P25

411 26 4
                                    

💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)

By
*Salmerh MD*

 

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *25*

" Allah sarki....ai dole yayi murna zaije yaga mahaifan sa".
Cewar Hafsat dake zaune tana kallon Nuree.

Noor kuwa " Hmm"  kawai tace gami da daidaita zaman ta, kafin ta sake yin wata maganar sai suka jiyo tashin 'kiran sallahr isha'i.

Take sai Hafsat tace
" Ikon Allah...ashe lokaci yaja har haka, muyi sallahr tukunna sai ki 'karasa bani labarin kafin Safwan ya dawo ko?"
Nuree bata furta mata komai ba dan haka kawai sai Hafsat ta mi'ke ta shiga bayi dan 'dauro alwala.


*****
         'Bangaren Deen kuwa...har yanzun bai farka ba  da yake ma anyi masa allurar bacci shiyasa abin ya 'dan ja lokaci.

  Safwan ne dai hankalin sa ya kasa kwanciya dan allurar baccin ba mai nawi akayi masa ba, in har dan allurar ne to bazai wuci 1hr ba zai farka amma sai gashi kusan 3hrs amma ko motsi bai sake yi ba, sosai Safwan ya kasa natsuwa da hakan shiyasa ma tun fitar sa daga 'dakin da aka kwantar da Jasmine bai sake dawowa ba, yana can yana zirga-zirga tsakanin Deen da Sani mura'din sa kawai yaga farkawar Deen amma abin ya faskara, dan ma kar Hafsat tayi masa zancen komawa gidane yasa tun fitar sa daga 'dakin bai dawo ba in da suke ba, dan harga Allah shi bai jin zai iya tafiya ya bar Mu'een cikin wannan halin saboda amincin dake tsakanin su ga kuma Alhaji Baba da yace ya kula masa da su kafin isowar sa gobe....burin sa ya samu jin dai-daituwar lafiyar Mu'een 'din kafin ya koma gida.



〰〰〰
     Jasmine ma bacci take yi har yanzu, koda Hafsat ta 'dauro alwalar ta fito ma bata nufi wurin dadduma ba sanadiyyan ganin Noor gaban gadon da Jas ke kwance, tsaye taje tayi a kanta sannan a hankali kuma sai ta koma ta zauna gami da ta6a jikin Jas 'din, cikin sa'a sai taji zazza6in jikin tan ya sau'ka ba kamar 'dazu ba.

Ajiyar zuciya ta sau'ke mai sanyi gami da fa'din
" _Alhamdulillah_ " cikin zuciyar ta, ji take tamkar ta 'daukewa Jas ciwon ya dawo kanta, amma tasan hakan ba mai yiyuwa bane.

   Iska ta sake furzarwa daga bakin ta a fili ta furta " Allah zai saka miki Baby...Allah ya isan miki".

  Hafsat dake tsaye daga can gefe ne ta 'karaso gami da dafa kafa'dan ta cikin sanyin murya tace da ita " kiyi ha'kuri please Hudah ki fawwalawa Allah komai...nasan abin da ciwo amma ya zamuyi 'kaddarar nan dai ya kamata ta kasance a koda yaushe cikin zu'katan mu matsayin mu na musulmai masu kwa'dayin kasancewa cikin za6a66un Allah masu imani...in har muna son samun wannan kusancin kuwa dole sai mun sanyawa ranmu dangana da komai zai faru na rayuwa"

   Nuree kallon Jasmine ta sake yi, batare da ta furta komai ba kawai ta kusanta fuskar ta izuwa fuskar Jas ta sumbaci goshin ta cikin ranta ta furta " speedy recovery mamana" sannan ta mi'ke tsaye ta shige bayi.

Yayin da Hafsat ta bita da idanu har ta 'karasa shigewa bathroom 'din kana ta girgiza kanta cike da tausayi ta wuce kan dadduma ta tada sallahr isha'i.

Nuree bata fito daga bayin da wuri ba, cuz lokacin da ta fito ma har Hafsat ta idar da sallahr tana 'ko'karin gyarawa Afrah kwanciya....
'Karasowa tayi ta zauna kan kujerar dake ajiye a wurin yayin da Hafsat ta koma kan daddumar ta zauna ta zuba mata idanu gami da bata hankalin ta gaba 'daya...." ina jin ki"
Hafsat tace a hankali.

      Noor kuwa sai ta sau'ke ajiyan zuciya cikin sanyin jiki sannan ta cigaba da fa'din......"

      ♾ Washegari da safe da nazo sai na tarar da Zaid zaune a parlour ya baje yana zane inda ya bada dukkan hankalin sa kan zanen kinsan zanen Intro- Tech na bu'katan natsuwa sosai.

Ni kuwa tun shigowa ta hankalina ya koma kansa shiyasa ma ina bawa Ammi sa'kon da na kawo kawai da sauri na na nufo inda yake zaune nima na zauna daga gefen sa kan 'kafaya 'daya....nace dashi" Zane kaka yi ne Zaid?"
Kansa 'kasa ya bani amsa da
" a a caca nake bugawa"!
batare da ya ko kalle ni ba.

Ban damu da jin irin amsar da ya bani ba sai na sake cewa da shi
" Ina cacar take to nima zanyi".

" Bansani ba".
Yace da ni a takaice a kuma 'dan harzu'ke.
   Yatsina fuska ta nayi gami da jan guntun tsaki sannan nace " Allah kai Zaid 'din nan ka fiya masifa...daga tambayar ka shikenan zaka fara yi min ihu?"

Sai yanzun ya 'dago kansa ya kalleni, idanun sa cikin nawa yace dani " to ke 'din makahuwa ce da ba ki ganin abinda nake yi ne?"

Shiru nayi na cigaba da kallon littafin nasa, shima 'din bai sake furta komai ba haka ya cigaba da zanen sa bai sake bi ta kaina ba ma.

Ban gushe ba ina zaune a wurin har sai da na dangana hannuna da littafin nasa Zaid sai yayi saurin bige min hannu yace " karki dameni ni dallah".

Ban damu ba sai ma na sake fa'din " kawo to in tayaka".

Cike da masifa yace " see u..an gaya miki suyan waina ne da zaki ce in baki ki tayani......?"

Ban ko bi ta kan maganar da yake yi ba cuz tun kafin ya rufe bakin sa na wafce takaddar na mi'ke da gudu nayi hanyar waje.

  Kafin Zaid ya ankara sai gani yayi bana gaban sa haka ma littafin sa....da hanzari ya tashi ya bini a harzu'ke yana fa'din "Ammi kin ganta ko?"

Nima ina cikin gudun sai nace" ai tayaka zanyi..."
    Ban gama rufe baki na ba kawai naji...Kau... nayi karo da abu wanda tun kafin in ankara in gane da me nayi karon sai kuma naji sau'kan mari saman kuncina daya matu'kar gigita min lissafi har ya sanya ban ma san lokacin da na yada takaddar ba na dafe fuskata gami da yin baya ka'dan na 'daga kaina sama na kalle shi.

   Gani nayi ya wani ha'de rai sosai tamkar shi aka mara ba ni ba.

Kwa6a fuska ta nayi nima gami da 'kif-'kif da idanuwa na da suka cika taf da hawaye sai dai basu gangaro ba.

" Non-sence" naji yace kawai tare da wucewa ya bar gurin direct ya nufi table 'din cin abinci.

Ni kuwa sake juyawa nayi na bisa da idanu har ya isa ya zauna ban daina kallon sa ba, shikuwa koda wasa bai sake kallon inda nake ba...... ji nake tamkar in bishi in rama marina amma tsoro nake ji, cuz ban san shi ban kuma ta6a ganin sa a gidan ba haka kuma ban tuna cewa su Zaid da Saif nada Yayah ba balle inyi tunanin ko shine.

  Zaid da tun 'dazun ya ja yayi turus shima a hankali ya 'karaso ya 'dauki littafin sa gami da fa'din " Allah shi 'kara".

Daga haka ya juya ya koma ciki abinsa daga inda yake ya mi'kawa wancan 'din gaisuwa da fa'din " ina kwana Yayah?"

Da " lafiya " ya amsa shi a takaice batare da ya ko kalli Zaid 'din ba.

Haushi ne sosai ya kamani bayan jin furucin Zaid 'din, take sai hawayen na da suke ma'kale suka 'karasa gangarowa....da gudu na wuce na tafi wurin Ammi dake kitchen ina kuka.
  Sai lokacin da nazo wucewa ne kafin ya 'dago ya kalle ni gami da sakin tsaki sannan ya koma ya kishingi'da akan kujerar harda lumshe idanu.

  Ina shiga sai na rungume 'kafafun Ammi ta baya ina kukana.
   A rikice Ammi take fa'din " Subhanallah! menene ya faru? Me akayi miki?

Ban tankata ba kawai na cigaba da kukana, yayin da Ammi tayi 'ko'kari ta cire ni daga jikin ta sannan ta sake tambaya ta " wa ya ta6a ki?"

Cikin kukan na bata amsa da fa'din " wani ne ya mare ni"!

Ido ta 'dan zaro gami da fa'din " mari dai? A ina yake?  me ma ya ha'da ki dashi da zai mare ki?"

Da murya kuka na bata amsa da fa'din
" Ni ban masa komai ba kawai dan na 'dauki takaddar Zaid shine mukayi karo ya mare ni"
Inda na 'karashe maganar tawa da sheshsh'ka.

Ido Ammi ta lumshe gami da girgiza kanta gefe da gefe a hankali ta furta " _MU'EEN_ ".






_Comment_
_Vote_
_Share_







*Salmerh ce* 😍

NOORUL✔️Où les histoires vivent. Découvrez maintenant