Chapter Eighty - Nine

154 16 0
                                    

Huda tana isa Lagos, bata wuce gida ba kai tsaye gidansu Summy ta fara zuwa
Tana shiga daya daga cikin masu aikin gidan ta soma sanar da ita cewa Summy bata nan, taje asibiti tun safe. Har ta juya zata koma sai ga Nani ta fito daga kitchen "keh uwar marasa tarbiya kin wani shigowa mutane gida kai tsaye ko gaisuwa babu".

"Wazan gaisar? Wurin ki nazo?" Huda ta tambayeta hade da watsa mata wani irin kallo cike da raini.

"Meya kawoko gidan nan bayan ina murna kwana biyu kin bace, kin kuma dawowa da shegen bakar zuciyarki da bakar aniyanki ki shafawa ya'ta to ta baki isa ba, ki kama hanyarki ki tafi tun wuri kisan inda dare yayi miki don jibi insha Allah za'a daura mata aure da wanda takeso kuma tare zamu tafi mu bar kasan da ita, sai dai ki mutu".

Wani irin dariya Huda ta sake ha'de da shewa "ki bar cika baki tsohuwa, idan abubuwa suka tafi yanda nakeso daga ke har yar'taki zan bar muku tabon da har ku mutu bazaku manta dani ba".

A gigice nani ta soma binta da kallo jin abunda ta fadi "tabo? toh ta Allah ba taki ba bakar munafuka Ai daman tun farko nasan ke ba kawar arziki bace, kina ganin kanki kinfi karfin kowa, shiyasa tun ranar dana fara daura idanuna akanki naji sam baki kwanta mun ba, ke ba alheri bace ga mimi na".

"Niba alheri bace ga miminki, toh ke alheri ce gareta? Ki dinga hanata mun abubuwa kina aibatani a gabanta saboda kina kishi da irin kulawan da take bani".

"Ni ban hanata yin abubuwan alkairi ba, kece dai na gano bakida mutunci kuma bakisan meye mutunci ba, baki cancanci irin kulawan da kike samu daga mimina ba. Kina bakin ciki da ita kina son ki mallaki duk abunda take dashi toh karyanki tasha karya a hakan zaki kare bakar munafuka mai fuska biyu, kina ji kina gani ya'ta zatayi aure ta barki sai dai ki tsiyaci yawon gantalinki a gari babu miji!"

"Haka kikace ko? Toh shikenan mu zuba mu gani, zakiga wanda zai rasa miji kuwa". Tana gama fa'din haka ta juya ta bar gidan a fusace nani sai faman binta da zagi take.

Ko data isa gida tun daga kofar gida Anty Rakata ta hangota ta karaso cikin sauri tana fa'din "yauwa daman ina zaune ina jiran shigowarki, ki gaya mun da kudin uban wa kikayi tafiya zuwa Abuja?"

A fusace Huda ta bata ansa da "Kinga Rakata ki kyaleni yanzu na dawo, ina ruwanki da tafiyata zuwa abuja?"

"Da ruwana kuma dole na bincike ki! Kowa suspect ne akan kudina musaman ke don haka ki gaya mun tun wuri in ba haka unguwan nan sai ya mana kadan".

"Unguwan nan zai mana kadan? wlh anty Rakata ki kiyayeni ki fita daga harkata don duk yanda kikeji da tashanci nafiki  akan me zaki zo ki tsareni akan hanya daga dawowata har nawa kike dashi da za'a shiga a miki sata..wani kudi ne dake?. Ta fa'da hade da hankadata gefe tayi shigewarta cikin gida tana maganganu, Anty Rakata ta bita da ruwan zagi Huda na shiga cikin gida ta soma da'ga murya tana zage zage har ta shiga uwar daka tana ganin Ammi tace "Ammi ki jawa Anty Rakata kunne, ki gaya mata ta tsaya iya gulmace gulmacenta akaina amma karta ce zata zarce da daura mun sata don wlh wlh zan karta mata rashin mutunci da bata ta'ba tsamani ba cikin unguwan nan! Zan gyara mata zama! Akan me zata zo tana tsareni akan kudinta daga dawowana!"

Mikewa Ammi tayi cikin zafin rai ta karaso ta tsaya gabanta tana hucci "daman shigowanki nake jira, kizo ki gaya mun gidan uban wa kika samu kudin tafiyan Abuja da kikayi!"

Shiru Huda tayi tana binta da kallon mamaki "Ammi har yanzu baki kawar da zargin da kike mun ba kina tunanin nice na daukewa matan nan kudi? In har kin yarda nice na dauke mata kudi meyasa tun a ranar baki caje ni ba?" zuciyarta na tafarfsa ta juyo ta dauko jakar data shigo dashi hade da purse dinta ta soma zazage abubuwan ciki "toh gasunan na bude miki kina iya bincikawa son ranki ki tabbatar wa kanki!" Ta karasa maganar tana da'ga murya tamkar da sa'arta take magana.

🔥Huda🔥💄Donde viven las historias. Descúbrelo ahora