Chapter fifty-four

126 16 0
                                    

Ashraf zaune yake cikin office dinsa yana waya da mahaifiyarsa, inda take tambayarsa yaushe zaizo gida.

Ashraf yana murmushi yace "karki damu Umma, insha Allah nan bada jimawa ba zakiga da'anki."

"Toh muna nan muna sa rai, Allah ya nuna mana da rai da lafiya".

Ashraf ya ansa da "Ameen".

"Ya aikin naka toh?"

"Wlh umma komai na tafiya daidai Alhamdulillah, kinga yanzu ma an kara mun girma ni nake assisting a duk surgeries din da akeyi."

Cike da jin dadi umma tace "kai amma naji dadin haka, ubangiji Allah ya kara daukaka kuma Allah ya maka albarka".

Ashraf yace "ameen umma nagode, ki cigaba da sani cikin addu'a insha Allah komai zai tafi daidai kamar yanda akeso. Jiya ma ake sanar damu batun wani conference da zamuje muyi a Aminu kano teaching hospital, idan tafiyan ya yu' insha Allah zan karaso gida nazo na ganku".

Umma tace "kace zaku hadu da safah kenan, itama tana kano ta samu admission a Buk tana karatu".

"Dan Allah umma, yanzu Safah tana kano?" Ya tambayeta cike da mamaki, don Safah cousin dinshi ce kuma rabonshi da ita tun kafun ya tafi Japan, kusan tare suka girma don da mahaifiyarta da umma uwarsu daya ubansu daya.

Umma tayi dariya tace "kwarai kuwa, yanzu haka ma ta kusan kammala karatun nata, bari fadimatou ta dawo daga makaranta sai nasa ta turo maka da numberta".

Ashraf yace "toh shikenan Umma, nagode. Sai zuwa anjima kenan idan na kira, ki gaishe mun da Abba da Fadimatou".

Umma tace "insha Allah zasu ji" Addu'oi da albarka sosai ta dadda saka mishi yana mata godiya daga bisani ya katse kiran.

Mikewa yayi ya fice daga office din ya karasa kasa zuwa office din Dr Abdul.

sallama yayi ya shiga office din, nan ya sameshi zaune yana duba wasu takardu.

"Abdul ka samu ka kammala report din angiography da akayi wa mahaifiyarsu Huda kuwa?"

Cike da damuwa Dr Abdul ya mike yana fadin "wlh na samu na kammala report din amma fa abunda ake tsoro shine ya tabbata. Test din ya nuna akwai blood vessel a gaban kwakwalwarta, kalla wall din kaga, it's extremely thin". Ya fada yana mikawa Ashraf takardan scan din.

Ashraf ya karba takardan ya soma dubawa. Tabbas kuwa gashi scan din ya nuna akwai jinin daya taru a kwakwalwar nata.

Zufa ne ya soma karyo masa ta ko ina, Dr Abdul ya dafashi yana fadin "karka damu Ash, insha Allah zamuyi iya daidai kokarin mu tabbatar ta samu duk wani kulawa da take bukata. Insha Allah bazamu rasa ta ba".

Cike da sanyin jiki Ashraf yace "toh Abdul, Allah yasa. Bari naje na dubata na bata sauran magungunan nata tasha".

Haka yaje wurin nurses ya karba magungunan yaje dakin da Ammi take kwance ita kadai idonta biyu.

kujera yaja daga gefe ya zauna, bayan sun gaisa ya soma janta da hira yana kokarin kwantar mata da hankali. Daga bisani ya soma bata magungunan da allurai.

Bangaren Ammabuwa kuwa tana zaune a reception sai ga dr Abdul nan ya karaso.
Wuri ya nema a kusa da ita ya zauna sa'anan ya kira sunanta a hankali yace "Ammabuwa....."

Cike da damuwa ta dago tana dubansa tace "na'am Abdul, meya faru? Ina Ammi na?"

"Ammabuwa ina so ke da Huda ku dage akan kulawa da mahaifiyarku...."

Bata bari ya karasa maganar ba, muryarta na rawa tace "abdul please ka fada mun, wani abun ne ya sameta?"

"Zan fada miki gaskiya Ammabuwa, bazan boye miki komai ba. Maganar gaskiya scan din da mukayi mata ya nuna cewa tanada tarin jini a cikin wani jijiya dake cikin kwakwalwarta, ma'ana idan aka bari jininta ya sake hawa, wanan jijiyan zata iya fashewa".

🔥Huda🔥💄Where stories live. Discover now