Chapter fourty- three

166 16 1
                                    

Ashraf yana isa gida ya tadda Muhseen shima har ya dawo daga aiki.

Nan ya soma fada mishi yanda sukayi da Summy yace "kasan Summy ta samu ta shawo kan mahaifinta akan batun auren mu, amma ni gashi har yanzu na gagara fahimtar da daddy. Na rasa yanda zanyi na fahimtar dashi wlh". Ya karasa maganar yana dafe kai.

Ashraf yace "Muhseen, ni kaina naje na sameshi mun zauna munyi magana nayi kokari na shawo kansa. kaima dole ka dage ka cigaba da masa magiya ko zai samu ya sauko. Yanzu fushi ba naka bane".

"Toh me kakeso na ce mishi kuma Ashraf, nayi nayi ya kasa fahimta ta, ni yanzu ma sai nake tunani akan What if he's right yanada gaskiya"

Ran Ashraf ne ya bace bai san sanda ya dakawa Muhseen tsawa ba yace "haba Muhseen! Lafiyan ka? Ya kakeso ka mayar da tunaninka irin nasa? Daddy fa tunaninsa da namu ba iri daya bane. Mutumin da yake yiwa Summy kallon kasashiya? Haba".

Muhseen ya katseshi yace "i know Ashraf, na san da wanan amma kawai maganganunsa ne sunsa jikina yayi sanyi wlh. What if nan gaba muzo muna samun matsalar haihuwar da ita?"

Ashraf shiru yayi yana kallonsa cike da takaici don yama rasa me zai ce ma abokin nasa.

****************
Washe gari da safe Daddy ya sauko kasa ya tadda Summy da Nany suna zaune a parlor suna dan taba hira.

Bayan sun gaisa daddy dubi nani yace "nani inaso ki fito da wheel chair dinan"

Gaban summy ya fadi ta dubeshi cikin sauri tace "Daddy? Me kuma za'ayi da wheel chair? Ni yaushe rabona danayi amfani da wanan abun?"

Daddy ya saki ajiyar zuciya yace "inaso muje asibiti ne a sake dubaki"

Hankali a tashe Summy tace " haba daddy ai na samu sauki yanzu. Duba fa ina iya takawa da kaina yanzu ba tare da an taimaka mun ba. ko jiya ma da Ashraf yazo dubani ai ya fada maka cewa targaden dana samu ya warke yanzu"

Daddy yayi shiru yana dubanta bai ce komai ba.

Summy ta marairaice masa tace "Daddy ko baka yarda da Ashraf bane don ya kasance abokin Muhseen?"

"A'a princess. So nake mu sake jin ta bakin wani likitan. Another opinion is not bad ai, ballantana ma yanzu da kike shirin barina ai gwanda na tabbatar da kina cikin koshin lafiya zan damka mishi ke. Yanzun haka ma na sa anyi mun bincike akwai wani national hospital dake nan cikin island ance sunada kwararun likitoci na qashi sosai, so nayi booking appointment dasu nace musu zamu zo yau".

Summy ta da'an turo baki cike da shagwaba tace "toh daddy... amma daddy kasan bana son zuwa asibiti wlh. I don't like it".

"Kiyi hakuri my princess, kema kinsa lafiyan ki shine number one priority dina i have to make sure you're okay". Daddy ya karasa maganar yana murmushi.

Haka daddy ya dinga binta da baki har ya samu ya lalabata ta amince taje ta shirya suka nufa asibitin.

Suna zuwa Asibitin, office din dr Dangora aka kaisu. Dr dangora ya tarbesu cike da fara'a ya nuna musu wurin zama suka zauna.

Bayan sun gaisa Daddy ya soma mishi bayani yace "dr, daman ya'ta ce na kawota a duba mun kafarta. Daman tun asali tanada dr dayake dubata amma yanzu baya nan yana kasan waje, toh tun lokacin daya tafi har yau bamu samu specialist daya kware kamar sa ba, shine aka mun recommending wanan asibitin akace zan samu the best orthopedist anan"

Dr dangora fuskarsa dauke da murmurshi ya jingina kansa yace " karka ji komai Alhaji, ai you've come to the right place don yanzu haka ma zan hada ka da one of my best doctors. Indai fanin daya danganci kashi ne bakada matsala, he's perfect"

Suna cikin wanan maganar akayi knocking a kofar office din, dr Dangora ya bada izini a shigo.

Turo kofar akayi hade da sallama, Ashraf suka gani ya shigo cikin office din, sanye yake cikin white shirt da tie da kuma black trousers sai white coat na doctors daya daura akai. Kafarsa sanye cikin talakma bakake, komai na jikinsa very neat. Kyakyawar fuskar nan tasa sai fidda wani annuri takeyi na musamman.

🔥Huda🔥💄Kde žijí příběhy. Začni objevovat