Chapter fifty-seven

177 22 2
                                    

Sai da Huda taci kukanta ta gaji tukuna ta ta soma sauke ajiyar zuciya. Jiki babu kwari ta mike tana share hawayenta ta shige ciki.

Tana shiga daki ta tsaya a gaban mudubi tana karewa kanta kallo. Manyan idanunta sunyi ja sunfifito tsabar kukan data sha.

Hannu tasa ta goge hawaye da'ya daya samu nasaran zubo mata tace "nayi kukan karshe kenan akanka Ashraf, insha Allah bazan kara zubda hawayena akanka ba.

Da wanan ta sake daure, ta kara karfafa zuciyarta. Wuri ta samu a gefen gado ta zauna tana ajiyar zuciya.

Bangaren gidansu Muhseen kuwa, Mommy ne da Alhaji safwan zaune kan dining suna cin abinci.

Mommy ta dubeshi tace " Alhaji naji dadi daka sauko ka saurari yaron nan har ka amince za'ayi bikin nan".

Ajiyar zuciya Alhaji ya sake sa'anan yace "naji na amince amma bawai hakan yana nufin ina son Muhseen da yarinyar nan bane kawai babu yanda na iya ne".

Dariya mommy ta dan sake sa'anan tace "Alhaji kenan, ai babu yanda ka iya don nasan kana matukar son Muhseen kuma kasan bashida wani uban daya wuce kai".

Murmushi Alhaji ya sake, ya kamo hannunta cikin nashi ya kai bakinsa ya sumbaci wajen sa'anan yace "Matata kenan, Nasan cikin yan kwanakin nan muna samun sabani amma ina so ki sani cewa banida kamar ki a rayuwata. Muhseen jini na ne, kuma bazan so wani abu ya tauye masa farin cikinsa, farin cikinsa shine nawa don haka na amince masa yaje ya auri duk yarinyar da yakeso."

Mommy cike da jindadi tace "hakane Alhaji, naji dadin haka kuma ina alfahari dakai mijina, Allah ya kara mana dankon kaunar juna, kuma ya yayye duk wata fitina da zata sanyo kai. Allah ya tabbatar da alkhair ya nuna mana bikin da'anmu lafiya".

Alhaji yace "Ameen Ameen".

Haka suka cigaba da cin abincin dake gabansu suna hira cike da jindadi da anashuwa.

Bangaren su Ammi kuwa, Ammabuwa ce ta dawo daga aiki tayi sallama ta shigo ciki tana tambayar Ammi ya jiki.

Ammi ta dan numfasa sa'anan tace "da sauki alhamdulillah"

Shiru tayi daga bisani ta cigaba da fadin "Ammabuwa ki fada mun gaskiya, meke damuna".

Hankalin Ammabuwa ne ya soma dagawa amma tayi kokari ta danne damuwarta tace "babu abunda yake damunki ammi, meya faru?"

"Dazun dr Abdul yazo yana mun wasu tambayoyi kafun ayi mun gwaji".

"Wani irin tambayoyi yayi miki Ammi?"

"Tambayoyi yayi mun akan cututuka dake yawo a cikin family dinmu, ko akwai wani daya taba irinsa".

Ammabuwa ta kamo hannun Ammi cikin nata ta soma fadin "Ai wanan ba komai bane Ammi, ki kwantar da hankalinki, kinga fa yanzu kin rigada kin samu lafiya".

Numfashi Ammi taja sa'anan ta sauke ta cigaba da fadin "Addu'a nakeyi Allah yasa inada tsawon kwanaki da zan kara na kasance tare dake da yar'uwarki, na taimaka muku wajen gano yanda rayuwa take ciki musamman ga yar'uwar Huda don hanyar data dauko take tafiyar da rayuwarta ba hanya bace mai kyau."

"Insha Allah Ammi zaki kasance tare damu har tsawon wanan lokacin, dan Allah kidaina wanan maganar yanzu kamata yayi ki samu ki huta, kina bukatan hutu Ammi".

A hankali Ammi ta kira sunan Ammabuwa tace "Ammabuwa... ina so ki dau mun alkawari akan koda nan gaba bana nan, zaki rike yar'uwarki kusa dake. Koma me zai faru Karki ce zaki barta tayi rayuwa ita kadai, ki juya mata baya. Inaso ku hada kanku, duk wuya duk runtsi ku kasance kuna tare."

Hawaye ne suka ciko idon Ammabuwa tasa hannu ta goge tana fadin "insha Allah Ammi, na dau miki wanan alkawarin. Bazan taba bari aji kanmu ba".

Shiru Ammi tayi bata sake cewa komai ba, tana jin kirjinta na mata wani irin nauyi.

🔥Huda🔥💄Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon