Chapter Three

634 57 0
                                    

Tana cikin wanan tunanin sai sukaji muryan wani babban mutun yana waya yana saukowa a hankali daga saman matakala.

Wayace dafe a kunnenshi yana magana cikin harshen turanci daga bisani ya katse kiran ya karaso cikin fallon fuskarsa dauke da murmushi.

Summy na ganinshi cike da murna ta taso ta soma fadin "oyoyo daddy, harka dawo?ai ban ma san kana ciki ba, kuma fa ban jima da dawowa ba shine nani ko ta fada mun kana ciki?" ta karasa maganar cike da shagwaba.

Dariya yayi yana fadin "princess kenan, ai bama zama nazo yi ba, yanzu haka ma da kika gani fita zanyi. Munada meeting a office ana jirana".

" Toh shikenan daddy sai yaushe zaka dawo?" Ta tambayeshi.

"Sai zuwa anjima idan mun kammala meeting din da wuri." Ya bata ansa.

Duk wanan maganar da sukeyi Huda na zaune sai faman binsu takeyi da kallo cike da sha'awa. Ji takeyi dama itace takeda mahaifi haka irin na Summy.

Summy ce ta nuna ta tana fadin " daddy ga aminiyata Huda ta school da nake yawan baka labarinta. Yau kaga tazo har gida zamuyi nazarin karatunmu tare." Ta karasa maganar fuskarta dauke da murmushi tana duban huda.

Huda cike da girmamawa ta gaisheshi, Alhaji lawal ya ansamata fuskarsa dauke da fara'a. Kana ganinshi kamar an tsaga kara an karya saboda tsabagen kamanin da summy takeyi dashi. Alhaji lawal ya dan manyanta don kallo daya zaka mishi kasan shekaru sun dan ja mishi.

Bayan sun gaisa yace shi zai wuce wajen aiki, sukayi sallama Summy ta raka shi har wajen mota sa'anan ta dawo cikin fallon tazo ta zauna kusa da Huda. Huda ce ta dubeta tana fadin " Gaskiya daddy yana ji dake Summy. Kefa kin samu gatan komai a rayuwa. Ga baban gida irin wanan, ga kuma mahaifinki kin samu yana biya miki dukan bukatunki na rayuwa.

Dariya kawai summy tayi tana fadin " Huda kenan, ai daddy daman haka yake. Yawanci lokuta ma zaki gani bai cika zama ba saboda yanayin aikinsa. Amma kullum zaki ji yana fadin idan nayi aure na tafi na barshi bai san yanda zaiyi ba"

Dariya sukayi tare, Huda tace " yauwa yama maganar muhseen da kika soma gaya mun dazu, ya kuke dashi ya soma miki maganar aure ne wai?"

"Eh toh bamu fara wanan maganar ba kinsan nidashi har yanzu bamu taba haduwa ba, sai dai hotuna da muke turawa junanmu. Huda tun lokacin da muhseen ya turo mun da friend request a intagram muka soma magana dashi naji gabadaya banida wata sauran tunani sai nashi, Huda ina bala'in son muhseen. He's very matured kuma yanada hankali sosai. Allah Allah nakeyi nida shi mu hadu na ganshi a zahiri."

"Allah ko kawata?Yanda kike ta faman wasa muhseen dinan nima zan so na ganshi, naga wanda ya tafi da zuciyar aminiyata haka" huda ta fada tana dariya. Itama summy dariya tayi ta mike tace        " taso muje sama zuwa dakina".

Huda ta mike ta bi bayanta suna hira suna haurawa matakallan da zai sadasu zuwa sama " amma summy daddynki ya san da batun muhseen kuwa?" Huda ta tambayeta a lokacin da suke kokarin shiga cikin dakin summy. Suna shiga, Wani irin sanyi AC da kamshi ne taji ya ratsa jikinta ta samu wuri ta zauna a kujeran dake dakin. Ta fara bin ko ina da kallo.

Summy ce ta bata ansa da " na dai soma fadawa daddy batunshi, baki ma san meye ba, ashe ma sun taba yin business da uncle din muhseen don ina fadawa daddy cikakken sunanshi yace ai ya san sunan family din kuma ya taba business da kawun muhseen din."

"Toh ai kawunsa daban, shi mahaifin Muhseen din fa?" Huda ta tambayeta.

"Ai Muhseen zan iya cewa kamar ni yake, don iyayenshi tun yana karami suka rasu, tun daga lokacin kawunsa ya daukeshi kuma a hanunsa ya girma."

"Ayya, Allah sarki Allah ya jikansu" Huda ta fada tana dubanta.

"Ameen, ai kawun nashi tamkar mahaifi yake a wajenshi, don shi ya dinga kula dashi har ya kawo haka yanzu, harta dukiyar da mahaifinsa ya mutu ya bar mishi da companies duk kawunsa ne ya dinga kular masa dasu, bayan muhseen ya girma ya danka masa komai a hanunsa, don shi yake tafiyar da komai a yanzu haka, dukda dai yana can japan din amma still komai na tafiya masa daidai. Kinga ma hoton da suka dauka a hongkong, dazu ya turo mun  shida abokanansa sun fita shakatawa " summy ta fada tana nuna mata wayarta.

🔥Huda🔥💄Donde viven las historias. Descúbrelo ahora