Chapter thirty- four

220 24 0
                                    

Huda taci wani uban kwaliya, sanye take cikin riga da wando jeans da suka dame ta, suka fito da ainun shape din jikinta. Doguwar sumar kanta mai laushin gaske ta zubesu har gadon bayanta, sai faman yauki takeyi a gaban Ashraf.

Shi kuwa sai binta da kallo yakeyi yana jin sonta yana dadda karuwa cikin zuciyarsa.

Clear Essence California Spa & Wellness Resort Muhseen ya kaisu yayi parking motarsa.

Tare suka fito, Muhseen yana tafiya shida Summy suna dan taba hira cike da so da kaunar junasu, haka zalika Huda da Ashraf suna biye dasu a baya.

Huda karewa wurin kallo takeyi don a rayuwarta bata taba zuwa wuri hadade na shakatawa irin wanan ba.

Wurin yayi kyau sosai harta ma'aikatan wurin turawa ne musamman aka zubesu suna lura da wurin.

Muhseen ya juyo yana duban Ashraf yace "lets take a ride first, akwai inda ake hawa boats a lagoon din. Bari nayi musu magana. Ko ya ka gani?"

Ashraf yayi dariya yace "sure why not, nima it's been long dana hau".

Muhseen yace musu yana zuwa, nan yaje yayiwa masu wurin magana.

Bafi minti biyar ba sai gashi nan ya dawo tare da daya daga cikin ma'aikatan wurin.

Nan akayi directing dinsu zuwa ciki, suna fitowa ta dayan bangaren sai ga lagoon da mutane da dama suna shakatawa. Lagoon din baban ruwa wanda yake gangarawa ya hade da ruwan teku.

Wurin tamkar beach, don ga kasan beach a yashe kota ina yara na wasa akai.

Ga kuma jirage an zubesu musamman na yawo akan ruwa.

Tare suka karasa inda aka hawa, Huda ce akan gaba don Allah Allah take taje ta hau tayi cruising.

Muhseen ya dubi Summy yace "baby zaki iya hawa kuwa?"

Summy dariya kawai tayi tace "why not, zan iya mana".

Toh dayake akwai gadan da zaka dan hau da zai sada ka da inda ake shiga boats din, yasa su suka hau suna tafiya a hankali, gashi kuma kasan gadan duk ruwa ne.

Suna isa suka bawa mai tuka jiragen tickets ya duba sa'anan ya basu wuri suka soma hawa.

Ashraf ne ya fara hawa, ya taimakawa Huda itama ta shigo ciki.

Sa'anan ya juyo ga Summy yana kokarin taimaka mata ta hau jirgin.

Ai kuwa Summy tana sa kafa zata hau, kafan nata ya goce.

Kafun kace mai, sai gata nan cikin ruwan tsundum.

Wani irin razananen kara ta sake, babu shiri Muhseen shima ya shige cikin ruwan hankalinsa a tashe ya fara swimming zuwa inda take yana kokarin ceto ta.

Huda tana tsaye tana kallon abunda yake faruwa, dariya ne ya kusan kubuce mata ganin yanda Summy taketa faman ihu. Ita ko ajikinta, sai Allah shi kara da take fadi a zuciyarta don ita daman tun farko bata so sun fita tare dasu Summyn ba.

Shima Ashraf yana tsaye gabadaya hankalinsa a tashe yake. Da kyar dai Muhseen ya samu ya kamota, Ashraf yasa hannu suka fito da ita daga cikin ruwan.

Gabadaya hankalin kowa a tashe yake harta ma'aikatan wurin sun karaso inda suke suna kokarin suga abunda yake faruwa.

Summy kuwa sai faman kuka takeyi, gabadaya a tsorace take, gashi kuma ta bugu sosai, don akan kafan dayake mata ciwo ne ta fadi.

Kwantar da ita Muhseen yayi a gefe, duk yabi ya rufe sai faman yi mata sannu yakeyi.

Ashraf ya tsuguna a gabanta, kafan dayake mata ciwo ya kama, yana kokarin dubawa cike da kwarewa a matsayinsa na liktitan qashi.

Wani wurin ya kama, Summy ta sake wani irin razananen ihu, salati ta soma yi tana kamo hannunsa saboda wani irin azaba da takeji yana cinta a wanan kafar.

🔥Huda🔥💄Where stories live. Discover now