Chapter Fifty-two

154 21 0
                                    

Ashraf yana isa gida ya tadda Muhseen zaune a parlour. Shima wuri ya nema ya zauna yana sauke numfashi don gabadaya a gajiye yake.

Muhseen ya dubeshi ya soma tambayarsa ya jikin Ammi.

Ashraf yace "jikinta da sauki Alhamdulillah".

Shiru yayi sa'anan ya cigaba da fadin "Muhseen kudin daka kashewa su Huda yau a asibiti inaso ka kara akan bashin da kake bina da".

Wani irin kallo Muhseen ya watsa mishi sa'anan yace "Haba Ash, ya kake irin wanan maganan ne?

"Kiranka fa tayi ta daura maka wanan nauyin, gaskiya hakan baiyi mun ba. bana so".

"Wai kaga nayi complain ne? Taimako ne fa kawai Ashraf ba wai wani abu ba".

"Na sani Muhseen, I know. Amma koma dai meye ni ya kamata na dinga daukan wanan nauyin ba kai ba".

"Toh shikenan, idan kanaso ka fada mata cewa ka biyani kudin taimakon danayi musu, fine go ahead. Bazan hanaka ba".

Ashraf ya girgiza kai yace "ba haka bane Muhseen. Bazaka gane ba, Amma insha Allah zan biyaka nan bada jimawa ba. kaga yanzu na samu aiki mai kyau inayi ballantana ma yanzu da Dr dangora ya kara mun girma yace na zama assistant surgeon dinsa kaga komai zai dinga zuwa mun da sauki. Kudi zasu dinga shigo wa insha Allah".

Muhseen yayi murmushi yace "masha Allah. congratulations abokina ina tayaka murna wlh. Allah yasa albarka".

Ashraf yayi murmushi ya ansa da Ameen daga bisani suka dauko wani chapter na daban suka cigaba da hira a tsakaninsu.

**************

Washe gari da sassafe Ashraf ya nufa asibiti don tun kafun shida ya baro gida yana gudun karya tadda traffic akan hanya.

Yana isa straight dakin da aka kwantar da Ammi ya nufa. Sallama yayi ya shiga dakin.

Da Huda ya soma cin karo tana kwance akan two seater dake gefen dakin ta da'an lulube jikinta da gyale.

Tsayawa yayi ya tsura mata ido yana kallon kyakyawar fuskarta tana baccinta hankali a kwance kamar batada wata damuwa.

Muryan Ammi ce ta farga dashi daga kallon dayake mata. Kunya ce ta da'an lulubeshi ya soma sosa kai har ya karaso inda Ammi take kwance.

Ammi tana murmushi tace "harka karaso doctor?"

Ashraf yace "na karaso Ammi. Ina kwana an tashi lafiya? Ya jikin? Da fatan dai jikin da sauki yanzu?"

Ammi tace "Alhamdulillah Ashraf. Jiki da sauki nagode".

Temperature dinta ya soma dubawa, Ammi tace "Ashraf naga alama har yanzu kana son Huda baka cireta a ranka ba".

Murmushi kawai Ashraf yayi bai ce komai ba ya cigaba da dubata.

Ammi ta dan nesa sa'anan ta cigaba da fadin "karka damu Ashraf, jiya na zaunar da ita munyi magana sosai kuma tayi mun alkawarin cewa insha Allah zata canza. Nima ban fidda rai ba, ina ji a jikina insha Allah zata canza".

Ashraf yayi murmushi yace "toh Ammi, Allah yasa. Kin karya kuwa? Ya kamata ace kin sa wani abu a cikinki don ki samu kisha magunguna".

Ammi zata bashi ansa kenan, Huda ta farka. Tana ganin Ashraf a dakin ta mike cikin sauri tana fadin "Ashraf me kazo yi anan?"

Ashraf ya dubeta na ya'an sekoni sa'anan yace "ai anan nake aiki Huda. Ko kin manta?"

Huda ta dawo da dubanta ga Ammi cike da damuwa tace "wani abun ne ya sameta?"

Ashraf yace "a'a kawai nazo na duba yanayin jikinta ne".

Shiru Huda tayi bata sake cewa komai ba.

🔥Huda🔥💄Donde viven las historias. Descúbrelo ahora