Chapter fifty- five

176 23 2
                                    

Bangaren su Ashraf kuwa, har ya kammala aikinsa ya koma gida.

Muhseen yana ganinshi cike da murna ya soma zayano masa yanda sukayi da kawun nasa yace "Ash, yau dai an samu nasara! Na samu na shawo kan Daddy ya amince da batun auren nan. Duk da dai baya son auren don yana tunanin Summy bata dace dani ba amma na samu na fahimtar dashi".

Cike da jin dadi Ashraf yace "kai! Amma naji maka dadi wlh, yanzu kana nufin ka samu ka shawo kan Daddy? Toh Allah ya tabbatar da alkhair! I'm so happy for you wlh. Kuma karka damu, da sannu zai gano cewa kayi babban dace samun summy a matsayin mata".

Muhseen yana dariya cikeda jin dadi yace "haka ne abokina. Ban ma tambayeka ba, Ya jikin mahaifiyarsu Huda?"

Ajiyar zuciya Ashraf ya sake sa'anan yace "eh toh Alhamdulillah, da sauki kenan za'a ce amma mun gano wani abu da bai mana dadi ba wlh".

"Me kenan?" Muhseen ya tambayeshi.

"Scan da muka mata ya nuna cewa tanada brain aneurism, wani jijiya ne yake cike a jini cikin kwakwalwarta kuma idan har aka bari jininta ya sake hawa kamar yanda ya hau yanzu toh komai zai iya faruwa".

Muhseen hankalinsa a tashe yace "toh yanzu babu wani abun da za iya yi akai kenan?"

"Gaskiya babu, don baza iya mata operation ba, sai dai a kiyaye kawai"

Ajiyar zuciya Muhseen ya sake yana jinjina lamarin.

*****************

Washe gari da safe, Ashraf yana isa asibiti zai shiga ciki kenan yaci karo da Huda itama ta fito zata wuce makaranta.

Tsayawa sukayi suna kallon juna na da'an mintuna, zucuyoyinsu na harabawa da karfi.

Ashraf ne ya karaso yazo ya tsaya a gabanta, wani irin ajiyar zuciya ta sake data ji kamshin turarensa da take matukar so ya bugi hancinta.

Ashraf cike da sanyin murya yace "Huda ina zaki haka?".

"Makaranta zani". Ta bashi ansa kai tsaye tana kallon cikin kwayar idanunsa.

Ashraf yace "Ammabuwa ta fada miki abunda scan ya nuna ko?"

Cike da sanyin jiki tace "eh ta fada mun".

Ashraf yace "karki damu, insha Allah idan aka kiyaye babu abunda zai sameta, zamu cigaba da bata duk wani kulawan da take bukata, everything will be fine insha Allah" ya karasa maganar yana kokarin dadda matsowa inda take.

Huda ta dakatar dashi tana fadin "a'a Ashraf, please don't come any closer ka tsaya inda kake".

Bai saureta ba ya dadda matsowa yana fadin "meyasa? Tsoro kikeji? Ko kuma baki so kiyi accepting cewa sona yana nan fal cikin ranki kuma bazaki taba iya cireshi a ranki ba?"

Zatayi magana ya katseta da "indai akan Amminki ne karki damu, zan kular miki da ita, ki fada koma meya, zanyi muku Huda. Nasan yanzu banida wani karfi sosai amma inada rufin asirina daidai gwargwado da Allah yayi mun".

Huda ta marairace masa kamar zatayi kuka don wani irin kokuwa takeyi da feelings dinta tana kokarin danne su karsu sawo kai. Bata son wani abunda zai sake hadata dashi amma ta kasa daina tuaninsa, da zaran ta ganshi nan take sai taji feelings din na sake dawo mata sabo. Ta rasa yanda zatayi ta cireshi daga cikin ranta. Kokarin danne abunda taji ya taso mata tayi tace " Ashraf kaima kasan bazai yu' ba don i'm still the same, bazan iya canzawa ba".

"Huda zaki iya canzawa, zai iya daukan lokaci amma idan har kika sa kanki, you'll see changes. It all depends on you. Kuma ina miki wanan maganar ne don a shirye nake da na kasance tare dake a duk yanda kike, flaws and all I'm willing to accept you, zan cigaba da sonki a hakan. Nima ina so kiyi accepting dina a hakan".

Kallonsa kawai takeyi yana magana, gabadaya a rikice take da shaukin sonsa. Kyakyawar fuskarsa da daddaden muryansa na sake jefata cikin kogin sonsa.

Suna cikin haka, sai ga Summy nan ta taho tana kiran sunanta.

Huda najin muryan Summy wani irin freeze tayi, nan take taji wani irin haushi ya turnike ta.

Summy ta karaso tana fadin "Huda Allah yasa na ganki anan. Daman nazo ne na duba jikin Ammi. Ina kwana Ashraf". Ta karasa maganar tana murmushi tana kallon Ashraf.

Ashraf shima murmushin ya sakar mata  yace "ina kwana Summy, an tashi lafiya?"

"Lfy kalau lau Ashraf".

Ashraf ya dubi Huda yace "ni zan wuce ciki yanzu doctor Dangora yana jirana. Sai zuwa anjima and please karki manta nidake bamu gama magana ba, zan kiraki a waya idan na gama abunda nakeyi".

Bai jira yaji ansar da zata bashi ba ya bar wurin cikin sauri.

Bayan Ashraf ya tafi, Summy tace "kiyi hakuri, nazo na katse muku maganar da kukeyi".

Huda tace "babu komai mu karasa ciki mana".

Tare suka karasa  cikin asibitin, suna tafiya Huda na zayano mata abunda likiti yace a game da lafiyar Ammi.

Sosai Summy itama ta shiga cikin damuwa tace "yanzu toh ya za'ayi kenan Huda?"

"Kawai zamu cigaba da mata addu'a ne kuma mu dadda kiyayewa."

Summy ta sauke ajiyar zuciya tace "karki damu insha Allah zata samu lafiya, kuma kamar yanda na fada miki, idan har akwai wani abun da ake bukata ki sanar dani karki ji shakkan komai kinji kawata".

Huda tace "toh Summy, nagode kwarai da gaske. Allah ya bar zumunci."

"Ameen, jiya munyi waya da matar kawun Muhseen. Kuma maganar da kika fada mun gaskiya ne".

Huda zaro ido tayi tace "badai kin fallasa ni kince mata ni na fada miki ba?"

"No... no ban fada mata ba, kawai dai munyi magana akan yanda abubuwa zasu kasance ne. Da farko dai na tsorata sosai don nayi tunanin za'a fasa auren ne".

"Yanzu kina nufin baza'a fasa auren ba kenan?" Huda ta tambayeta kirjinta na harbawa don ita ta rigada ta gama sa rai cewa auren Summy da Muhseen za'a fasa tunda kawun nasa baya so.

Summy tana murmushi tace "a'a Mommy ta dadda kwantar mun da hankali, tace ta tabbatar Muhseen yana sona, kawun nasa ne kawai yakeda wuyan sha'ani amma  insha Allah zata sake zaunar dashi suyi magana, zai sauko. Ai Huda Naji dadi da kika fadamun wanan maganar, kinga hakan ma yasa mun sake shakuwa da mommy don jiya mun jima muna waya da ita. Nagode kwarai da gaske Huda".

Kallonta kawai Huda takeyi can kasan ranta tana fadin "tabdijan, yanzu hakan yana nufin Summy zatayi aure ta barta kenan? Wato duk maganar data fada mata jiya akan ta juya mata ra'ayi batun aurenta da Muhseen baiyi tasiri ba kenan? Wani irin haushi ne da zafin kishi taji ya turnuke ta, can kasan ranta ta soma kissa abubuwa da dama da kuma hanyar da zata bi ta bullo wa lamarin don bazai yu ace Summy ta samu farin ciki ita kuma tana cikin bakin ciki, inaaa.... bazai yu ba.

Murmushin karfin hali  kawai ta kirkiro bisa fuskarta tace " toh shikenan, ina tayaki murna kawata, Allah ya tabbatar da alkhair kema sai kiyi kokari ki dage da addu'a".

"Insha Allah zanyi iya kokarina nima. Nagode Huda".

Bangaren Muhseen kuwa, zaune yake cikin office dinsa yana aiki, wayarsa ta soma ringing. Shamsu ne ke kiransa don haka cikin sauri yayi picking call din ya kara a kunnensa.

Bayan sun gaisa, Muhseen yace "badai akan maganar tafiyan bane?"

Shamsu yace "a'a oga, ai nama kiraka ne nace kasha zamanka don comapany din sunce no need, ba sai kazo japan din ba".

"Haba dai, ko sun fasa aikin damu ne?" Ya tambayeshi cike da damuwa.

🔥Huda🔥💄Donde viven las historias. Descúbrelo ahora