P40

629 25 2
                                    

💕 *NOORUL* 💕
(Haske nah)

By
*Salmerh MD*

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

🤞🏻

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *40*

Lokaci sun 'dan ja sosai, dan kusan watanni shida kenan da ganin da na yiwa Yah Deen da budurwar sa na farko, ko hutun can ma kuwa daya zo na 'kara ganin su, marasa kunya a 'kofar gida ganin dan unguwar babu mutane sosai ya sanya ko kunyar Allah basu jiba suke kissing juna ga dukkan alamu ta fito zata tafi ne.

Ni kuwa yanzu har na saba da bi ta gidan da yake matu'kar yana gari idan zani gidan Ummah ta sai nabi ta can dan kawai inga ko wannan farar motar tazo...bansan me yasa na damu da zuwan motar ba duk kuwa da cewa idan na ganin na kanji haushi sosai har cikin raina, sau tari kuwa ina ganin motar, sai dai bansan me suke aikata wa ba a cikin gidan tunda ba gani nayi da idanu na ba amma koma de miye ina da tabbacin ba abin alkhairi bane.

Ko Ammi ma yanzu kwata-kwata ta daina aika na wurin sa, idan yana son abu sai dai shi da kansa yazo ko kuma ya aiko yaro amma Ammi bata tura ni sam...musamman ma da ta fahimci irin tsoron sa da nake yi sosai.


*****

Yau 'din ma kuwa gidan Ummah ta zani gaida Addah ta Maryam da tazo tun jiya, ni ka 'dai nake tafiya ta cikin hankali kaina 'kasa, sai dai maimakon in 'dauki hanyar gidan Ummah direct a a sai na yanka na kama hanyar da zata sada ni da gidan Yah Deen.

Tun daga nesa na fara hango motar take sai naji wani iri cikin raina, sai dai duk da naga motar ban dakatar da tafiyar da nake yi ba inda nake sake tunkarar gidan ban kuma san me ke ingiza ni ba kawai dai nasan bai wuci tsabar gulma ba, cak na tsaya ganin ta fito ita ka'dai ta shiga motar ta taja tayi gaba har ta 'karasa wucewa ban ga ya fito ba ga dukkan alamu dai ranar bai yi mata rakiya ba.

Juyawa nayi da sauri na kama hanya 'kafafu na har na sar'kewa saboda yanda jiki na ke rawa da ganin Husnan.

Husnah kam yanzu hat ta saba da zuwa wajen sa ma ko ganin wahalar hakan batayi balle rashin dacewar sa, ko da shi bai 'kira ta saboda bu'katar sa ba ita da kanta ma bata iya sati batare da ta zo inda yake ba hakan yasa jama'ah da dama suka farga da zirga-zirgan da take yawan yi a garin musamnan da kowa ua san cewa gidan da take zuwa 'din gidan 'dan Alhaji Baba ne kuma shi ka'dai ke zama a gidan.

Sannan zuwan Husnah yana farawa ne da zarar ya dawo hutu gida, idan akace baya nan kuwa ba'a ta6a ganin ta tazo, wannan dalilin ya sanya jama'ah zargin wannan ala'kar tasu tare da dasa tunani a zu'katan jama'ah.

Haka na isa gida wata iri da ni sam na rasa walwala ta, su'kuku na yini ranar gaba 'daya, abin na ci na arai amma ban iya na sanar da kowa ba...koda su Addah ta suka tisani gaba da tambayar abinda ke damu na sai cewa nayi kaina ke ciwo, ai kuwa take aka nemo min magani na sha dan dole ba dan raina ya so ba.

Ana saura sati biyu zai koma school ranar da sassafe Alhaji Baba ya 'kira shi a waya inda yace yazo ya same shi....

Yanayin da yaji muryar Alhaji Baba yayi maganar ya sanya bai 6ata lokaci ba ya iso gidan dan cika umarnin Alhajin.

Bayan sun gaisa cikin sakin fuska sai Alhaji Baba ya tambaye shi cewa " Abinda yaji gaskiya ne ko kuwa, ance wata yarinya na yawan zuwa wancen gidan da kake, wacece ita?" Numfashi Alhaji Baba ya sau'ke tare da cigaba da fa'din " Ni da kaina naga tana shiga gidan rannan ko ba ita bace ke zuwa da farar mota?"
Ya 'karashe maganar yana kallon fuskar Yah Deen domin karantar yanayin sa.

NOORUL✔️Donde viven las historias. Descúbrelo ahora