P79

528 51 13
                                    

💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)

By
*Salmerh MD*
 

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *79*

Hakan kuwa akayi domin  Noor cikin zuciyar ta ta ringa maimaiata _Innalillahi wa inna ilaihi raji'un_ har Hafsat ta dawo ta zuba musu abincin, a hankali ta fara ci amma sam sai nemi  natsuwar ta ta rasa, bugun da zuciyar ta ke yi sai 'kara yawaita mata yake yi, bata fi spoon biyar ba taji abincin ya ishe ta gaba 'daya, ruwa mai sanyi ta 'dauka ta sha sannan ta kwantar da kanta tare da lumshe idanu.

Ta 'dauki tsawon lokaci  a hakan Hafsat kanta bata iya fa'din komai cuz a yanda ta san Safwan da dukkan yanayin sa tasan da wani abu musamman yanda taji sauyi cikin muryar sa..amma da yake bata san ko menene ba shiyasa tayi shiru..fatan dai Allah yasa ba jikin Baby da mahaifin ta ne ya tsananta ba...tuno Sani da tayi ne yasa ta ta6e baki ashe har shima ba lafiya...

Wasa-wasa kusan mintina hamsin da uku suka 'dauka bayan wayar da Safwan ya 'kira sannan suka ji tsayuwar motoci kimanin uku daga harabar gida.

    Hafsat ne mai 'dan 'karfin hali dan haka ita ta fara mi'kewa tsaye yayin da zuciyar Noor ya amsa da 'karfi...'kafafun ta har na sar'kewa tabi bayan Hafsat Little Afrah kam tuni tayi baccin ta.

Ganin yanayin da su Ammi suka firfito daga motar yasa ta kasa motsawa daga inda take tsaye, bata san me yasa ta tsorata ba, a hankali idanun ta ya sau'ka kan  Bala Mai gadi da hannun sa duk biyu ke kansa yana kuma girgiza kan da alamun alhini.

Hakan ne ya 'kara tabbatar mata da cewa ba lafiya ba, gani tayi su Alhaji Baba, Safwan da wasu da bata ma gane ba sun tattaru wurin mota guda 'daya.
Dole cikin uku tasan akwai 'daya cikin Yah Deen, Jasmine ko Sani...Ammi ce ta taho wajen ta da sauri ta kamata tayi ciki da ita, da ka ganta kuwa zaka san cike take da damuwa, Noor dai kawai ta bita ne amma ba wai dan ranta yaso.ba, taso taga menene ya faru acan wajen, me su Alhaji suka taruwa gaban motar can.

Ji tayi kawai hawaye na gangaro mata yayin da zuciyar ta ya gama cika da waswasi..Ammi bata ce da ita komai ba har suka isa 'dakin ta da Ammi.
Anan ne Ammi ta fara bata ha'kuri da alamun kwantar da hankali  amma bata san dalilin ha'kurin ba..burinta kawai taji menene ya faru kuma.

Da 'kyar ta iya bu'dan baki tana hawaye ta tambayi Ammi" Me ya faru ne wai Ammi...?"
Kafin ta rufe bakin ta sai ji tayi murya kamar ta Hafsat tana Salati daga waje.

Ai bata san lokacin da ta zabura ta mi'ke da sauri ta fita ba, Ammi na 'ko'karin tarota amma ina ta riga tayi gaba.
.....turus taja ta tsaya sakamakon ganin abinda ke kwance a parlourn ta, gwiwoyin ta ta zuba a 'kasa kamar wacce hankalin ta ya bar jikin ta tana nuna abinda ta gani.

Da 'dayan hannun ta ta rufe bakin ta tana fatan Allah yasa zargin ta kar ya kasance gaskiya...Da muryar kuka batare da ta dubi fuskar Alhaji ba tace
" Alhaji Baba waye aka na'de haka?...Innalillahi...wa inna Ilaihi raji'un...Yah Allah kasa mafarki nake ba gaskiya ba..Hafsat waye wannan dan Allah?"
Da kuka ta rushe tana rufe bakin ta da dukkan hannuwan ta biyu, Ammi ce tazo ta kamata itama 'din hawaye take zubdawa...rungume kanta tayi a 'kirjin ta tana bubbuga bayan ta a hankali..tana fa'din" Kiyi ha'kuri Uwata...Kullu nafsin za'i'qatul maut...kinsan mutuwa dama dole ce..."

Bata jira ta 'karasa jin abinda Ammin ke fa'di ba tayi saurin barin jikin ta ta mi'ke ta tafi..jin cewa da gaske mutuwa akayi, kuma bata raba'dayan biyu 'yar ta ce domin duk cikin marasa lafiyan itace 'karama kamar yanda taga wannan abin.

NOORUL✔️Donde viven las historias. Descúbrelo ahora