P48

459 32 0
                                    

💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)

By
*Salmerh MD*
 

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *48*

Ita kanta ta matsu ta jishi su gana, musamman ma da ta tuno jiya da dare bayan dawowar Abbah da ta gaida shi yanda ya kar6i gaisuwar ta cikin nuna halin ko'in kula, yana gyara zaman sa zuwa kishingi'da yace da ita" Wato mahaifiyar ki ce ta gayyato ki musamman domin ki zo ki gaya min cewa baki amince da za6in da nayi miki ba ko?"
Da sauri ta 'daga kai ta kalle shi tana girgiza kai tace" Ba haka bane  Abbah..Mummy fa bata ce da ni in ce ban yadda da za6in ka ba..."

Tun kan ta rufe baki yace" To ai shikenan..sai ki je ki jira ranar 'daurin auren dan ba dogon lokaci za'a saka ba,  mahaifan sa sunce min already kun daidaita kanku da yaron dan haka ba wani abinda zamu jira... daga Shuwarin suka zo wai sunan sa Muhammad...sai kije ki bincika cikin maneman ki babu mamaki kiyi saurin gano shi".

Sum-sum ta tashi tana juya sunan cikin ranta da matu'kar mamaki sai taji yace" Yauwa tunda kin riga kin dawo to babu kuma batun komawa sai bayan auren, idan mijin ki ya yarje miki komawa Falillahil hamd in kuwa yace a a shikenan sai ki fawwalawa Allah kinji?"

Kai ta 'daga masa alamar " Erh taji".
Sannan ta juya ta 'karasa fita daga 'dakin nasa wanda ada ya kasance 6angaren mahaifin ta ne.

Yanda 'karara wan mahaifin ta ya nuna rashin damuwa kan halin da zata shiga ya nuna rashin damuwar sa kan farin cikin ta ko akasin haka yasa a daren ranar sai da ta sha kuka amma babu wanda ya sani daga ita sai Allahn ta ne ka'dai da ta gaji ta lallashi kanta.

Shiyasa yanzun ta damu sosai wajen ganin ta same shi a waya, tafara gano kamar shi 'din ne amma bata da hujjar gaskatawa inba taji daga bakin sa ba....ko kashe wayar tasa ma sai take ganin kamar yana da nasaba da faruwar maganar auren amma duk tayaya zata gaskata hakan?..No way".

Ta riga ta san halin sa da kafiya da kuma bakin hali in ba dan haka ba da ko wata friend 'din zata 'kira tace a kai masa waya suyi magana amma tasan inba ra'ayi yayi ba Mu'een ba zai ta6a ansan wayar ba sai dai a idon 'kawartata yayi 'karyar ta bari zai 'kira ta kawai.

Ishaq ne ya fa'do mata cikin ranta, sai kuma ta tuna bata da contact 'din sa..haka ta zauna tayi tagumi tana tunani ta ringa sa'ma sa'ka abubuwa tana kuma warware su da kanta.

*****
      Shi kuwa Mu'een har lokacin ya 'ki 'daga wayar ta sa ma a inda ya wullata balle ya kunna ta, haka zai yi duk abubuwan da suka zame masa dole ya yi shirin sa ya wuce makaranta ko kallo wayar bata ishe sa ba, wani sa'in ma bai zuwa makarantar sai dai ya yini a gida yana tunani...Ishaq ne yafi damuwa da lamarin sa, cuz sosai ya fahimci akwai abinda ke damun sa da yake so ya hana shi sukuni yake kuma faman 6oye musu.

    Watarana da bai shiga school ba sai Ishaq da Imran da wani abokin su Anas jibo suka taho gidan sa dan duba shi dan sau tari idan basu gan sa ba suka sha gwada 'kiran wayar sa amma bata tafiya dole suke hakura su bar sa.

Yau kam Ishaq yace suje gidan su dubo shi, tun zaman su da shi kuwa ranar shine rana na farko da suka ziyar ce shi har gida, yau din ma bazata suka yi masa da yake already sun riga da sun san gidan, Mu'een bai ta6a basu daman zuwa inda yake ba ko da wasa.

Da sallama suka shiga gidan inda suka zarce har ciki.

A palour suka tarar da shi kwance fuskar na kallon ceilling, jikin sa kuwa ko singlate babu balle riga wandon jikin sa ne dai dogon ba'kin jeans ya sanya...hannun sa 'daya ya lan'kwaso ta ta ratsa ta saman fuskar sa yayin da 'dayan kuma ya dafe saman 'kirjin sa da shi.

NOORUL✔️Donde viven las historias. Descúbrelo ahora