P59

475 40 2
                                    

💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)

By
*Salmerh MD*
 

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_*Daga marubuciyar Littafin CAPTAIN ABBAS*_

💕💕 ~*This page is 4u Dear Zainab Kabir Ingawa...Alkhairin Allah ya kai mk duk inda kike...nagode sosai da 'kaunar ki gare ni.*~💕💕

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *59*

Addah ta Maryam ma tazo da wasu 'yan uwan mu a hakan ma abin yazo ne cikin lokaci 'kan'kani amma duk da haka ba laifi gidan mu ya tara jama'ah ka'dan.

Itama Addah Maryam tayi mamakin faruwar lamarin yanda yazo agaggauce, ta yi 'ko'karin ganin ta samu cikakken bayani daga bakin Ummahn mu amma hakan bai samu ba, sai da suka zauna da Addah Saudah shine tayi mata bayani gamsashshe a fahimtar ta, tace Baban mu ne ya matsa akan dole sai an kai ni 'dakin na saboda labari ya iske shi cewa Mijinnawa shine ke da alhakin cikin dake jikin Ma'u 'yar gidan malam Barau shiyasa Baban mu yace agaggauta kai masa matar sa a tunanin sa ko laifin nasu ne da tun farko ba su bashi matar sa ba suka bar ya a gida..inda ta 'kara da fa'din ni.nama yi mamaki wallahi ban zaci Baban mu zai kuma amincewa da zaman Hudah tare da yaron ba bayan jin abinda ya faru sai ga shi da kansa kuma yayi umarni da akaita gidan sa batare da ya koyi tunanin me hakan zai haifar ba".

Baki kawai Addah Maryam ta ta6e tare da kawar da kanta gefe bata iya ta furta komai ba, sai dai har cikin ranta bata ji da'din maganar ba sam...aganin ta ba haka ya dace ayi ba..kamata yayi a bar Hudahn agida tukunna inma ba zasu iya raba auren ba har sai an tabbatar da shiryuwar sa kafin abrta zama dashi baya ga haka taya za'ayi a 'dauki yarinya 'karama kamar ni abawa mutumin da bai san ciwon kansa ba Baban mu yana nufin bai damu da abinda ya farun bane ko me? ..taso su tattauna maganar da Ummahn mu amma bata samu fuska ba hakan yasa dole ta ha'kura tayi shiru da bakin ta.

Ana gobe za'a kaini gidan Yah Deen Saif yazo gidan mu shi ka'dai hr naso ma nayi msmskin ganinsa shi ka'dai 'din amma sanin ba'kin hali irin na Zaidu yasa mamaki na ya kau ...y Saif yasha Jumpa milk colour da hula kamar wani babba, fuskar sa fayau sai 'dan 'kasumba da ya fara tarawa, yayi kyau sosai abin sa...a 'dakin Baban mu aka masa masau'ki inda aka yi 'kirana bayan sun gama gaisuwa da Ummahn mu.


Jin cewa Saif necyazo ya sani tahowa cikin tsananin farin ciki, jiki na da doguwar rigar material sai 'dan 'karamin ba'kin mayafi da na yane kaina da shi...fuska ta da fara'a muka gaisa da shi na tambayi su Ammi da Zaidu..yace min lafiyan su qalau.

" Meya sameka kai in kuma?"
Na tambaye shi ina kallon fuskar sa.
Take ya amsa ni shima da tambayar" Me kika gani?"
Nace" Kamar baka da lafiya".
Yace" Ni lafiya ta qalau".
Ya 'karashe maganar yana suman shafo kansa.

Shiru nayi ban kuma fa'din komai ba cikin rains nake tunanin abinda zai iya sashi canzawa haka cikin sau'ki dan nasan Saif ba haka yake ba...tashin farko tunanin na kan Yah Deen ya sau'ka cuz a sani na shi ka'dai ne ke takurawa su Saif a gidan..baki na ta6e cikin raina nake fa'din" Har yanxu ba zai canza hali ba".

Lallen dake zane a hannu na naga yana kallo ban damu ba sai ma nayi murmushi da fara'a ta nace 'dazu da safe aka zana min yayi kyau ko?..har an min kitso ma 'kanana zafi ma kaina yake min har yanzu".

Ido ya tsura min yana kallon fuska ta kamar wanda ke son gano wani abin acikin idanu na....Nima 'din sai nayi shiru ban kuma cewa komai ba.

Cikin sanyi ya ambaci sunana sai na amsa nima a hankali jin yanda yanayin muryar sa ya koma.
Yace
" Hudah dagaske Yah Deen mijinki ne yanzu?"

NOORUL✔️Where stories live. Discover now