Chapter Six

447 43 0
                                    

Haka summy ta dinga kokarin kwantar mata da hankali har ta samu ta dan sauko.
"Ban ma fada miki ba huda, jiya muhseen ya aiko mun da sako. Bari kiga". Summy tasa hannu cikin jakarta ta ciro wata tsarka mai shegen kyau ta nuna mata.

Huda tayi kokarin dane wani abu data ji ya taso mata, ta karba tsarka tana binsa da kallo, sai faman juyawa takeyi  a hanunta. murmushi ta kirkiro a fuskarta sa'anan tace "yayi kyau summy, gaskiya muhseen yayi kokari. Kice mishi muna godiya. Allah ya saka da alkhair".

"Ameen, yama ce mun nan da kwana uku zai dawo. Bakiga farin cikin dana kwana cikinta ba jiya". Summy ta fada sai faman washe baki takeyi.

Huda ta danyi shiru daga bisani tace " summy na tambayeki mana"

Summy ta dubeta sa'anan tace "inajinki"

" kin fadawa muhseen kinada matsalar kafa kuwa?"

Huda na jefo mata wanan tambayar nan take summy taji gabanta ya fadi, murmushin dake fuskarta ta dauke.

Girgiza mata kai tayi tace "a'a huda, ban fada mishi ba, ban ma san taya zan fara fada mishi ba" ta karasa maganar hankalinta a tashe.

"Ai ya kamata ki fada mishi, kar yazo ku hadu kuma yaga kamar kin yaudareshi. Akan haka ma kinga zai iya cewa zai rabu dake"

"Nasan ya kamata na fada mishi lalurar da nake fama dashi amma na kasa huda, banjin zan iya don ban ma san taya zan fara ba. Ni kaina abun yana damuna wlh. Summy ta karasa maganar kamar zatayi kuka, Gabadaya hankalinta a tashe yake.

Huda tace " kiyi hakuri summy, banyi wanan maganar da niyar daga miki hankali ba ko wani abu ba, kawai gani nayi ya kamata ace muhseen ya san da wanan maganar, bai kamata ace kin boye masa abu mai muhimanci irin wanan ba"

Summy ta mararaice fuska ta soma fadin  "huda kar muhseen yazo yace ya fasa don ban san inda zan sa kaina ba, bazan iya rabuwa dashi ba, idan muhseen yace zai rabu dani wlh mutuwa zanyi.

"Insha Allah muhseen bazai rabu dake ba, kiyi kokari kawai ki sanar dashi kar lokaci ya kure".
Summy tayi shiru Gabadaya jikinta yayi sanyi. Tunani kala kala na mata yawo aka daga bisani tace " Toh shikenan huda, naji insha Allah zanyi kokari na fada mishi"

"Yauwa kawata, ki kwantar da hankalinki kinji".
Anan suka tsayar da maganar suka fita daga ajin.

Bangaren gidansu huda kuwa, ammi ce ke kofar gida gaban sana'arta. Jama'a sai shiga da fita sukeyi daga cikin rufan suna cin abinci. Ba jima ba sai ga anty rakata tazo wucewa, taga ammi tazo ta tsaya suka gaisa. "Ummul Amma ina kwana, ya kasuwa?" Ta gaisheta da yaren shuwa.

Ammi fuskarta dauke da fara'a ta ansa mata da " lfy lau rakata, kuma kasuwa alhamdulillah. Ya yaran?"

"Lafiyan su lau wlh". Bayan sun gama gaisawa Anty rakata ta danyi jimm daga bisani tace "amma ummul ammabuwa, ya huda da karatunta?"

Ammi ta dago tana dubanta, don tasan anty rakata sarai da surutu da kuma shiga cikin abunda babu ruwanta. " karatunta na tafiya lafiya, meyasa kike tambaya? Wani abun ne ya faru?"

"A'a ba abunda ya faru ummul amma kawai dai inaso naga ranar da zaki huta ne da wanan aikin wahalar. Kinga idan Allah yayi huda ta gama karatunta ta samu aiki mai kyau ai kinga kin huta".

Ammi ta danyi shiru daga bisani tace.         "Allah ya nuna mana wanan lokacin".

"Ameen" ta bata ansa, maimakon ta kama hanya tayi gaba sai kuma ta cigaba ta fadin "amma ummul Ammabuwa, nasan  huda tana zuwa makaranta amma baki ganin ya dace itama ta samu wani aikin itama tana dan yi, ai ko dan dinkin nan ta samu tanayi shima wani abu ne, kinga nauyin ma zai dan ragu wa Ammabuwa harta ke ma za ki dinga hutawa".

🔥Huda🔥💄Where stories live. Discover now