shi ba, amma ya zama ta ha'kura da shi, badan komai ba sai dan labarin da mahaifin ta ya bata, abu guda 'daya tak ne ya taka mata birki ya kuma yi mata katanga tsakanin ta da shi baya ga da babu abinda zai sa ta janyewa har sai inda 'karfin ta ya 'kare domin tana son shi sosai, amma kunyar abinda mahaifin ta ya aikata musu ka'dai ma ba zai barta ta sake kusantar inda Mu'een yake ba har abada.

Sam ta'ki mahaifin ta ta 'ki komawa inda yake kamar yadda mahaifiyar ta ma ta'ki...duk da cewa tana da masaniya akan irin 'kaunar da yake mata amma hakan bai hana ta jin haushin sa ba.

Mahaifin Jiddah lokuta da dama ya kan zauna ne yayi kuka da hawayen sa kamar yaro 'karami ganin cewa duk ahalin sa sun gushe shi ne saboda mugun halin da ya shuka tun abaya, ji yake dama lokacin ya dawo baya ya kasance bai aikata hakan ba, yasan da yanzu yana zaman sa cikin farin ciki da iyalan sa kamar kowa...tsananin tausayin Jiddah yake ji a koda wani lokaci, dan ya san abin ita zai fi ta6awa, gashi bata kusa da shi balle ya san halin da take ciki har ya samu daman tausan ta yana bata ha'kuri.

Cikin cousins 'din ta ta samu wani Bilal ke son ta..da farko 'kin bawa kowa fuska tayi wanda daga baya da kanta tayi tunani taga dacewar bawa wani dama ko dan ta rage ra'da'din damuwar da ke cin ta ma a kullum game da Mu'een hakan yasa ta amince da shi sai dai ba sosai take bashi fuska ba sai lokacin da ta ga dama...a hakan har manya suka sanya baki cikin maganar ta su.

Tambayar auren tane ya kai wasu daga cikin dangin mahaifiyar ta wajen Barrister nan suka tarar da shi ya koma abin tausayi, ciwon diabetes yake fama da shi gashi babu wani da ke kula da shi.

Koda suka tambayi auren batare da 6ata lokaci ba ya basu ya kuma ce da su duk lokacin da suka ga ya dace kawai su sanya ba sai sun sake dawowa wurin sa ba.

Shikam ma farin ciki yayi da jin batun auren Jiddah ya taso cikin 'kan'kanin lokaci haka kuma Allah ya nufe shi da bada auren da kansa.

Ko da suka koma gida hankalin su kasa kwanciya yayi haka suka dinga yiwa Mummyn Jiddah nasiha da yake manyan yayun tane da kuma kawunan ta bazata iya yi musu gardama ba dole haka ba dan taso ba ta dawo gidan mijin ta amma Jidda 'ki tayi tayi zaman ta can wurin dangin mahaifiyar ta.



*****
_Bayan wasu watanni_
Lokaci ya 'dan ja sosai dan 'yan biyun Ammi duk sun kammala makarantar su yanzu saura bautar 'kasa...sun girma sun zama manyan samari dasu.
Ishaq kuwa na nan har a lokacin bai kuma 'dago zancen aure ba tun da aka raba shi da wancan yarinyar shikenan ya fawwalawa Allah komai, da farko ma gani yake kamar zata dawo watarana amma da yaga har anci shekara guda shiru shikenan ya saki ransa ya manta da ita, ya kanzo Shuwarin ya gaida su Alhaji Baba duk lokacin da ya samu dama, kuma ba 'karamin da'di yake ji ba da yanda suka 'dauke shi kamar 'dan su na cikin su...abu da ke tsaya masa arai a kullum kan rashin matar Deen ne, gaba 'daya ya rasa har ina su Ammi ke son jan maganar dan har ga Allah shi ba 'kaunar rabuwar sun yake ba, gefe guda kuma da kansa ya 'daukan ma Alhaji Baba cewa idan yayi masa kyauta yayi al'kawarin baze mayar masa da kyautar sa ba, duk da be san miye ba amma ya amince masa yanzu kuma abin na damun sa bayan fahimtar da yayi cewa kyautan da Alhajin ke fa'di na aure ne bana komai ba nd be san wace ba.

NOORUL✔️Donde viven las historias. Descúbrelo ahora