Chapter-thirty three

184 17 0
                                    

Huda tace mishi a'a ba abunda zata kara waenan ma sun isheta.

Tare suka fito daga cikin shagon, suna cikin tafiya, Muhseen ya dubeta yace "Allah yasa Summy taso jewelries din".

Huda ta danyi dariya tace "ai nida Summy kusan taste dinmu daya, so zata so Su sosai baccin haka ma wace mace ce zata ga jewelries dinan tace basu mata ba? Ai summy is very lucky".

Muhseen murmushi kawai yayi sa'anan ya mata nuni da inda yayi parking motarsa yace "bisimillah muje na saukeki a gida mana".

Babu musu tabi bayanshi suka shiga cikin motar.

Bafi 30 minutes ba sai gasu nan sunyi parking a kofar gida.

Anty Rakata da maman zahra ne ke kusa da kofar gidan nasu suna hira sukaga hadadiyar mota tazo tayi parking.

Maman zahra ta tabo Anty Rakata tace "Rakata ba wancan motan bace ta kawo Huda gida ranan ba?"

Anty Rakata ta tabe baki tace "motarce  mana".

"Wai an samu an gano wanda yazo ya sauketa gida a ranar?"

Anty Rakata tace "ai wanda ya kawota a ranar shine likitan dayake zuwa yana duba Ummul Ammabuwa".

"Dan Allah, ko shine wancan". Maman zahra ta fada tana nuna Muhseen wanda ya fito ya tsaya da Huda suna sallama.

Anty Rakata tace "bashi bane. Wancen ai yafi wanan tsawo, Wanan wani ne daban don ban taba ganinshi ba"

Maman zahra ta girgiza kai tace " Ikon Allah, Huda kenan mai samari kala kala"

Anty Rakata yace "kya gane mun fa. Yarinya da shegen son mazan tsiya da abun duniya".

Maman zahra tace "toh ki fadawa yayarta mana ko zatayi mata fada".

Anty Rakata ta dafe kirji tana zaro ido tace "ni rakata, rufa mun asiri. Ai ammabuwa goyon bayan kanwan nata takeyi yanzu. Don haka bakina alekum, ni nawa ido"

Suna cikin maganarsu Huda tazo ta wuce su ko kallo basu isheta ba tana tafiya tana rangwada da wuce cikin gida.

Anty Rakata ta dubi maman zahra tace " ai kin gani ko? Kwata kwata batada hankali. Hankali yayi nan ita kuma tayi can".

Maman zahra tace "toh Allah ya kyauta".

Nan suka cigaba da hiransu da gulmace gulamacen da suka saba.

Huda tana shiga cikin gida tayi sauri ta boye ledan jewelries din cikin handbag dinta don karsu Ammi su gani.

Karasawa cikin gidan tayi nan ta tadda Ammi zaune a tsakar gida tana shan iska don har ta dan soma samun lafiya jikinta ya soma kwari.

wuri ta nema kusa da Ammi tana gaidata tace "Ammi sannu da gida"

Ammi ta ansa da "yauwa Huda. Sannu da zuwa, Ya makarantar yau?"

Huda tace "lafiya lau Ammi".

Ammi tace "Summaya fa? Ya take?"

"Summy tana nan lafiya Ammi. Tace ma na gaishe ki"

Murmushi ammi ta sake sa'anan tace "ina ansawa. Ai Huda ina sonki da Summayan nan sosai. Yarinyar tanada hankali. Duk cikin kawayenki ban taba ganin mai hankali da nutsuwarta ba. Kuma Huda ina rokonki da Allah ki cire wanan kishin nata da kikeyi daga cikin zuciyarki".

Huda ta tabe baki tace "ni Ammi sai kiyita cewa ina kishi, nifa babu wani kishi da nakeyi da ita, don na daya na fita kyau kuma na fita isashen lafiya. Toh kishin meye zan tsaya ina yi da ita. Kudi ne kawai zata nuna mun, amma nima nan bada jimawa na kusan cima burina. Don ban fada miki ba Ammi, Ashraf ya nuna mun cewa yana sona kuma da aure".
Huda ta karasa maganr tana murmushi.

🔥Huda🔥💄Onde histórias criam vida. Descubra agora