Chapter Thirty

259 28 5
                                    

Duk maganganun da Huda ta tsaya tana gayawa Auwal a kunnen Ashraf wanda tun dazun yake tsaye a bayanta yana sauraronsu.

Juyowan da zatayi kenan suka ci karo ta dago tana dubansa.

Idanun Ashraf kyam a kanta yace " ya lafiya naji kinata masifa haka?".

"Wlh Auwal ne ya takura rayuwata shine nake masa warning ya fita daga harkata".

"Toh meye matsalar sa?" Ashraf ya tambayeta.

"Waya san masa. Kasan shekaran jiya da muka je dinner dinan dambe ya kamayi da abokinsa a kaina"

Ashraf ya dan girgiza kai sa'anan yace " Huda kenan, naga alama masu sonki suna dayawa a makarantar nan".

Huda ta dan dubeshi tace "eh toh amma duk basu gabana. Shiyasa nake ja wa Auwal kunne daya daina mun shishigi cikin rayuwata, bana so, ban aikeshi ya dinga defending dina ba. wanan aikin saurayina ne".

Ashraf murmushi yayi yana dubanta sa'anan yace " toh waye wanan saurayin da ni ban san dashi ba?"

Huda ta d'an dubeshi da dara daran idanunta tace "well, nazata akwai wani abu tsakanina dakai but if that's not the case. Kowa sai..."

Ashraf yayi saurin katseta yace "off course akwai wani abu tsakanina dake mana. Kawai dai ina so naji daga bakinki ne. Kema kinsan Ina sonki Huda, i really do love you. Kuma i hope you'll allow me to prove it to you". Ya fada mata yana kallon cikin kwayar idanunta.

Murmushin jin dadi Huda ta sakar masa, zuciyarta pal da murnan jin kalamansa. Wani irin dadi ne taji yana ratsa duk ilahirin jikinta dataji ya ambato cewa yana sonta.

A hankali ta bude bakinta ta ce masa "i love you too Ashraf. Nima ina sonka".

Wani irin dadi shima Ashraf yaji ya ratsa shi. Ji yake kamar an masa babbar kyauta. Because he still can't believe cewa kyakyawar yarinya kamar Huda zata amince tace masa tana sonsa, though shima yasan shi kanshi babu laifi yanada kyau, kyaun da ko wace mace ce ta ganshi sai taso ta sake kallonsa, amma he still can't believe it.

Tare suka soma tafiya suna hira cike da so da kaunar junansu. Ashraf ya dubeta yace "tare da abokina fa Abdul muke, shi cardiologists ne kuma ya kware a fanin ciwon dake damun zuciyan d'an Adam, ni kuma kinsan a fanin qashi na kware, so tun ranan nayi kishi magana akan ciwon dake damun Amminki shine yau muka zo tare zai dubata."

Huda taji dadi sosai tace "toh babu matsala, sai muje gida yanzu a dubata. Bari na kira yayata na sanar da ita."

Wayarta ta ciro daga cikin jaka ta soma dialing number Ammabuwa, bugu daya ta dauka hade da sallama. Nan Huda ta soma mata bayani akan zasu zo gida da likita a duba Ammi.

Ammabuwa tace "toh shikenan sai sunzo.

Huda da Ashraf tare suka karasa wajen mota, nan suka tadda Abdul yana zaune cikin motan yana jiransu.

Gaisawa sukayi da Huda sa'anan ya tada mota suka kama hanyar gidansu Huda.

Suna isa gidan Huda ta fara shiga ciki ta sanar dasu Ammi sa'anan ta sake fitowa ta shigo dasu.

Ammi na kwance akan katifa, Abdul ya karaso da kayan gwaje gwajensa na likita ya ajiyesu gefe.

Bayan sun gaisa ya soma yiwa Ammi tambayoyi akan yanda takeji. Ammi ta zayane masa duk yanda takeji.

Nan ya soma mata gwaje gwaje da kayan aikin daya zo dasu. Sai daya dubata na kusan 30 minutes tukuna ya dauko hostler ya mika mata yana fadin " hajiya akwai wasu tests ta zan sake miki amma sai nan gaba, wanan hostler din dazan baki yanzu zaki dinga amfani dashi a ko wani lokaci don shi zai dinga gwaji yana saita yanayin hawan jininki".

🔥Huda🔥💄Donde viven las historias. Descúbrelo ahora