P12

566 39 4
                                    

💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)

By
*Salmerh MD*

 

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *12*

Farin ciki ne mai tsanani ya ziyarci zu'katan su, Deen kam ji yake tamkar ya taka rawa, _Alhamdulillah....Alhamdulillah_ kawai yake furtawa a fili ba tare da damuwa ba.

Yayin da Noor ke faman hawaye da murmushi lokaci guda idanun ta kan Jasmin 'din hannun ta kuwa na gefen fuskar ta.

Ta 'dayan gefen bed 'din Deen ya koma ya ri'ke hannun ta yace " Jas 'din Daddy kin tashi?"

Jasmine sai ta 'dage kanta sama a hankali tana kallon shi daga kwancen.

" ina ke miki ciwo yanzu ?"
Ya sake tambayar ta da kulawa cikin sassanyar murya.

Shiru Jas tayi tana kallon fuskar shi batare da ta bashi amsar tambayar tasa ba.
A hankali ta maida idanun ta kan Safwan inda nan take ta 'dan tura baki a hankali ta bu'di tace " Daddy kaga Uncle Safwan yayi min allura ba? kuma ni ai lafiya na 'kalau Sani ne yace bashi da lafiya 'dazu".
Tana maganar cikin shagwa6ar ta da ta saba yi masa.

Murmushi Deen yayi inda ya da'da ran'kwafowa ha'di da kai hannun sa 'daya yana shafo kanta yace " kar ki damu kinji mamana, shima ai Sanin an yi mishi alluran har guda uku ma, yanzu ina ke miki ciwo?"  Deen ya 'karasa maganar tasa da tambaya yana me cigaba da shafa kanta.

Jas sai tace
" Ciwo?"
Ta sake mai maita abinda ya fa'da 'din.

Shima sai yace " uhmm fa'da min inji ko mamana, kanki na ciwo ne?"

Jijjiga kai Jas tayi a hankali alamar ah ah
" cikin ki fa ?"
Ya sake tambayar ta.

Sai kuma tayi shiru tana 'kara turo baki.

Noor kam tagumi tayi tana binta da kallon jin da'di jin har tana yi musu hira, ashe da gaske ne da Yah Deen yace " nata ciwon da sau'ki ba kamar na Sani ba......hamdala kawai take ta zubawa mahallici.

Jas ne taci gaba da fa'din " ai 'kafana na min ciwo da 'dan 'dina..."
Tayi masa nuni da bandages 'din dake kanta.

" Ayyah....sorry baby kinji, soon zai warke insha Allahu".

Sake 6ata rai Jas tayi sosai sannan tace " Daddy!"

Deen ma sai yace " Na'am 'yar gidan Daddy ina jinki akayi ?"

" Ba sani bane ya cinye min bakina a mota ba kuma ya rufe min bakin da 'karfi har ina jin zafi....., banyi pupu ba a school kuma ko fitsari ma banyi ba amma ya min tsarki mai zafi......ni kam Daddy kace mishi bana so.......".

Wani dumm dukkan su suka ji tamkar sau'kan wani abu mai nawi a tsakar kawunan su, yayin da idanuwan Noor duk suka firfito waje ta zuba su akan Jasmine tana kallon ta.

Deen ma kansa tsura mata idanu yayi yana faman harha'da bayanan nata wuri guda domin so yake ya fahimci ma'anar su.

Inda karon farko tunanin sa ya basa a kan zancen nata da inda ya dosa gaba 'daya sai yaji wani  bambabara'kwai kamar ba hakan bane........'dan jijjiga kansa yayi tare da fa'din " no ths can't be".
Still yana ri'ke da hannun Jasmine cikin nasa.

'Dagowa yayi ya kalli Noor da bakin ta ke faman 6ari tana son furta magana amma ta rasa me zata ce ma kwata-kwata, domin ita tashin farko batare da wani dogon nazari ba ta fahimci inda maganar ta dosa.

NOORUL✔️Donde viven las historias. Descúbrelo ahora