Chapter fourty-nine

197 19 4
                                    

Bangaren su Ashraf kuwa, sun fito daga cikin theatre kenan shida da dr Dangora don har sun gama emergency operation din.

Sanye yake cikin kayan likitoci na shiga theatre green riga da wando. Ba karamin wahala suka sha kan patient din ba don gabadaya a gajiye yake, gashi tunanin Huda da abunda ya faru dazun sun gagara barin kwakwalwarsa.

Suna tsaye dr dangora ya soma masa godiya yana jinjina masa yace "Ashraf abunda yasa na kiraka kazo ka taya mu da wanan operation din ba komai bane don ina so na gwada kwarewan ka da kuma kwazonka, don haka congratulations naji dadin abunda na gani cikin threatre yau". Dr Dangora ya karasa maganar yana murmushi yana mika masa hannu.

Ashraf ya rasa ma abunda zai ce, ya soma bin dr Dangora da kallon mamaki sa'anan ya mika masa hannu.

Dr Dangora ya cigaba da fadin "today you have proven that i can always rely on you. You're a magnificent surgeon Ashraf. Kuma Daga yau, na kara maka girma ka zama assistant surgeon dina, duk operations kai zaka dinga tayani yinsu".

Wani irin dadi da farin ciki ne ya lulube Ashraf nan take ya soma yi masa godiya yana kara godewa Allah.

Dr Dangora yace mishi babu komai ya cigaba da kokarinsa.

Duk maganganun nan da sukeyi, dr Abdul yana tsaye a gefe yana kallonsu. Bayan dr Dangora ya tafi, ya karaso inda Ashraf yake yana tambayarsa ya surgery din.

Ashraf yace "lafiya lau Alhamdulillah. Komai ya tafi yanda akeso. Patient din yana cikin koshin lafiya".

Dr Abdul yace "toh masha Allah yayi kyau. Yauwa Ashraf dazun fa da rana Huda tazo tana nemanka, naga gabadaya kamar bata cikin nutsuwa hankalinta a tashe yake. Ko ka ganta?"

Ashraf ya saki ajiyar zuciya cike yace "eh na ganta".

"Da fatan dai komai lafiya?" Abdul ya tambayeshi.

Ashraf yace "ina fa lafiya Abdul, zuwa tayi ta cimun mutunci a gaban mutane".

"Huda din? Toh me yayi zafi haka?"

"She broke up with me wai don akan banida kudi, da tanai mun kallon millionaire".

Abdul ya soma kallonsa cike da mamaki yace "daman saboda kudi take tare dakai?"

"Kwarai kuwa Abdul, saboda kudi take tare dani ni kuma ban ankara ba kamar wani shashasha na fada tarkon sonta!" Ashraf ya karasa maganar yana hucci cike da zafin rai.

Abdul yace "toh fa, yanzu ya zakayi kenan?"

"Wlh bansan inda zansa kaina ba Abdul, ko Muhseen ma bansan taya zan soma fada masa wanan maganar ba, kuma I don't think this is the right time for me to tell him"

"Gaskiya kam tunda kace wace zai aura aminiyarta ce sosai".

Ashraf yasa hannu daya ya dafa kansa dake masa wani irin sara yace "duk laifina ne Abdul, nine nayi encouraging dinta har tayi tunanin cewa inada kudi"

"Toh taya kayi encouraging dinta?"

"Tun farko ya kamata ace nayi mata clarifying cewa banida kudi, class dina ba daya bane dana Muhseen, ko ranan ma da muka fita na kaita wanan restaurant din, kamata yayi na fada mata cewa Muhseen ne ya biya kudin wurin bani ba".

"Ashraf naji bakayi mata clarifying ba amma still ba wai hakan yana nufin kayi mata karya ko ka yaudareta kamar yanda take kirari bane ai".

"No still Abdul in a way, i did deceive her and i made a fool out of myself saboda deep down nasan yanda take and i still let things happen. Yanzu na rasa yanda zanyi don har yanzu son Huda na nan fal cikin zuciyata na kasa cireta.

🔥Huda🔥💄Where stories live. Discover now