Chapter thirty- seven

191 21 0
                                    

Da dare misallin karfe takwas, Summy ce kwance akan gado, ta farka daga bacci. Da kyar ta iya motsawa saboda tsamin da kafanta yayi.

Wayarta ce ta soma ringing a kusa da ita ta daga tana duban screen din, taga Huda ce ke kira.

Kara wayar tayi a kunne hade da sallama.

Huda ta ansa sallamar hade da tambayarta ya jiki.

Summy tace "da sauki alhamdulillah"

"Kiyi hakuri kinga ban sake zuwa na dubaki ba. wlh Ashraf ne ya kirani dazun a waya yace akwai inda zamuje dashi. Amma if you're not okay har yanzu bazamuje ba, zanzo gida kawai na zauna tare dake".

Summy ta girgiza kai tace "No haba,dan Allah kuje, naji sauki fa sosai yanzu. Pls don't cancel on my account".

"Kin tabbata babu wata matsala".

"Wlh babu wata matsala Huda. Karki damu nagode sosai da kulawarki".

Huda tace "toh shikenan. Idan na dawo zan kiraki. Allah ya kara sauki".

Summy tace "Ameen".

Nan sukayi sallama ta katse kiran.

Tana ajiye wayan, Nany tayi sallama ta shigo dakin hannuta rike da tray din abinci.

Tana ganin Summy ta farka ta karaso cikin sauri tana tambayarta ya jikin.

Cike da sanyin jiki Summy tace "da sauki, sai dai nany gabadaya duk jikina yanai mun ciwo wlh.

Nany ta dubeta cike da tausayi tace " sannu Mimina, Karki damu ciwon zai laffa miki nan bada jimawa ba bi izinillah".

Summy tace " toh Nany nagode".

"Yauwa, yanzu ki samu kici abincin nan kisha magani. Sai kisa kaya ki dan gyara jikinki. Ga Muhseen nan yana can kasa  yazo ya dubaki".

Summy cike da fargaba ta dubeta ta soma girgiza kai tace "a'a Nany. Wlh kunyar Muhseen nakeji yanzu. Bazan iya hada ido dashi ba. Duba fa yanda nake"

Nany ta bata rai tace " kunyarshi name kikeji mimina? Ai kowa yasan tsausayi ne don haka karkiji komai. Ke bakiga yanda ya damu bane?"

Summy tayi shiru tana jinta. Nany ta turo mata tray din abincin ta soma bude mata coolers din tace "oya bisimillah yiki ci na samu na shirya ki sai yazo ya dubaki".

Babu musu, summy to soma cin abincin. Jollof rice ce da salad sai soyyayar naman turkey da akayi mata sauce.

Kadan Summy taci daga bisani ta ture plate din gefe tace ta koshi. Nany ta kwashe kwanukan daga gabanta, sa'an ta ballo mata magungunanta da ruwa ta mika mata ta sha.

Wardrobe dinta taje ta ciro mata daya daga cikin dogayen rigunanta sa'anan tazo ta tayata shiryawa.

Bayan ta gama shiri, Nany ta dubi Summy  tace "Mimi gaskiya ya kamata a sanar da Alhaji abunda ya faru kafun ya dawo".

Gaban summy ne ta fadi ta soma girgiza kai tace "dan Allah nani karki fada mishi tukuna".

"Toh ai gani nai gwanda a sanar dashi tun kafun ya dawo ya ganki baki iya tafiya kema kinsan akwai matsala".

Cike da damuwa Summy tace "still Nani dan Allah karki fada mishi. Ni nasan yanda zanyi in mishi bayani yanda zai fahimta".

Nani ta sake ajiyar zuciya sa'aan tace "toh, amma kema kinsan babu wanda zai daurawa laifi sai ni. Akaina zai jibge komai".

"A'a nani, babu wani daura miki laifin da zaiyi. Shima yasan kaddara bata wuce kan kowa. Nasan yanda zan mishi bayani, karki damu nani".

Nany tace "Toh shikenan, bari naje na shigo dashi".

🔥Huda🔥💄Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang