Chapter twenty- five

274 21 1
                                    

Auwal yana isa wurin da akeyin order din drinks still idanunsa na kan Huda, gani yayi ita da Summy sun mike sunyi hanyar waje.

Bafi minti goma ba sai gasu nan sun dawo amma wanan karon basu kadai suka shigo ba.

Wani irin mumunar faduwar gaba ne ziyarci zuciyar Auwal dayaga Huda ta shigo tare da Ashraf, ita kuma Summy tare da Muhseen.

Kasa tsayuwa yayi da kyau yayi saurin dafe kujeran dake kusa dashi. Hudan shi ne yake gani tare da wani? Ai daya san zai ganta tare da wani da bai mayi kokarin zuwa dinner dinan ba.

Su Huda tare suka karasa wurin table dinsu suka zauna, Muhseen ya zauna kusa da Summy, shi kuma Ashraf ya zauna kusa da Huda.

Ashraf sanye yake cikin blue kaftan hade da hula dayayi matching din kaftan dinshi, shi kuma Muhseen yana sanye da kana nan kaya, Sunyi kyau sosai kamar wasu couples suka soma hira suna dariya tsakaninsu.

Jubril ne ya karaso table dinsu, nan Huda tayi introducing din Jubril wurin su Ashraf.

"Barkan ku da zuwa". Jubril ya fada musu yana mika musu hannu suka soma gaisawa fuskarsa dauke da murmushi yace " kuyi hakuri nazo nayi interrupting dinku amma i'm confused ne akan table distribution dan Allah Huda ko zaki dan bani minti kadan muyi sorting out din abun?"

Huda tace babu komai, nan ta mike tacewa su Ashraf tana zuwa sa'anan tabi bayan Jubril suka tafi.

Huda tana tafiya, Muhseen ya dawo da dubansa ga Summy yana fadin " Baby what's wrong? Meke damunki naga tunda muka shigo kamar you're not yourself. Wani abun ne ya faru?"

Summy tayi sauri ta girgiza masa kanta. Ganin Ashraf yana wajen, kuma suna cikin jama'a ne yasata yin shiru bata dauko maganar da sukayi da daddy ba.

Muhseen ajiyar zuciya ya sake sa'anan yace " Baby daman inaso na kaiki gida ku gaisa da Mommy, matan kawuna. Inata bata labarin ki shine tace tana son ganinki na kawo ki gida ku gaisa." Ya karasa maganar yana murmushi yana kallon cikin kwayar idanunta.

Gaban Summy ne ya yanke ya fadi jin abunda ya fadi, don tsoro takeji, bata san wani irin tarba family din nasa zasuyi mata ba.

Kokari tayi ta danne abunda ya taso mata ta kirkiro murmushi bisa fuskarta tana fadin " babu komai habibi. Duk yanda kace".

"Toh gobe yayi miki? Ina tashi daga wajen aiki sai na biya nazo na dauke ki mu tafi gida tare. Ko ya kika ce?"

Summy tace "haka nan ma yayi. Allah ya kaimu goben".

Muhseen ya ansa da Ameen. Sa'anan yace taho muje waje mu dansha iska. Tace toh.

Nan yayi wa Ashraf magana yace suna zuwa, Ashraf yace babu damuwa.

Mikewa sukayi tare sukayi hanyar waje.

Bangaren Huda kuwa tazo wucewa ta hango Asta zaune ita kadai ta zabga uban tagumi.

Murmushin mugunta Huda ta kirkiro a fuskarta ta karaso inda Asta take zaune ta soma fadin " yau kuma ina khalid din, ko har ya gaji dake ne ya kyale?"

Wani irin kallo Asta ta watsawa Huda tana hararanta tace " ina ruwanki?"

"A'a mayar da wukan, daga tambaya
kuma?"

Tsaki Asta taja bata sake ce mata komai ba.

Huda ta rungume hanunta bisa kirjinta tace " kinga wanda nazo dashi dinner dinan kuwa?" Ta tambayeta tana nuna Ashraf dake zaune can wurin VIP section yana danne wayarsa.

Asta tana ganin Ashraf ta kara harzuka taji wani irin kishi ya taso mata, Zata bata ansa kenan, sai ga Auwal nan ya karaso inda suke hade da sallama.

🔥Huda🔥💄Donde viven las historias. Descúbrelo ahora