Chapter thirty-one

206 20 0
                                    

Bayan su Ashraf sun bar gidansu Huda, Suna kan hanyarsu ta tafiya Abdul ya juyo yana duban Ashraf yace " yanzu ina zakaje, asibiti zan sauke ka ko gida?"

Ashraf ya bashi ansa da "gida na nufa wlh, kasan yanzu ina zaune tare da abokina Muhseen. Amma very soon nima insha Allah inaso na kama gida na kaina. Kaga ina zaune tare dashi a gidan nan kamar nauyi ne, So nima ina so na samu nawa".

Abdul yace " toh ai tunda ka samu wanan aikin a asibiti abubuwa zasu zo maka da sauki, tunda ana biya da kyau".

Ashraf yace "hakane. Shiyasa I'm planning towards it, insha Allah very soon i'll get a place".

"Ya kamata kam". Da wanan conclusion dinne suka karasa gida, Abdul ya sauke shi.

Bangaren su Huda kuwa, still Ammabuwa bata gamsu ba, don haka ta biyo ta cikin daki ta sata a gaba tana fadin "nidai Huda gaskiya ban amince da batun likitan nan yazo ya cigaba da duba Ammi da ba tare da mun biyashi ko sisi ba".

Huda ta dubeta tace "kai ya'ya Ammabuwa yanzu don yace bazai karba kudi a hanun mu ba shine zaki wani tada hankalinki? Abdul fa Abokin Ashraf ne, kuma suna mutunci sosai,Yanzu idan nace mishi a'a zai ji wani iri yaga kamar bana so ya taimaka mana".

Ammabuwa ta girgiza kanta tace " a'a Huda nidai ina gudun miki ne, Kar nan gaba yazo yace zai bukace wani abu gunki a madadin wanan taimakon dayayi mana."

"Wlh yaya Ammabuwa kin cika sawa kanki damuwa. Yanzu fisabilillah meye Ashraf zai zo ya bukace a wurina nan gaba? Ni nasan ba haka yake ba".

"Toh shikenan, nidai na gaya miki ki dai bi a hankali."

shuri tayi shiru tana nazari, daga bisani ta cigaba da fadin "Ni yanzu haka ma ina tunanin karban aikin sales girl da aka kirani dazun wai akwai vacancy. Gwanda in fara mu samu mu dan rage zafi a gidan nan".

wani irin kallo Huda tamata sa'anan tace "yanzu kina nufin aikin sales girl zaki koma? taya wanan aikin zai rike mu? Salary dinki a da duka duka nawa ne yaya Ammabuwa da har zaki amince ki karba wanan aikin, kema kinsan bazai taba kaimu ko ina ba. Wai a hakan ma shine kike so wanan likitan ya charje mu? Tabdijan, taya zamu samu kudin biyansa?ai gwanda ma kawai ki hakura ki barshi yayi aikinsa don ni inason uwata ta samu lafiya".

Ammabuwa shiru kawai tayi tana kallonta don tama rasa me zata ce mata.

Bata sake cewa komai ba, duba lokaci tayi taga la'asar ya kusa, ta mike ta fita ta barta a wajen.

Bayan barin Ammabuwa wajen, wayar Huda ya soma ringing, ta dauko wayar tana duba mai kiran nata, ganin sunan Summy rubuce a screen din wayar ne ya sata tayi picking.

Bayan sun gaisa Summy tace "Huda kina gida?"

Gaban Huda ne ya fadi tace " eh ina gida"

"Daman so nake nazo na duba jikin Ammi"

Huda ta dan nesa domin tasan wanan karan babu wata excuse, dole ta bari Summy tazo gida ta duba Ammi don haka tace mata "babu matsala sai kinzo".

Summy tace "toh shikenan gani nan yanzu zan shirya nazo, ki turo mun da address please".

Huda tace "toh. nan tayi mata typing ta tura mata da address din".

Within 30 mins, sai ga kiran Summy nan ya shigo wayanta tace mata tana kofar gida.

Huda ta mike ta fita taje ta tadda ita. Drivern gidansu ne ya kawota.

Cike da fara'a Summy ta fito tana fadin "kinga munyi sauri ko? Wlh yau hanya free, bamu tadda go slow ba".

Huda tace "ai kam dai. Bisimillah mu shiga ciki".

Haka Summy tabi bayanta suka karaso cikin gida. Huda tanata lura da yanayin Summy ko zata nuna wani kyama ko wani abu game da yanayin gidan nasu, amma Sai taga akasarin haka, Summyn ma ko ajikinta bata nuna mata hakan ba.

Tare suka karasa cikin daki sukayi sallama nan suka tadda Ammi kwance akan tabarma.

Huda tace "Ammi, ga kawata Summy danake ta fada muku batun ta, tazo zata ta dubaki".

Summy fuskarta dauke da fara'a ta karaso tazo ta tsuguna kusa da Ammi tana fadin "Ammi ina wuni, ya karfin jikin naki".

Ammi itama cike da jin dadin ganinta ta ansa mata da "lafiya kalau, ya'ta. Jiki da sauki alhamdulillah. Ya mutanen gida?"

Summy ta ansa mata da "lafiya lau Ammi. Allah ubangiji ya kara sauki".

Ammi ta ansa da "Ameen"

Ledan da Summy tazo dashi ne ta mikawa Ammi tace "Ammi ga wanan babu yawa, zai taimaka wurin kara miki karfin jiki".

"A'a har da dawainiya haka Summayya?"

Summy tana murmushi tace "ai babu komai Ammi, mudai burin mu bai wuce ki samu lafiya ba".

Ammi itama tana murmushi tace "toh Allah yasa, mungode sosai Summaya."

Huda ce ta karaso tace "Summy kinga gidan namu ba kaman irin naku ba ko?"

Gaban Ammi ne ya fadi ta dago cikin sauri tana duban Huda jin abunda ta fadi. Amma tayi kokari ta danne ta dawo da dubanta ga summy tace, "karki ji komai Summaya, a duk sanda kikeso zaki iya zuwa nan gidan. Ki dauka nan ma tamkar gidanku ne".

Summy tayi dariya tace "nagode sosai Ammi. Insha Allah zan dinga zuwa ina gaida ku". Wani irin dadi takeji a lokacin don yanda Ammi take mata sai ta tuna mata da mahaifiyarta. Ta soma tunani yanzu dabadin mutuwa ba da itama yanzu tana tare da mahaifiyar tata.

Kamshin Turaren wutan dake ci a gefe ne ya bugi hancin Summy, abunka da mai son kayan kamshi musamman turaren wuta irin wanan, bata san sanda tace "Amma turaren nan akwai kamshi. ban taba jin kamshi mai dadi irinsa ba".

Huda tayi sauri ta capke tace " ai wanan ba irin kalar da kike amfani da bane. Ke da kika saba ana kawo miki daga india da Sudan. Wanan fa Ammi ce ta hada".

Summy murmushi kawai tayi tace " nima dana samu Mahaifiyata tanada rai tana hada mun turaruka masu dadin kamshi haka, ai dana more".

Shiru kawai Huda tayi, taja jinin jikinta don batayi expecting abunda Summy ta fadi ba.

Wayancewa tayi tace bari taje ta kawo mata abu mai sanyi tasha.

Huda na fita daga dakin Ammi ta juyo tana duban Summy ta jata a jiki tana fadin " kiyi hakuri ya'ta, Allah ya jikan Amminki da rahma, nasan da tana nan data miki ma wanda yafi wanan, amma karki damu, nima gani nan ki dauke ni tamkar uwa kinji ko. Kuma daman na jima inaso na ganki nayi miki godiya akan duk abubuwa na alkhairi da kikeyiwa Huda, Allah ya bar zumunci kuma Allah ya barku tare".

Summy tace "Ameen Ameen Ammi, nagode sosai."

Shiru ne ya dan ziyarce su daga bisani Summy tace "Ammi ina yaya Ammabuwa?"

"Yanzun nan aka kirata a waya ta fita. Bata jima da fita ba".

Summy tace "Allah sarki, babu rabon mu hadu kenan".

Ammi tace "banjin zata jima. Kilan ta dawo kafun magrib".

Summy tace "toh shikenan Ammi, inata jin labarinta wurin Huda inaso na ganta".

Haka Summy da Ammi suka cigaba da magana kamar ba wanan bane farkon haduwansu. Summy ta sake jiki sosai sunata hira.

Bangaren Muhseen kuwa, maganganun kawunsa gabadaya ne ya kashe masa jiki.

Sai faman tunani yake akan wanan tafiyar. Ko daya isa gida ma, zama yayi a gefen gado ya daura kansa bisa hanayensa yana tunani.

Daga bisani yasa hannu ya dauko wayarsa dake gefen gado ya shiga gallery.

Hoton Summy ya lalubo ya kurawa cute face dinta ido.

Anya kuwa zai iya making decision dinan ya tafi Japan?

Yanzu me zai ce mata, ta ina ma zai soma mata bayani?

Wata zuciyar ce ta bashi ansa da " why not ka fara tafiya. Daga baya sai ka mata bayani, kasan tanada saukin kai. Idan ka mata bayani zata fahimce ka".

Wanan tunanin yana fado masa yayi sauri ya lalubo number shamsu.

Bugu daya shamsu ya daga. Bayan sun gaisa Muhseen ya soma shaida masa yace "shamsu, ayi mun booking din flight zuwa Japan din cikin satin nan. A sanar dasu cewa nayi accepting din offer din zan zo".

🔥Huda🔥💄Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang