Chapter Sixty

189 17 0
                                    

Suna cikin haka sukaji ana sallama, mikewa Ammabuwa tayi ta fita. Nan ta tadda Abdul yana tsaye sanye cikin kayansa na likitoci da alamu daga asibiti ya nufo nan kai tsaye.

Bayan sun gaisa, yace mata yazo duba jikin Ammi ne. Tace mishi bisimillah ya shigo.

Abdul ya karasa ciki yaje ya soma duba jikin Ammi, bafi 10 minutes ba sai gashi nan ya fito.

Ammabuwa ta soma tambayarshi ya yanayin jikin, yace "jikinta da sauki yanzu Alhamdulillah. Na sake duba pulse rate dinta, komai ya dawo normal yanzu".

Ammabuwa tace "toh Alhamdulillah, mun gode kwarai da gaske Abdul Allah ya saka da alkhair"

"Ameen, daman inaso na baki documents na account dina da kika ce zaki tayani yi".

Ammabuwa ta karba documents din daya mika mata tana murmushi tace "karka damu insha Allah zan samu na kammala maka zuwa gobe".

Abdul yana murmushi yace "Nagode Ammabuwa, you've saved me alot of work wlh".

Anty Rakata dake zaune a gefe tana jinsu ne tayi karap ta mike tana fadin "toh Ammabuwa ni zan wuce yanzu. Amma waenan kayakin ya kamata ki shiga dasu, bari ma na tayaki shiga dasu ciki. Nasan waenan na Amminku ne, wanan kuma wani saurayinta ne ya kawo mata kayan dazun" ta karasa maganar tana kallon dr Abdul wanda ya tsaya yana kallonta cike da mamaki yana kokarin ya fahimce inda maganar nata ya dosa.

Ammabuwa kusan mutawan tsaye tayi a wajen jin abunda Anty Rakata ta fadi, kamar kasa ta bude ta fada ciki tsabar kunyar. Muryanta na rawa tace "kai Anty Rakata, yaushe Mahmud kuma ya zama saurayina".

"Saurayinki ne mana, tunda ya nuna yana sonki".

Abdul dariya ya dan'sake wanda bai kai ciki ba yace "wow Ashe Ammabuwa kinyi saurayi, toh congratulations." Ya karasa maganar yana kafeta da fine eyes dinsa.

Ammabuwa gabadaya rikicewa tayi ta soma yiwa Anty Rakata alamu da ido da tayi shiru amma inaa Anty Rakata taki yin shiru sai faman zuba takeyi.

Haka Ammabuwa tayi shiru tana jinta cike da takaici.

Shikam Abdul dariya kawai ya dinga yi daga bisani yace zai wuce yayi musu sai da safe.

Har kofar gida Ammabuwa ta rako shi ta soma bashi hakuri akan surutun Anty Rakata, yayi dariya yace "karki damu Ammabuwa. It's just that kin cika serious n baki sakewa sosai. Ko da'an taimakon nan ma kina avoiding daga wajen mutane saboda bakison commitments. You're too..."

"Old fashioned koh?" Ta karasa masa maganar tana dariya.

Shima dariyan yayi yace "eh toh, da wanan ma. Akwai banbanci sosai tsakaninki da yar'uwarki".

"Hmm haka ne you're right, nida ita we have different perspectives kowa da yanayin da yake kallon rayuwa, kilan shiyasa nida ita muke yawan samun rashin ji'tuwa tsakanin mu. Amma ina matukar kaunar kanwata har cikin raina Abdul, Yanayin da take tafiyar da rayuwarta ne kawai bana amana dashi".

*********************

Bangaren su Huda kuwa, tsaye suke a gaban mudubi, ita da Summy tana tayata shiri.

Kirjin Summy sai faman harbawa yake, jikinta na bari tace "Huda kina tunanin wanan gown din zatayi fitting dina?"

Huda tace "zatayi fitting dinki mana. Kinga Summy ki kwantar da hankalinki. Saboda Kinga wanan karan Muhseen tare da kawunsa zai zo, inaso ki tattara wa kanki nutsuwa, you need to be confident kuma kiyi kokari kina tafiya da sauri, kinga nan zai gano cewa lalurar kafar naki bai dameki ba, zaki iya tafiyar da komai naki normal".

Summy tayi shiru daga bisani tace "matsalar ban saba tafiya da sauri bane ba ai Huda, kar naje na fadi".

"A hankali zakiyi Summy. Shiyasa nace ki kwantar da hankalinki. Kinga kyaun da kikayi kuwa". Huda ta fada tana da'an gyara mata makeup din fuskarta.

🔥Huda🔥💄Opowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz