P53

369 34 0
                                    

💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)

By
*Salmerh MD*
 

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *53*

Ishaq Babbar rigar jikin sa ya cire ya ajiye agefen sa sannan yace" Ai ka bari kawai mutanen nan 'kananun 'yan gabas ne wallahi...sai da fa muka gama shiri mun baza kunnuwa zamu ji an 'daura auren ka kawai sai ji akayi ya wakilci auren Husnah da wani daban, ashe ma wai wancen Hisham 'din 'dan sa ne na cikin sa, in ba rainin hankali ba yau ne yasan da zaman 'dan nasa da bai yi tunanin aura masa ita tun farko ba sai da ya bada ta ga wani ?...abin takaici ma wai sai daga baya bacin har an gama komai kafin ya zo yana bawa su Alhaji ha'kuri...a lokacin ji nayi tamkar in mare sa..."

Anas ne ya tare maganar tashi da fa'din.." Ai Alhaji ba 'karamin birge ni yayi ba, kai baka ga yanda ya nuna masa bai damu ba, sai ma wata kwantacciyar fara'a da fuskar sa ke haskawa...jikin Mutanen ai har sai da yayi sanyi 'yan rainin sense..".

Baki Yah Deen ya ta6e, cikin nuna halin ko in kula da batun ya furta" can musu su suka sani...ni dai Alhamdulillah kawai zance tunda an raba ni da ita".

Babu wanda ya ko kwatanta sanar da shi cewa an sake 'daura masa auren da wata  kawai suka bar shi da murnar sa na bai auri Husnah ba.


*****
   'Bangaren Husnah kam tunda taji cewa da Hisham aka 'daura auren ta bada Mu'een ba sai ta ringa kuka gwanin tausayi idan ka ganta, hawayen ta sam ya kasa tsayuwa, sai dai ita kanta bata san ainahin me take yiwa kukan ba, shin kukan an raba ta da Deeni ne ko kuwa kukan auren da akayi mata da Hisham?
A yanzu baza ta ce akwai soyayyar Mu'een cikin zuciyar ta ba balle tace taji haushin rabuwa da shi, sannan ta san Hisahm 'dan uwanta kuma mai 'kaunar ta amma me yasa ta kasa jin farin ciki da jin labarin aure tsakanin su? Ta riga ta shiryawa zama da Mu'een tuntuni, ta yiwa kanta al'kawarin zama da shi cikin ko wani irin hali.

Mahaifiyar ta kam jikin ta sanyi yayi da jin wani juyin da aka kuma yi, sam ta rasa me yake damun Alhaji Mamman a dauniyar nan, tsananin son kansa ya fiye masa yawa, wancan karon da ya bada auren Husnah batare da neman yardar ta ba ta yi masa uzuri da tunanin ko abokan sa ne iyayen yaron shiyasa amma duk da haka hankalin ta bai kwanta ba, wanda bata samu natsuwa ba sam har sai da ta tabbatar da cewa Husnah na son yaron sannan hankalin ta ya kwanta da auren, yanzu kuma bacin sun gama kwantar da hankalin su kan hakan sun kar6i auren sai ya kuma 6ullowa da wata sabuwar zance...wai auren Hisham da Husnah...she is totally speechless kan hakan

Husnah kam kukan ta na 'kara yawaita ne a duk lokacin da ta tuno da mahaifin ta, tasan da ace yana raye da duk hakan ba zai faru da ita ba, ta san da babu wanda ya isa ya ringa juya mata rayuwa batare da yardar ta ba, balle irin wannan juyi irin na rashin mutunci da 'kas'kanci 'karara hatta mahaifiyar ta ba'a bawa darajar da za'a shawara da ita ba, tasan ba kowa ne zai iya 'daukan hakan ba duk kuwa rashin gatan mutum.

Yini ta yi tana kuka, yayin da kanta ke tsananin yi mata ciwo amma sam bata damu ba, kafin maghrib kuwa ko motsin kirki bata iya yi da jikin ta saboda yanda kanta ke sarawa, idanun ta ma nawi sosai suka yi mata.

Lokacin da Mummyn ta fahimci halin da Husnah take ciki kuka ta sanya kawai itama, gani take kamar bata kula da maraicin Husnah ba, a 'yan kwanakin nan Husnah tayi kukan da be kamata ace tayi sa ba duba da yanayin shekarun ta, gani take kamar Allah zai tambaye ta akan hakan,  haka ta zauna gefen Husnahn tana faman sheshshe'ka itama, wata 'yar uwar tace dake tsaye dafe da kafa'dar ta take bata baki akan taya Husnah kukan bashi da amfani sam, bata ce da ita komai ba illah ro'kon ta da tayi akan ta 'dauko mata wayar ta.

NOORUL✔️Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang