P18

489 32 2
                                    

💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)

By
*Salmerh MD*

 

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *18*

Batare da tunanin komai ba Ja'afar ya amince dan kuwa sosai yake da ya'kinin cewa Allah yana tare da su kuma shi zai taimake su, farin cikin sa 'daya kawai shine yau 'dan uwan sa zai kwana cikin gidan sa da iyalan sa .

Kamar yadda suka fa'da 'din kuwa hakan ne ya faru domin kullun yakan je yayi signing kamar yadda suka bu'kata har tsawon sati biyu batare da yayi fashi ba.

Ammi kuwa s
duk iya 'ko'karin da zatayi na ganin cewa ya amince an saida abubuwan data gada daga gurin mahaifin ta tanayi domin a biya bashin sharrin da aka tiwa mai gidan naga amma sam Taheer ya 'ki amincewa bai kuma sanar da ita da dalilin 'Kin amincewar yasa ba.

            'Bangaren shi Tahir 'din kuwa har cikin ransa yake jin tamkar idan yayi hakan bai kyauta mata ba duba da yanda wancen Lawyern ya damfare ta ya tafi da dayawa daga cikin dukiyar ta sannan 'dan abinda suka rage kuma yace zai yi haka dasu ai bai kyauta ba....shi aganin sa.

Ammi kuwa rashin amincewar tasa sosai ya bata haushi har ma take jin tamkar da'ace takaddun dukiyar na wajen ta da tuni tayi abinda zatayi sai da ya 'dau duk matakin daya ga daman 'dauka daga baya amma baby abinda zai hanata aiwatar da nufin ta.

Abin na damun ta sosai a duk lokacin da ta tuna cewa mijin ta matsayin mai laifi yake dan har fargaban dare yayi gari ya waye take yi sai take ganin kamar lokacin rabuwan ta da mijin ta ne yake 'kara kusanto ta, dan haka ranar wata talata ta fara bincike sosai cikin 'dakin sa da niyyan duba takaddun dake wurin sa.....domin sunyi magana dashi ko yana da wasu ku'dade cikin account 'dinsa sai yace mata bad
baza su haura 10million ba ku'din ita kuwa bata son rasa shi ta ko wani 6angare.

Gaba 'daya tayi kaca-kaca da 'dakin amma bata ga komai ba kuma tana da tabbacin a 'dakin suke bai kai su ko'ina ba dan haka sai ta cigaba da dubawa da fatan Allah ya taimake ta can su....kamar daga sama kawai ta ganshi tsaye a bakin 'kofa dan ko motsin shigowar sa ma bataji ba tsaban yanda hankalin ta ya tafi.

Suna ha'da idanu da shi sai ta diririce abinda ke hannun ta ya fa'di 'kasa, batayi zaton zai dawo  yanzu ba dan kuwa division yaje yin signing shiyasa ma ta saki ranta take binciken cikin kwanciyar hankali ko zata gansu tunda ya hanata ta da'din rai gara ta 'dauka tayi abinda ya dace dasu...ina amfanin ba'di ba rai" acewar ta kenan......

Da rawar murya tace dashi " har...ka....da wo?".
Sai yace
" Ke ma 'din na miki satan ne?"
ya tambaya a tsare batare da yabata amsar tambayar ta ba wanda daga jin yanayin muryar sa ma zaka san cewa ransa a 6ace yake.

Sai ta jijjiga kanta a hankali alamar " ah ah"
"So...?" Yace da ita da 'dagaggen gira 'daya.

Kwa6a fuska tayi kamar zatayi kuka gani da watsa hannayen ta tace dashi " please Taheer give me the documents i want use them...me yasa kake hakane wai?"

Cikin 'dakin ya 'karaso a hankali cike da 6acin rai ya nuna mata hanyar waje gami da fa'din " leave this room please"!

Tsayuwa taci gaba dayi cikin karya wuya da niyyan sake ro'kon sa amma kafin tayi magana  sai ya daka mata tsawan " i said leave from here now"!

Fita tayi a hankali tana matse 'kwallan takaici.....yayin da Taheer ya rakata da jajayen idanun sa har ta fita.

NOORUL✔️Donde viven las historias. Descúbrelo ahora