Chapter Eighty- six

173 17 2
                                    

Bangaren su Huda kuwa, da kyar Muhseen ya samu ya banbareta daga jikinsa ya shiga rarashita, tace sai ya daukan mata alkawarin zai fasa aurensa da Summy ya zaba cikin su biyu don bazata iya rayuwa babu shi ba, Muhseen kansa a cike ya rasa yanda zaiyi da ita daga karshe dai yace mata karta damu gobe da safe zai kirata suyi magana duk yanda ake ciki zai sanar da ita da kyar dai ya samu ta hakura ya kira mata uber ta tafi gida.

Tana tafiya ya zauna yayi shiru yana tunanin abunyi, tunaninsa duk a hargitse ya rasa inda zai sa kansa, daga karshe dai ya yankewa kansa shawaran barin garin gabadaya, zaije Abj yayi koda kwana biyu ne ya samu ya saita kansa ana gobe daurin aure sai ya dawo. Da wanan ya mike ya shige da'ki ya soma neman Summy a waya ya soma sanar da ita batun tafiyan nasa. Hankalin a tashe tace "haba habibi.. yanzu ana tsakiyar bikin namu zakayi tafiya? Duka duka kwana nawa ya rage a daura mana aure? Kuma gashi jibi fa munada dinner".

Muhseen yace " noo baby ba haka bane kwana biyu kawai zanyi na dawo. kuma tafiyan nan da zanyi saboda maganan visan mune, inaso da zarar an daura mana aure zan daukeki muyi tafiyar mu, kuma kinga inba naje da kaina ba bazan samu su kammala mana da wuri ba." Sosai ya shiga kokarin kwantar mata da hankali yace insha Allah jibi ana kammalawa zai dawo, kuma batun dinner dinsu babu matsala, ana iya shifting dinsa bayan daurin auren sai ayi. Nan ne hankalin Summy ya da'an kwanta tace toh amma ya tabbatar yana gamawa ya dawo, yace mata karta damu.

Washe gari Huda shiru shiru tasa ido tana sauraron kiran Muhseen amma bata gani ba, ta shiga neman layinsa taji a kashe jiki babu kwari ta mike ta soma shirya zuwa school tun daga uwar da'ka take jin muryar Ammi na fa'dawa Ammabuwa karta kuskura ta sake bata kudi koda da wasa ne, tunda abun nata babu mutuncin bata san zafinsu ba itama ta dage ta nema na kanta.

Hankalin Huda ya tashi jin abunda Ammi take fad'i don tasan idan Ammabuwa ta yanke mata kudi yanzu bata san inda zata dinga samu ba.

Ammabuwa dayake sauri take zata fita bata ja maganar da tsawo ba ta dau jakarta tacewa Ammi sai ta dawo. Ammi tayi mata addu'a a dawo lafiya. Sai lokacin Huda ta fito cikin parlourn ta sami Ammi tace "Ammi naji abunda kika fada'wa Ya Ammabuwa".

Ammi ta juyo tana fuskantarta ranta a bace tace " yess kindai ji da kyau abunda na fadi. Kuma babu wasa cikin maganata Huda daga yau na yanke duk wani kudin da zai kuma shigo miki daga gidan nan, kema Ki da'ge ki nema na kanki Tunda abun naki naga gaba gaba yake bakida hankali baki san me kikeyi ba har yanzu kin kasa gane cewa rayuwa batada tabbass, mu talakokine amma hakan bawai yana nufin zamu dauki kanmu mu kai inda Allah bai daura mu bane. Huda ba'asan gawan fari ba amma ina bakin ciki ace na mutu na barki kina cikin wanan halin.Sosai Ammi ta shiga mata fa'da Huda tana tsaye tana jinta amma babu magana da'ya dake shiga kunnenta har Ammi ta dasa ayarta tace toh taji zata kiyaye ta dau jakarta tace su Auwal na jiranta a school karta yi latti lectures. Tun a school taketa faman neman layin Muhseen amma still baya shiga don haka tana gama lectures ta wuce gidansa, tun daga gate security ya soma sanar da ita cewa oga bayanan yayi tafiya. Ta tsaya tayi shiru tana tunanin abunyi. Muhseen yayi tafiya? Toh ina yaje? Tasan tabbas saboda ita yayi wanan tafiyar. Tana tsaye a hakan sai ga kiran Summy nan ya shigo wayarta, bayan sun gaisa cike da dabara ta dauko mata batun Muhseen, nan Summy ta sanar da ita cewa baya gari yayi tafiya zuwa Abuja batun maganar visa dinsu amma kwana biyu zaiyi ya dawo.

Bayan sun gama wayar Huda tayi shiru tana nazari. Wato Abuja ya tafi kenan sai ana gobe daurin aure zai dawo. Hankalinta yayi mugun mugun tashi don tasan tabbas idan ta bari har sai lokacin ta gama rasa shi kenan don haka ta yankar wa kanta shawaran binshi Abuja, duk abunda zai faru sai dai ya faru. Tunaninta da'ya yanzu inda zata samu kudin mota tunda Ammi ta yanke mata kudin dake shigo mata yanzu, tasan bazata iya tambayar Auwal ba don shima bai dashi. Toh kodai zata gwada tambayar Ammabuwa ne koda rance ne ta bata ba tare da sanin Ammi ba. Da wanan tunanin ta wuce gidansu Summy.

🔥Huda🔥💄Donde viven las historias. Descúbrelo ahora