P64

477 46 9
                                    

https://www.facebook.com/106273870926057/posts/149762286577215/?app=fbl
💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)

By
*Salmerh MD*
 

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *64*

Yanzu Ammi ta daina damuwa da ni saboda taga na 'dan saki jiki na, kuma ko na shiga wurin san bana sake fitowa.

Abu 'daya dai da kullum baya raba ni da ita shine kafin in shirya in tafin sai ta tisa 'keya ta nake tafiya wanda burin ta kawai a kullum yanzu shine taga tafiyar na tafin matu'kar na riga na shiga 6nagaren nasa shikenan itama sai ta wuce shiyasa ma ko da ya aiko nin 'dauko masa ruwan tun fitowa ta na farko ban tadda ta a parlour ba.

Yanzun kuwa da na fito jin yanda 'kafafu na ke sar'kewa da yanda 'kirji na ke dokawa ne ya sanya ni samun wuri na zauna akan kujera na 'dan maida numafshi na.

Sai da na tabbatar na samu natsuwa kafin na tashi na canzo masa ruwan, ko da na shiga 'dakin kuma sai ban gan shi ba.

Da'di naji har cikin raina, da sauri na 'karasa dan inyi in ajiye masa inyi baccin 'karya kafin ya tuhume ni amma tun kafin in 'karasa tsakiyan 'dakin na gansa ya fito daga bayi kamar dama jiran shigowa ta yake yi, take wata fargabar ta sake kamani mai tsanani.

Jikina sanyi 'kalau na 'karasa na ajiye masa ruwan gefen da na same shi 'dazu ko iya sake kallon inda yake ban yi ba...'dagowa nayi da niyyar isa nawa 6angaren in kwanta sai naji nayi karo da mutun ta baya na, da sauri na waigo cike da firgici da ya bayyana har kan fuska ta.

Kafin nayi wani yun'kuri sai naji hijab 'di na ya bar jiki na gaba 'daya.

'Kan'kame jiki na nayi zan saki kuka sai yayi saurin dakatar da ni da tsare ni da idanu tare da tsaida yatsan sa saman bakin  sa.

Taimako 'daya Allah yayi min kayan bacci na masu yalwa ne riga mai botila da kuma dogon wando farare ne masu zanen flowers maroon amma duk da haka sai naji na kasa sake wa a gaban sa.

" Miye matsayi na a wajen ki?"
Naji ya tambaye ni bayan ya cire hannun sa daga bakin nasa.

Ban bashi amsa ba sai nayi baya ka'dan ina dama fuska ta amsar da zan bashin sam banji ta cikin brain 'dina ba.

Biyo ni yayi da taku 'daya zan sake matsawa baya kawai sai naji ni jikin bed na...take hawaye ya gangaro min tsoro ya kamani cuz ba wurin guduwa kuma.

Yanda naga yake kallo na ya sani sake yun'kurin neman hanya inda na sake yin baya zuciya ta cike fal da tsoron sa, cikin rashin sa'a sai na fa'di da baya na kan bed 'din ina neman hanyar zamewa sai naga ya matso daf da ni, fuskar sa kusa da tawa, kallo na ya tsaya yi daga idanu na zuwa dukkan ilhirin fuska ta...yayin da zuciya ta ta cigaba da dokawa da sauri da sauri jiki na ya fara kakkarwa sosai.

Da hannun sa naga ya shafo kansa tare da juya idanu..." Ba ance ni mijinki ba ne?"
Naji ya sake fa'di cikin jan maganar kamar dole aka sanya shi.
Saboda ina so ya 'kyale ni nayi saurin 'daga masa kaina sama alamar " Erh"
Sai yace" To daga yau banson wannan abin a inda nake.. kinji ko?"
Yayi maganar tare da 'dago hannun da ya ri'ke Hijab 'dina da shi dayake har a lokacin yana na'de a hannun sa.

Kaina na sake 'dagewa ina bin hannun san da idanu kuma har a lokacin jiki na bai daina rawa ba, buri na kawai inji ya bar kusa da ni...shiru ya 'dan biyu baya na sakanni, yayin da ya cigaba da 'karewa fuska ta kallo batarecda ya 'karacfa'din komai ba idan na yun'kura sai ya tsare ni da idanun sa dole na ha'kura illah hawaye.

NOORUL✔️Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon