P87

279 38 4
                                    

💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)

By
*Salmerh MD*
 

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *87*

    Bai fito daga motar ba sai da ya tabbatar basu yi kuskure ba tukunna...sai da aka yi  musu iso wurin Alhajin ya bada Umarnin su shigo kafin ya fito daga motar.

Zama suka yi suna jiran zuwan sa dan a lokacin yana tare ne da wasu costumers 'din sa,  zaman jiran sa suka yi a inda aka tanadar musamman saboda saboda ba'ki...P.A in sa na tsaye ne daga gefen sa wanda ganin hakan yasa Abban Jiddah bashi umarnin su jira shi wurin mota dan wannan personal issue ne.

   Hakan kuwa akayi P.A  komawa yayi ya bu'de mota ya shiga yana jiran fitowar Ubangidan nasa.

Gyara zaman Abban Jiddah yayi ha'di da murmushi tuno yawan 'kiran da Jiddah tayi masa daga lokacin da ya bar gida zuwa yanzu..ko bayan shigowar su garin nan ma sai da ta yi 'kiran sa burin ta kawai shine taji cewa an amince da batun aura mata shi.

Yana murmushin yake bin cikin wurin da idanu... sosai lambun ya birge shi saboda akwai ni'ima sosai, 'kasan wajen luf-luf yake da korayen ciyayi masu birgewa awani 'bangaren ma har design aka cire da shi ya kuma bada ma'ana mai kyau abin sai wanda ya gani.

Murmushi maahifin Jiddah ya sake yi, cikin ransa yake tuno rigima irin ta Jiddah" 'Dan gidan mai lambu...".
Ya furta a fili inda ya 'karasa da murmushin mugunta.
Gyara zaman sa yayi yana sake bin ko'ina da idanu.
Wannan karan cikin ransa ya furta" Da alamu Naira zata yi amfani tunda naga akwai 'dan kashi..."
Ya 'karashe da jinjina kansa.
Cigaba yayi da sa'ka abubuwa cikin ransa yana me sake bin lambun da idanu.
"Jin sa kawai yafi ganin sa, 'kila da hakan ya yaudari zuciyar Jiddah har ta fa'da tarkon sa... gashi nima yasa na taso ba shiri saboda fitinar ta...ai da nasan hakane da aike kawai zanyi a gama komai ba sai nazo ba".
Ya 'karashe wannan tunanin da canza yanayin zaman sa ya karkace gefe guda, 'kafar sa 'daya ya mi'kar bayan ya cire takalmin sa ya maida 'kafar akai yayin da ya 'dayar ke tan'kwashe.

Hannun sa 'daya ya 'dago ya tallafi gefen fuskar sa da shi..a hakan sai yafi jin da'din 'karewa lambun kallo da kyau.

Baki ya ta6e lokacin da yaga manyan motoci guda biyu dake 'ko'karin fita daga lambun da alamu muhimmin abu ke gaban su duba da yanayin da yaga suka figi motocin.

Sam bai kula da tahowar Alhaji Baba ba dake tahowa kansa 'kasa yana gyara zaman babbar rigar dake jikin sa...Sanye yake da shadda wagambari mai kalar madara wanda duban.farko zaka fahimci maku'dan ku'daden da aka kashe kafin samuwar kayan.

Idanun sa na wani wuri can da ya 'dauki hankalin sa ga kuma haushin.6ata lokacin sa da yayi wurin zuwa wannan garin da yayi... har Alhaji Baba ya 'karaso kusa da shi har ma yayi masa sallama amma bai ji sa ba.

Sai da Alhaji Baba yayi gyaran murya kafin Abban Jiddah yayi saurin ankarewa.

Waigowa yayi domin.ganin.wanda ke masa sallamar nan take sai suka ha'da idanu da juna.

Cak Alhaji Baba ya tsaya yana duban sa cikin idanu yayin da mahaifin Jiddah yayi saurin mi'kewa tsaye har yana 'ko'karin fa'duwa amma ya yi sa'a be fa'din ba.

Alhaji Baba duban sa yake yi da tunanin in da ya sanshi, domin fuskar sa sosai tayi masa kama da wanda ya sani amma ya kasa tunawa.

Mahaifin Jiddah jikin sa rawa ya fara da tunanin Allah yasa mafarki yake ba gaskiya ba, gaba 'daya ya rikice ya rikita zuciyar sa, kallon da Alhaji Baba ke yi masa na a ina ya sanshi ne..yayin da shi kuma da ke tsarge yake sai yake ganin tamkar kallon tuhuna yake yi masa.

NOORUL✔️Место, где живут истории. Откройте их для себя