Chapter Eighty-Two

137 14 0
                                    

Bangaren Huda kuwa, bayan ta gama abunda zatayi a school, ta wuce can kamfaninsu Muhseen. Office dinsu ta fara shiga ta tadda Hajiya Maryam zaune tana aiki ta gaisheta sa'anan ta fito tayi hanyar office din Muhseen. Tana shiga babu kowa ta fara zarya cikin office din tana dube dubenta idanunta suka fa'da kan hoton Summy dake manne cikin frame, wani irin haushi ne taji ya turniketa ta watsawa frame din harara hade da fadin "fool kawai.. jibeta".

Tana cikin haka ta soma jin takun mutum cikin sauri ta saita kanta, Muhseen ne ya shigo yana ganinta gabansa ya yanke ya fadi ya hadiye abunda yaji ya taso masa yace "Huda yaushe kika shigo?"

"Uhm ban jima da shigowa ba, daman nazo nayi submitting resignation letter nane.. amma yanzu zan wuce". Ta fada tana kokarin ciro paper daga jakarta, garin cirowa ne sauran kayan cikin jakan suka watse a kasa ciki kuwa har da hoton Muhseen.

A kidi'me Muhseen ya soma bin hoton da kallo daga bisani ya tsugana ya dauko hoton yana fa'din "Huda me kikeyi da hotona? Summy ce ta baki?"

Zaro ido tayi tana kallonsa muryanta na rawa tace "a'a Muhseen dan' Allah karka fadawa Summy kaga hotonka a hannuna. Nima I don't know how it happened kawai na tsinci kaina da...." sai kuma tayi shiru ta juya mishi baya tana kokarin matse hawayen daya taru mata cikin idanu.

Muhseen jikinshi na rawa yazo ya tasaya a gabanta yana fa'din "menene Huda? Please tell me"

Ajiyar zuciya ta sauke ta da'go fararen idanunta ta zubesu cikin nasa, shima kallon yake binta dashi from nowhere yaji ta furta "Muhseen bazan cigaba da boye maka ba ina cutar da kaina ba, nima bansan ya hakan ta faru ba amma na tsinci kaina da matsanancin sonka".

Haba... wani irin bugawa kirjin Muhseen yayi jin abunda ta fa'di tamkar a mafarki, jikinshi na rawa ya kuma matso inda take har suna shakar numfashin juna yace "me kikace Huda?"

Tana kallonshi ido cikin ido ta kuma furta "sonka nake Muhseen..." Hannunta duka biyu tasa ta tallafo fuskarsa ta cigaba da kallon cikin kwayar idanunsa tace "nayi iya kokarina naga na hana zuciyata fa'dawa cikin tarkon sonka but I couldn't help it. Ina sonka Muhseen, ina bala'in sonka". Tana gama fa'din haka ta hade bakinsu wuri da'ya ta shiga kissing dinsa. Sunfi 10 minutes makale da juna sai faman aikawa junansu zafaffan kiss suke daga bisani Huda ta kwace bakinta daga nashi ta hade goshinsu wuri daya tana wasa da sumar kansa muryanta kasa kasa tace "i'm so sorry Muhseen, I'm feeling bad already, nasan yanzu you're thinking the worst of me ko?"

A hankali Muhseen ya bude idanunsa ya zubesu cikin nata, shima yasa hannu yana tallafo fuskarta yace "noo Huda please karki ce haka. Don't feel bad, I understand how you're feeling because nima i feel the same way. Nima ina sonki, ina mutuwan sonki Huda". Yana gama fa'din haka ya hade bakinsu wuri da'ya ya cigaba da kissing dinta. In between kisses suka cigaba da fadawa junansu yanda suke ji. Daga bisani ya rungumeta tsam a jikinsa yana ajiyar zuciya, ita kam wani irin shu'umin murmushi take sakewa tana da'da matso shi jikinta.

Suna cikin haka from nowhere suka an shigo ana fa'din "yauwa Muhseen ga sauran......" maganar ne ya mutu a bakin wanda ke kokarin shigowa ya tsaya curuss yana kallon abunda ke faruwa a gabansa. Suma cikin sauri suka ware kansu daga jikin juna suka juyo suna kallon Alhaji Safwan dake tsaye yana dubansu cike da mamaki, kirjinsu na bugun tara tara.

"Daddy..." Muhseen ya fa'da muryanshi na rawa sai faman zaro ido yake.

Huda ce tayi saurin daukan jakarta ta fice daga office din kafun Alhaji Safwan yayi wata magana. Tana fita ta sake wata yar dariya tana fa'din "yess!" Bata ma damu da kamasun da Alhaji Safwan yayi ba don ita already ta rigada ta samu abunda takeso, Muhseen has fallen for her completely.

A cikin office d'in kuwa Alhaji Safwan ne ya cigaba da kallon Muhseen mamaki rubuce karara a fuskarsa, tunani yake anya abunda idanunsa suka gano masa daidai ne koko gizo suke masa. Muhseen kam kasa kallonsa yayi ya soma kame kame, Alhaji Safwan ya daka masa wani irin tsawa "kai ashe daman iskancin da kukeyi kenan kai da ita a office?! Muhseen kawar wace zaka aura ce fa? Meye hadinka da ita da har kuka kawo wanan stage din? What's going on between you and Huda?"

🔥Huda🔥💄Donde viven las historias. Descúbrelo ahora