Chapter seventy

143 15 0
                                    

"Tun yaushe yaya, har na kusan gamawa ma, anan AKTH fa nakeyi".

"Dan Allah? Toh ai a can zamuyi conference din namu by 12 inaga, yanzu ogana nake jira su iso".

"Toh Allah ya kawo su lafiya, ya aikin naka na lagos. Kana jin dadin zamanka a can kuwa?"

"Toh ya muka iya. Garin ne babu dadi Saffah, jama'a sunyi yawa ga uban traffic but alhamdulillah yanzu tunda aiki na tafiya daidai yanda ya kamata. Daga zuwana na samu karin girma kinga kuwa sai hamdallah".

Cike da jin dadi tace "kai yaya nayi maka murna wlh, ina budurwar taka Huda".

Shiru Ashraf yayi ya kasa cewa komai.

Cike da sanyin jiki Saffah tace "Jubril yace mun kun rabu, meyasa kuka rabu yaya?"

"Hmm saffah ki bari zuwa anjima zamuyi wanan maganar, nazo nan kano i want to clear my head bana son abunda zai kuma daga mun hankali".

Murya a sanyaye Saffah tace "toh shikenan".

"Bari naje na shirya sai mu fita koh"

"Murmushi ta sakar masa tace "toh"

****************

Alhaji Safwan tsaye yake tare da matansa Mummy a parlour tana tayasa shiryawa "yanzu sai yaushe zaka dawo kenan Alhaji? i'm going to miss you so much".

Sumbatar ta yayi a goshi yace "i'll miss you too as usual, insha Allah bazan jima ba zan dawo. Kwanan nan ne meetings suna mun yawa".

Kanta ta kwantar bisa kirjinsa tace "gashi kuma Muhseen ba jimawa zaiyi a kamfaninka ba, da sai ya dinga tayaka da tafiye tafiyen nan, nifa Alhaji so nake kayi retire so that mu samu lokacin na kanmu. Kwata kwata baka zama, zirga zirgan yayi yawa".

Haushi maganganun Momy suka soma bashi don shi yasan dalilin dazai je kano ba aiki bane zai kaishi. Amma yayi shiru bai ce komai ba ya cigaba da shafa bayanta a hankali yana bata baki.

Bangaren Huda kuwa, shiru shiru bata ji duriyar Muhseen ba yasa ta mike ta nufi hanyar office dinsa, knocking tayi hade da sallama ya bada izinin shigowa.

"wow" ya fada yana kare mata kallo, yau kin shigo da wuri Huda, I didn't expect to see you this early."

Karasowa ciki tayi tana wani irin taku mai hade da salo har tazo ta tsaya a gabansa tace "yau morning lectures ne dani shiyasa nazo da wuri".

"Summy fa?"

"No na baro ta a school, courses daban daban muke da ita".

"okay".

Duban takardun da suke zube kan table dinsa tayi "yau me da me za'ayi kenan?"

"Wlh Shamsu nake jira yazo mu karasa tataunawa dashi, akwai wasu takardun ma dazai kawo mun. I think that's all for today".

"No ka manta da abu daya Muhseen kuma a matsayina na PA dinka dole ne na tuna maka". Ta karasa maganar tana murmushi tana aika masa da wani irin kallo".

"Me kenan?"

"Yau birthday din Summy".

"Wow" ya fada yana zaro ido yana shafa sumar kanshi."Kinsan na manta da batun birthday dinta. Wlh kaina ya dau chargi"

"Karka damu, a matsiyana na babbar kawarta zan rakaka muje mu zabo mata present na musamman wanda zai kwantar mata da zuciya.

"Allah koh?".

"Yes" ta fada tana aika masa da tsadaddar murmushi. "Ni nasan abunda takeso kuma baza'a rasa a city mall ba".

"Toh shikenan shirya muje".

🔥Huda🔥💄Où les histoires vivent. Découvrez maintenant