P21

510 26 0
                                    

💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)

By
*Salmerh MD*

 

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

~Dedicated to👇🏼 Hussaina B. Abubakar~
~Wannan kam naki ne Mrs Habou~ ~(Sa'eenah) wallah kina sani nisha'di sosai....~
~Allahu ya bar min ke~ 😘👌🏻

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *21*

Bai wani tsawaita tunanin ba balle har ya hana shi sukuni kawai yaci gaba da harkokin sa.

Bai kuma kara bi ta kan yaran ba haka bai sake ganin su ba, kamar yadda bai sake tunawa da su cikin sha'anin rayuwar sa ba dan basu ne a gaban sa ba a halin yanzun.

Karatun sa kawai ya sa agaba littattafan sa sune abokan sa baya shiga rayuwar kowa cikin makarantar.

*****
*Bayan sati 'daya*

         Zaune yake daga gefen bakin Varandern 'kofar class 'din su yana duba wani handbook fuskar sa sanye da farin siririn glashi, yayin da uniform 'din dake jikin san suka matu'kar amsar fatan jikin sa yafito shar da shi.

Wajajen goma da rabi ne dan break akeyi a lokacin hankalin sa sosai ya 'dauku ga karatun littafin, batare da yayi zato ba kawai yaga an 'daura masa wani takadda kan nasa handbook 'din har ya kansance ma baya ganin nasa sai wannan 'din.

Mamaki ne ya cikashi na ganin hakan mamakin waye mai wannan uban 'ko'karin da har zai masa haka, dan shi ba saba yin hakan yayi da kowa ba, sai dai yana da ya'kinin duk yadda akayi an sa6a lamba ne shiyasa akai masa hakan, may be kama yayi da wani daban da har yasa aka ga kamar wancen 'din ne.

A hankali ya 'dago kansa dan ganin kowaye sai yaga ashe ma mace ce, macen ma kuma waccen yarinyar da suka ta6a hast duwa a Libry last week... ita ce tsaye kansa cikin sakalalliyar fuska take duban sa....da wata 'kawar ta su biyu suka zo.

Suan hada idanu da ita sai yaga ta tura baki gaba kamar yanda yaga tayi rannan a Libry, sarai ya gane ta amma sai ya ce da su " me ya faru?"

'Dayar yarinyar ne ta juya ta kalle ta sai ta wani yan'kwana fuska sannan cike da shagwa6a tace da shi " Ayyah Bross tun ranar fa nake ta neman ka ban ganka ba, am bamu assignment na mathematics da yawa ni kuma ban iya ba, kullum sai na ta duba ka amma ban samun ka na kaima Yayah Hayatu shi kuma yace wai bai iya ba ni bansan yanda zan yi ba sai yau na ganka anan".

Bai furta mata komai ba illa takaddar tata da ya 'daga da niyyar ganin set 'din da take sai idanun sa ya sau'ka kan sunan ta dake rubuce a bangon littafin da manyan haruffa RAHMA SALIS GIMBA......
yaga an rubuta...Dum yaji zuciyar sa ta tsinke haka kawai bai san dalili ba.

Tuno sunan Hayat yayi da ya baro a wancen makarantar wato HAYATUDDEEN SALIS GIMBA.....
Batare da ya 'dago ya kalle ta ba ya tuno kamannin su take ya fahimci dalilin da ya sanya yake ganin kamar ya san yanayin fuskar ta a wani guri.
Kenan itan blood sister 'din Hayat ne....me hakan ke nufi kenan?"
Ya tambayi zuciyar sa.

" Please kayi min anjima zanzo nan in kar6a wai gobe za'a yi submitting kaji".

Tana gama fa'din hakan ta kama hannun kawar ta suka bar wurin.

Bai iya yace da ita komai ba har ta 6acewa ganin sa, sai a sannan ya sake duba bayan littafin SS 2A yaga an rubuta.

Gaba 'daya sai yaji jikin sa yayi sanyi, Hayat da yafi tsana a duniya ne yau kuma Allah ya ha'da shi da sistern sa anan, me hakan ke nufi wai, na kasa ganewa ?"
Ya sake tambayar kansa...gami da cire gilashin dake manne a fuskar sa.

NOORUL✔️Donde viven las historias. Descúbrelo ahora