Chapter fifty-eight

181 17 0
                                    

Muhseen ne ya dubeshi yace "Daddy ko kana busy ne yanzu na dawo anjima mu cigaba da maganar".

Alhaji yace "nnoo.no kayi zamanka, kasan aikin ne baka rabuwa da damuwa da matsalolin mutane".

"Wani irin aiki kenan?"

Mikewa Alhaji yayi cikin sauri yaje wurin cabinet dinsa ya ciro wasu files ya soma budewa yana fadin "akwai wani project ne dana fara kuma naga alama zan kashe kudi fiye ga yanda nake tunani a wanan project din".

"This is perfect daddy, kaga idan na samu na siyar da gidajen nan ba sai mu hada kudin muyi investing a wanan project din ba?".

Alhaji wanda Gabadaya hankalinsa a tashe yake yace " a'a Muhseen, please don't even think about it. Kabar wanan maganar."

"Meyasa Daddy? Kaga na farko komai nawa yana hannunka, kuma duk dukiyan da mahaifina ya mutu ya bari duk kai ke kula dasu. Shiyasa naga wanan ma sai na hada na baka mu cigaba da investing".

Alhaji yace "Muhseen wanan kudin naka ne, kai kasan yanda zakayi tattalinsu, banso ka zo ha hadasu, kudin su salwanta".

"Haba Daddy, yanzu ka gwamace na dauki kudina nayi business a waje akan nayi dakai?"

Shiru Alhaji yayi bai bashi ansa ba don shikam ba wanan bane yake damunsa, kiran daya shigo cikin wayarsa ba karamin tadda mishi da hankali yayi ba. Allah Allah yake Muhseen ya tashi ya tafi don baya son ya gano komai.

Muhseen ya cigaba da fadin "Daddy inaso ka bani wanan damar na tayaka da wanan business din, kaga daga baya idan komai ya tafi yanda akeso sai ka biyani kudin danayi investing a ciki".

"Alhaji yace toh shikenan naji, ka bari zamuyi maganar idan na dawo gida."

Muhseen yace "toh shikenan" mikewa yayi ya yiwa kawun nasa sallama sa'anan ya fice daga office din.

Muhseen yana fita Alhaji safwan yayi sauri ya dauko wayarsa ya soma neman layin dan'nasa, bugu daya ya daga yana fadin "daddy, wanan aikin project din fa daka bani, authorities sunzo sun hana mu karasa aikin".

A fusace Alhaji yace "akan me?! Sun san makudan kudin dana kashe kuwa akan wanan project dinne da zasu ce zasu hanaku aiki?"

"Wlh daddy ban san musu ba amma PA din Alhaji Nasir ta bani wasu takardu nayi comparing da namu, so idan mun gama da aikin zan kawo maka takardun lagos ka gani".

Alhaji yace "noooo, jubril ba sai kazo ba. Ina bukatan ka a wajen, so nake kasa mun ido sosai akan wanan project din".

"Toh Daddy zaman me zan cigaba dayi yanzu tunda an tsayar da aikin".

Alhaji yace "karka damu, zanyi musu magana. Zasu barku ku cigaba da aikin".

"Amma daddy....."

"No Jubril, kayi abunda nace kawai".

Cikin sanyin jiki jubril yace "toh Daddy".

Alhaji ya da'an sassauta murya yace " kaga da'ana, inaso ka da'an dadda hakuri tukuna, ina kace kana son aikin project dinan?".

"Inaso daddy, amma kaga inada aikin project dina a school da banzo na karasa ba".

"Toh naji amma inaso ka da'an kara hakuri kadan, nima cikin kwanan nan nakeso zan shigo kano."

Jubril yace "toh shikenan daddy, Allah ya kaimu".

*********************

Summy da Huda ne suke tafiya tare cikin school don basu jima da gama lectures dinsu na safe ba.

Summy ta kalli Huda tace "Huda kiyi hakuri akan maganar da mukayi jiya, naga kamar ranki baiso ba. Dana shina ban fada miki cewa Muhseen ne ya biya kudin wanan wurin ba".

🔥Huda🔥💄Donde viven las historias. Descúbrelo ahora