P28

483 24 5
                                    

💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)

By
*Salmerh MD*

 

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *28*

Bayyanan niyar murmushi Alhaji Baba yayi sannan yace " wai 'yar sa ce daman duk wannan bayanin?"

" Eh ni dai bansan shi ba amma ance sunan sa Malam Mamman"
" to me yasa wanda ya fa'da makan bai gaya maka cewa tare muke aiki da shi ba?....a ina ma kaji...waye ya fa'da maka?"
Mu'een amsa shi yayi da fa'din
" wani friend 'dina ya gaya min tare muke 'kwallo dashi".

" To ai 'yar gidan Malam Mamman Jaji ce da muka baro shi yanzu a gidan gona, idan har 'yar wajen sa ce karka damu da iznin Allah baza'a samu matsala kan hakan ba ".

Wani sassanyan natsuwa yaji ta sa'k'ko masa har sai da ya lumshe idanu...." _Alhamdulillah_ " ya furta a fili.
   Zakuyi mamakin duk wannan abin na Mu'een bai ta6a magana da Nanne ba, tsakanin sa da ita ido ne kawai, bai ta6a koda gwada yi mata magana ba ba wai dan yana tsoron yi matan ba kawai dai nashi ra'ayin ne haka, sai de yaji sautin muryar ta agefe wanda a irin hakan duk ya haddace sautin muryar ta, zuwa yanzun kuwa ko cikin bacci yaji muryar ta toh take zai gane cewa itace.
      

           Ganin farin cikin da ya lullu6e fuskar Mu'een ne ya sanya Alhaji Baba fa'din " batun waina da ka daina ci fa..."
" me ya faru da  hakan kuma Alhaji?"
Alhaji Baba ne ya sake fa'din
" wainar gidan su ce to mahaifitar ta ke yinsa".

Gira 'daya ya dage sama " wai dan Allah dagaske ?" Ya tambayi mahaifin nasa.
Alhaji Baba ma batare da ya kalleshi ba yace " ina yi maka karyane?"
Cikin nuna rashin damuwa Deen yace " to ai ban sani bane shiyasa amma daga yau zan koma ci kullum".

Ajiyan numfashi Alhaji Baba ya sau'ke dai-dai lokacin da zasu shiga cikin gida.



〰〰〰
  Washe gari Umman mu bata yi waina ba dan tana 'dan jin fever hakan yasa banje gidan da safiyar ranar ba.

Karfe sha 'daya Yah Deen ya bar Shuwarin ya koma Azare...dayake ma ba wani shiri mukeyi da shi ba shiyasa ban san da labarin tafiyar tasa ba kuma ko da nazo bangan shin bama ban wani tuna dashi ba sam.

Alhaji Baba bai sanar da Baban mu batun da suka tattauna da Mu'een ba dan gudun kar yace dan yana yi masa aiki ne shiyasa....duk kuwa da cewa ba 'karamin farin ciki yayi da faruwar lamatin ba dan a ganin sa M. Jaji mutun ne da kowa zaiyi sha'awar hada zuri'a dashi musamman saboda gaskiya da ri'kon amanar sa, Alhaji cikin ransa ya ri'ke abin sai dai a fakaice yake kula da duk wani abinda ke tafiya, yayin da cikin ransa yake tsoron ranar da zaiji cewa an bada auren ta ga wani daban, idan hakan ya faru ya zai yi da amanar Mu'een da ya kar6a...kullum tunanin Alhaji Baba kenan.

    Gashi a kullun in har za suyi waya dashi sai yayi wayon da ya tunatar da shi amanar sa....da haka Alhaji Baba ya fahimci cewa da gaske fa Mu'een ya keyi ba da wasa ba.

    Ni da Nanne mun kai kusan 3weeks bamu sake ganin Mu'een ba, ni ban damu ba dan dama ba wata ala'kar kirki bace tsakanin mu bayaga gaisuwa shiyasa ma har yau 'din ban nemi jin ina yake ba.....sa6anin Nennen mu da kullum sai tayi min maganar sa, ba ni kadai bama ko cikin 'kawayen ta basa ta6a rabuwa batare da an ambace shi ba...ga dukkan alamu kuwa hirar tasa tafi musu da'di koda wani lokaci.

NOORUL✔️Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon