Chapter Eighty

199 16 2
                                    

Bangaren Dr Dangora kuwa, a fusace ya shigo office dinsa yana hucci Dr zakari na biye dashi "i can't believe this, yanzu ni Laylah zata duba tsabar idona a meeting dinan ta sallake ta bawa wanan karamin yaron director na project. Project din dana kwalafa rai zan samu?! Nine fa nayi introducing dinta ga wanan research din"

Ajiyar zuciya dr Zakari ya sake sa'anan yace "ai na fada maka tun farko, kamar son yaron nan take. Don interest din da take nuna akanshi yayi yawa"

"Tun a kano, ta tambayeni batunsa na fada mata ya daina aiki dani na sallameshi a bisa kuskuren dayayi. Nan ta tsaya tace sam bata yarda dani ba zatayi magana da sauran yan' committee kuma ta yanke halakar Doctor- patient dake tsakanina da ita, bata son na cigaba da kula da ita a matsayina na likitanta."

"Hmm this is serious, nidai shawarata gareka you have to be very careful don da Alamu she's very interested in this boy. Komai zai iya faruwa, nasan bazaka so mace kamar Hajiya Laylah ta juya maka baya ba".

Shiru Dr Dangora yayi tunani kala kala na masa yawo aka, sai faman hucci yakeyi gabadaya duk hanklinsa a tashe.

Bangaren Summy kuwa, tunda ta iso gida tasa daddynta a gaba akan lallai tana so ta koma therapy lessons dinta zata kira Ashraf ta mishi magana. Alhaji yayi mamaki, amma sai yaji dadi don yasan tunda suka je asibiti last bata kuma nuna interest akan theraphy din ba.

"Amma princesses meyasa kikeso ki cigabada da therapy? Why the sudden interest?"

Summy tana murmushi tace "wlh daddy Huda ce yau a school ta bani shawara, nima inaso naga tafiyata ta da'an gyaru kafun lokacin biki".

Daddy cike da jin dadi yace "toh shikenan princess, duk yanda kikace hakan ma yayi, kina iya yiwa Ashraf din magana sai yayi miki booking sessions ku fara".

Cike da farin ciki Summy tace "toh Daddy, thank you so much".

"Anything for my princess. Amma ya Muhseen? Kwana biyu bana ganinsa. Da fatan dai komai lafiya?"

"Wlh komai lafiya Daddy, kawai dai ayika ne suka mishi yawa kwanan nan, bai samun shigowa".

Daddy yace toh shikenan, Nan suka cigaba da hiransu cike da anashuwa da jin dadi.

*****************

Ashraf yana barin asibiti, straight kamfaninsu Muhseen ya nufa yaje ya sameshi a office, sosai Muhseen yaji dadin ganinsa ya soma mishi barka da zuwa.

Ashraf cike da zumudi ya soma fadin "Muhseen you won't believe this! Daman ance wani hanin daga Allah baiwa ne, kasan yanzu an bani chief director na project research dinmu?"

"Dan Allah Ash! Kai amma na maka murna. Tell me how did it go?" Muhseen ya shiga tambayarsa cike da mamaki.

"Wlh Muhseen wata mata ce da muka hadu da a can wajen conference a kano... itace..."

"Wait hold on... you're going too fast, naji kace wata mata?" Muhseen ya tambayeshi yana murmushi.

Ashraf ya da'go abunda yake nufi don haka Nan take ya dakatar dashi" noo.. ba abunda kake tunani bane Muhseen, kama kawar da wanan tunanin a ranka."

Dariya Muhseen ya shiga yi sa'anan yace "toh shikenan naji, now tell yanda kuka kare ina jinka".

Ashraf zaiyi magana idanunsa suka sauka kan wasu jakankuna dauke da kayaki a cikin su. "Muhseen waencan jakankunan fa? na meye?"

"Oh na Summy ne... ita na yiwa siyaya za'a kara cikin kayan lefe".

"Masha Allah, kace abubuwa sunyi nisa kenan na biki anata faman shirye shirye"

🔥Huda🔥💄Donde viven las historias. Descúbrelo ahora