Chapter Sixty - four

139 13 0
                                    

Bangaren Muhseen kuwa, tare suka shigo cikin office shida kawun sa, Alhaji Safwan na tambayarsa "Toh ya kaga tsarin office din? Yayi maka ko a canza?"

Muhseen yace " tsarin yayi Daddy. Nagode".

Shiru yayi yana nazari bai sake cewa komai ba.

Alhaji ya dago yana dubansa yace "ya naga kayi shiru, ko akwai wani abu ne?"

Muhseen ya da'an nesa sa'anan yace "ba komai Daddy, kawai dai ina tinanin ko Huda zata iya aiki tare dani a wanan office?

Cike da mamaki Alhaji yace "Huda kuma? Aikin me zatayi tare dakai".

Muhseen yace "eh toh, cewa tayi tana so ta biyani kudin taimakon dana musu a asibiti na rashin lafiyar mahaifiyarta".

"Kai kuma ka amince mata?" Alhaji ya tambayeshi.

Shiru Muhseen yayi bai ce komai ba.

"Atoh ni banga dalilin dazai sa tace zata soma aiki tare dakai ba, it doesn't make sense".

"Wlh Daddy ni kaina nace mata ba sai ta damu ba, amma ta nace wai sai tayi".

"Kai kawai kace mata babu wuri, company dinan ya cika, in har ta nace tana so tayi aiki anan toh sai dai ta jira in ka tafi Japan."

Gyada kansa kawai Muhseen yayi bai sake cewa komai ba, tunani kala kala na masa yawo a ka.

Bangarensu Huda kuwa, Summy ce ta fito da wayarta ta soma nuna mata wasu kayan amare masu kyau da takeso ta zaba tasa na fitan biki.

Wani simple gown maroon colour mai ratsin cream coloured flowers Summy ta nuna mata.

Huda ta tabe baki can kasan ranta tace "tab Allah ya sawwake nasa wanan abun ranar biki na".

Amma a filli murmushi kawai tayi tace mata yayi kyau.

Ba'a jima ba dare ya soma yi, Huda tace zata wuce gida. Summy tayi mata godiya sosai hade da rokonta data zauna tayi nazari akan Ashraf su samu su sasanta.

Mahmud Summy ta kira tace yazo ya kai Huda gida. Har kofar gida Mahmud ya kaita sa'anan yayi parking. Cike da gadara ta fito ko godiya bata masa ba ballanta tayi masa sai da safe ta fito zata shige cikin gida, shima ya fito.

Don tunda Summy tace mishi yazo ya kai Huda gida yaketa murna don at least zai samu yaga Ammabuwa, don a yanzu ya rigada yayi nisa a sonta, a koda yaushe bashida wani tunani sai nata.

Ganin Mahmud ya fito ya tsaya ne yasa Huda ta juyo tana yatsina fuska tace "ya Mallam lafiya?"

Mahmud ya soma sosa kai yana kame kame don yasan halinta sarai, batada mutunci.

"Eh..ee... daman inaso na tambayeki ya jikin mahaifiyarku?"

"Jikinta da sauki yanzu alhamdulillah" ta bashi ansa kai tsaye tana kara yatsine fuska.

Ta fahimci sarai abunda yakeso ya tambayeta, jira kawai take yayi magana ta sauke mishi kwandan rashin mutunci.

Ai kuwa yace "in kin shiga dan Allah ki mika gaisuwata gareta, da kuma yayarki Ammabuwa kice ina gaisheta".

A tsawace tace "Mene?! Ban jika da kyau ba".

"Cewa nayi ki tayani mika...."

"Amma sai yau na tabbatar da bakada hankali baka san me kakeyi ba, ka dubeni da kyau kace na mika maka gaisuwa wurin yayata. Yayata tayi kallan sarar ka ne, ko tayi maka kama da class dinka ne? Toh wallahi tun wuri ka canza tunaninka don yayata tafi karfinka. Dubeka tallaka dakai, aikin driver fa kakeyi? Dame zaka ci da ita? Daga yau sai yau nayi maka last warning kenan, karka kuskura kace zaka sake tunkarata da wanan shirmen". Tsaki ta buga masa sa'anan ta shige cikin gida a fusace sai faman zazaga ruwan bala'i takeyi.

🔥Huda🔥💄Donde viven las historias. Descúbrelo ahora