Chapter Sixty-seven

142 15 0
                                    

Ashraf yana barin wajen ransa a matukar bace ya ciro wayarsa ya soma neman layin Summy, bugu daya ta daga hade da sallama, bayan sun gaisa Ashraf ya soma tambayarta inda take tace mishi tana gida. Yace toh dan Allah yana son ganinta a gurguje gashi nan zuwa. Cike da damuwa Summy ta soma tambayarsa lafiya? Yace lafiya, sai dai yazo. Tace toh.

Yana isa gidansu, ya kirata a waya yace gashi a kofar gida, bafi minti biyar ba sai gata ta fito ta sameshi hankalinta a dage don Ashraf bai taba kiranta yace yana son ganinta haka ba, sai ta soma tunanin kilan wani abu ne ya hadashi da Huda.

Bayan sun gaisa, Summy ta dubeshi tace "lafiya kuwa Ashraf kakeson ganina haka? Meya faru?"

"Nazo ne inso nayi magana dake akan kawarki Huda".

Gaban Summy ne ya fadi tana dubanshi tace "Ashraf indai kazo ka fada munanan abubuwa akan kawata kuma ka cima mata mutunci ne toh gaskiya bana son ji"

"No...no Summy wlh ba haka bane, dan Allah ki saurareni kiji, nazo ne a matsayin abokin saurayinki kuma mai son yaga farin cikin ku, Summy nasan koda kunyi aure da abokina zaki sashi tsantsan farin ciki don samun mace kamar ki, mai hankali da nutsuwa abu mai kamar wuya ne, sai an bincika. Yanzu abu daya nakeso dake Summy, inaso ki kara kusanci da Muhseen".

Cike da rashin fahimta Summy tace "ai nidashi muna tare kusan koda yaushe"

"Eh nasan da hakan amma please i want you to always be with him, karki taba bari ya nisanta dake". Da siyasa yake mata maganar amma bata dago ba don haka sai ya bar maganar haka yace "toh ni zan wuce, daman nazo muyi sallama ne yau zan wuce kano".

"Lafiya kuwa?"

"Lfy wlh, akwai conference meeting da zamuje muyi ne, amma very soon zan dawo insha Allah".

"Toh Ashraf, nagode kwarai da gaskiya, Allah ya tsare".

"Ameen".

Nan sukayi sallama ya wuce abunsa.

Bangaren Huda kuwa, Ashraf na barin wajen ta buga wani uban tsaki hade da gyara zaman kayan jikinta, sa'anan ta karasa cikin building din.

Muhseen ta soma kira yazo ya tadda ita, wani irin kallo ya bita dashi dayaga kayan dake sanye a jikinta amma bai ce komai ba.

Huda ta soma mishi godiya akan amincewarsa, Muhseen yayi murmushi yace mata babu komai.

Tare suka karasa office din Alhaji Safwan suka gaisa, Alhaji Safwan yana ganin Huda ya danyi jimmm dayaga shigar dake jikinta amma bai ce komai ba, Hajiya Maryam PA dinshi yayiwa magana data kai Huda sabon office dinta. Godiya sosai Huda ta mishi sa'anan tabi bayan hajiya maryam suka tafi.

Suna tafiya Alhaji safwan ya juyo yana duban Muhseen yace "kai, a hakan zakuyi aikin da ita? Ji irin shigan dake jikinta".

Muhseen ya sake ajiyar zuciya sa'anan yace "toh daddy ni gaskiya babu abunda zan iya ce mata tunda Summy ce ta dage akan sai lallai na bata wanan aikin".

"Baka tunanin akwai wani abu a kasa data tillasta maka sai kawarta tayi aiki tare da kai? Ko dai sunyi planning ne tana so tasa maka ido, kasan wasu matan da tsananin kishin tsiya".

"A'a Daddy, Summy ba haka take ba. taimakon dana musu a asibiti ne yasa Huda ta dage tana so nima ta taimaka mun da wasu ayuka anan. Huda tanada kirki sosai Daddy, batada matsala".

Alhaji yace "alright toh shikenan. Allah yasa hakan shine".

"Ameen" Muhseen ya fada sa'anan yace "ni zan koma office daddy, daman na kawota ku gaisa ne".

"Toh shikenan. Idan ina bukatar wani abun zan sanar dakai".

Da wanan Muhseen ya fice ya koma office din nasa.

🔥Huda🔥💄Donde viven las historias. Descúbrelo ahora