Chapter sixty- three

123 14 0
                                    

Huda da Muhseen tare suka fito har cikin harabar gidan.

Huda tace "kayi hakuri na bata maka lokaci Muhseen, ban san ma zan tadda Ashraf a gida ba, dana san yana gida da ban zo ba. I just needed to talk to you ne wlh."

Muhseen wanda har lokacin bai daina jimamin abunda Huda tazo tayi ba yace "bakomai Huda karki damu, zan zauna nayi tunanin akan wanan maganar da mukayi, i'll get back to you".

Murmushi ta sakar masa tace "toh shikenan Muhseen, nagode i'll be waiting".

Sallama sukayi sa'anan tayi tafiyarta.

Shiru Muhseen yayi yana tunani, gabadaya kansa a daure yake, ji yake tamkar film abunda Huda tazo tayi masa.

Da kyar ya iya shiga motarsa yaja ya bar harabar gidan ya nufa makaranta wurin Summy.

Yana isa makaranta daidai gaban department dinsu ya hangota tsaye sai faman duba agogo takeyi, fuskarta cike da damuwa.

Cikin sauri yayi parking motar ya fito ya karasa zuwa inda take yana bata hakuri yace " baby i'm so sorry dan Allah kiyi hakuri".

Cike da damuwa Summy ta soma tambayarsa abunda ya faru.

Gabansa ne ya fadi ya soma tunanin me zai ce mata yace, amma sai yaga gwanda kawai ya fito filli ya fada mata abunda ya faru, don baya so ya kasance akwai wani boye boye tsakaninsu, shiyasa yace"eh toh, Na tsaya magana da Huda ne".

From nowhere sukaji ana fadin "wato Huda ce tasa ka shanya budurwan taka ko?"

Tare suka juyo suka ga Asta tsaye a gefe tana aika musu da wani irin shu'umin murmushi. Ashe daman tun dazun tayi labe a gefe tana sauraron abunda suke fadi. Bata jira taji mai zasu ce ba ta tabe baki tana girgiza kai tayi tafiyarta.

"Wacece kuma haka?" Muhseen ya tambayi Summy.

Summy tace "kawai shareta habibi, wata yar ajinmu ce, haka take da neman magana".

Muhseen yace " toh Zo mu tafi baby, kin jima fa a tsaye".

Tare suka karasa inda yayi parking mota, Summy ta soma tambayarsa abunda ya faru. Muhseen ya sake bata hakuri yace "Baby dan Allah kiyi hakuri na saki jira akan wanan abun".

Summy tace "No habibi I totally understand wlh. Taimakon kawata ka tsaya yi ai. Bakomai"

"I'm not sure baby, amma gaskiya ya kamata Huda da Ashraf su samu su sassanta kansu, don ban taba ganin hankalin Ashraf a tashe kamar na yau ba. Zan samu na zaunar dashi muyi magana, gaskiya they need to settle this".

"Oh Allah Huda". Summy ta fada tana dafe kai.

"Wlh wanan lamarin nasu abun dubawa ne, Amma kinsan dalilin dayasa suka rabu kuwa?"

Shiru Summy tayi tana sunkuyar da kai.

"Dan Allah ki fada mun, please".

"Eh toh, abun anan shine Huda tana tunanin Ashraf ya boye mata financial status dinsa, bai fito fili ya fada mata ga yanda yake ba."

Cike da mamaki Muhseen yace "Ashraf din?! Kai inaaaa... Ashraf ba haka yake ba"

"Toh nima dai haka na gani".

Tare suka karasa shiga cikin mota, Summy tace "yanzu ya kuka kare da ita"

Nan Muhseen ya kwashe duk abunda Huda ta fada mishi ya fada mata.

Summy kanta a daure tace "yanzu so take tayi aiki tare da kai a company din kawun naka ko meye?"

"Eh wai so take ta biyani kudin taimakon dana musu".

🔥Huda🔥💄Wo Geschichten leben. Entdecke jetzt