Chapter twenty- nine

246 26 2
                                    

Suna is kofar gidansu Summy, Muhseen yayi parking motarsa.

Sai daya d'anyi jimm tukuna ya juyo yana dubanta, daman yayi noticing yanayinta tun a gida gabadaya sai a hankali.

Kuma yasan ba komai bane illa she's self conscious akan situation dinta.

Don haka hakuri ya soma bata yana fadin"Baby I'm so sorry akan yanda daddy yayi reacting dazu. Ni kaina I don't know why he behaved that way. Amma i'm so sorry please, Kiyi hakuri".

Cike da sanyin jiki tace mishi "karka damu habibty, babu komai ai. I understand".

"Muhseen yace, yauwa Baby. That's why i love you. Kinada hakuri da fahimta sosai".
Haka Muhseen ya dinga bata hakuri har ta samu ta d'an saki jiki ta sauko sunata hira kamar babu abunda ya faru. Sai da suka taba hira na kusan 20 minutes sa'anan sukayi sallama ta shiga cikin gida.

Summy tana shiga daki tayi tunanin ko ta kira Huda ta fada mata abunda ya faru amma sai ta canza shawara tace idan sun hadu a school washe gari zata fada mata.

Washe garin kuwa a school, bayan sun gama lectures na rana sun fito tare kenan. Suna cikin tafiya, Summy ta dubi Huda tace "Huda, jiya fa Muhseen yazo munje gidansu ".

Cikin sauri Huda ta dago tana dubanta, don a tunaninta, Summy ta d'au shawaranta bata je gidan ba a jiyan. Nan take taji wani irin haushi ya turniketa, amma a filli tayi kokari ta dane bata nuna mata ba tace .

"Au kinje kenan. Ina munyi dake bazaki je ba".

Ajiyar zuciya Summy ta sake sa'anan tace "wlh babu yanda na iya ne, don I've already made up my mind nace bazani ba, amma daya zo kawai ya dinga bina da baki har yayi convincing dina muka je. Amma baki san me ba Huda. Dana sani na d'au shawaran ki don bakiga irin embarrassment din danayi facing ba a gidan nasu".

Huda kuwa kamar tana jira tace "ai daman na fada miki, da kin fada mishi you're not ready, amma kinqi. Ai gashi nan, abunda naketa miki gudu ya faru".

Jikin Summy ne ya kara yin sanyi tace "Allah Huda i was so embarrased bakiga kallon da aka dinga mun ba, musamman kawun nashi. Kwata kwata he's not happy, ni gani nakeyi kamar baya amana da soyayyar tamu".

Huda ta dubeta tace "shi Muhseen din fa meya ce?"

"Ai Muhseen kema kinsan babu ruwansa, ya nuna mun cewa duk wanan abun bai damesa ba. Yana sona a hakan da nake".

Huda tace "toh shikenan ai, tunda yace yana sonki a hakan ai babu wata matsala. Ki kwantar da hankalinki kinji kawata. Everything will be fine bi izinillah".

Haka Huda ta dinga binta da baki tana kokarin kwantar mata da hankali kamar da gaske.

Suna cikin wanan maganar sai ga Halima nan ta karaso inda suke, bayan sun gaisa ta fuskanci Huda fuskarta babu walwala tace "Huda kinyi magana da Auwal kuwa?"

Huda ta b'ata fuska tace "Maganar me kuma zanyi dashi?".

"Ina akanki ne yayi fada da abokinsa bello a wajen dinner, shekaran jiya".

Huda ta tabe baki tace "oh Wow, Ai ban sani ba. Daman saboda ni ne sukayi wanan fadan?" Ta karasa maganar tana murmushi.

Haushin maganar Huda Halima taji tace "au ke dadi ma kikeji? Wato ko ajikinki, ganin kikeyi birgewa ne don sunyi fa'da akanki? Kinga dukan mutuwan da Bello yayi wa Auwal kuwa? Har rasa aikinsa fa Auwal yayi a sanadiyar wanan fadan".

Summy dake tsaye tana jinsu tace "Subhanallah, amma Bello bashida imani. Yana abu kamar mai ta'buwan hankali wlh. Duba ranan abunda yayi kokarin yiwa Huda".

Huda tayi sauri ta capke tace "kwarai kuwa, kuma kinsan waye yazo ya ceceni daga hanunsa?"

Halima tace "a'a"

🔥Huda🔥💄Donde viven las historias. Descúbrelo ahora