Chapter Seventy-one

169 20 0
                                    

Wata yar karamar yarinyar akalla bazata wuce shekara tara zuwa goma ba taketa faman tsale tsale a parlour.

Mahaifiyarta wace itama akalla bazata wuce shekara 38 zuwa 39 ba taketa faman kwada mata kira akan ta bar guje gujen da takeyi. Kyakyawar mace ce matan fara sol da ita, tana sanye cikin wata tsadadiyar less dinkin riga da zani, fuskarta dauke da casual makeup.

Yarinyar karasowa inda mahaifiyarta take ta soma fadin"Mommy waya nakeso a siyan mun".

"A'a Amal ki bari idan kin kara nan gaba za'a siyan miki waya amma ba yanzu ba".

Yarinyar da aka kira da Amal ta turo baki cike da shagwaba tace "nidai gaskiya momy yanzu nakeso a siyan mun. Idan Daddy yazo zan fada mishi. Duba kawayena su hafsa duk daddynsu ya siya musu waya amma banda ni".

"Nidai na fada miki ki bar zancen wayan nan Amal. Kinga fa banason gardama. Ko yayanki ma Jubril haka kika sashi a gaba akan batun waya."

Amal zatayi magana sukaji anyi sallama an shigo parlourn. Tana ganin wanda ya shigo ta mike a guje tana fadin "Daddy oyoyo! Daddy oyoyo!" Taje ta fada jikinsa.

Cike da farin ciki Alhaji Safwan ya dauki diyar tasa ya rungumeta tsam a jikinsa yana fadin "oyoyo Amal dina."

Mahaifiyar yarinyar mai suna Maimuna itama tazo ta rungume shi tana fadin "oyoyo habibi, barka da zuwa. Tun dazun muka zuba ido muga shigowanka, ga yar'ka nan sai faman mun rigima takeyi tana sani surutu".

Juyowa yayi yana duban Amal yace "Amal meyasa kike wa mommynki rigima?"

Boye fuskarta Amal tayi da tafin hannunta tana dariya. Alhaji Safwan ya girgiza kansa yana dariya suka karaso cikin parlourn a tare ya zauna akan daya daga cikin three seater's na kujerun ya daura Amal a kafansa ya juyo yana duban matar nasa yace  "wlh na iso tun dazun, mun tsaya da Jubril ne acan Naibawa muna tattaunawa akan aikin project din dana sashi".

Maimuna tace "nima Dazun nayi waya dashi yace mun yana can. Amma anjima zai dawo". Tana gama fadin haka ta Mike taje fridge ta debo ruwa da lemu mai sanyi sa'anan tazo ta jera su a gabanshi tanai mishi sannu.

********************

Bangarensu Summy kuwa tsaye take a gaban department hankalinta a tashe don tun dazun take expecting Muhseen ya kirata amma shiru babu alamun kiran nasa. Halima ce ta fito daga cikin aji ta tada ta a hakan tace "yadai Summy Kodai Muhseen din kike jira har yanzu?"

"Wlh Halima shi nake jira, ya saba kirana by this time yaji kona gama lectures yazo yayi picking dina amma har yanzu shiru".

"kilan aiki ne suka mishi yawa amma kidan jira ko kuma ki gwada kiransa mana."

"Tun dazun naketa gwada kiran nasa amma baya picking".

Suna cikin wanan maganar sai ga saurayin Halima khalid nan ya karaso yana fadin "baby taho muje mana tun dazun fa naketa jiranki".

Halima ta juyo tana duban summy tace "Sorry summy nidai zan wuce yanzu. Sai zuwa gobe kenan". Sallama sukayi sa'anan ta wuce ta bar Summy tsaye zuciyarta cike da damuwa.

Bangaren su Huda kuwa, tana saukowa ta tadda Muhseen wanda gabadaya duk hankalinshi ya gama tashi, yana ganinta ya mike yana fadin "Huda har kin gama".

Murmushi ta sakar masa tace "na gama Muhseen." Agogon hannunta ta duba tace "laaa.. kaga har lokaci ya tafi, baka kira Summy ba. Ya kamata kaje kayi picking dinta".

Tataba aljihunsa ya somayi yana neman wayarsa amma yaji wayam wayar bata tare dashi yace "kash kamar nabar wayar ma cikin mota". Karasawa yayi wajen cashier din ya tambayeta nawa ne kudin kayan da Huda ta zaba ta fada mishi, babu musu ya ciro Atm card dinshi ya mika mata. Huda na tsaye tana kare mishi kallo aranta tace "gaskiya dazan samu Muhseen ya zama mallakina dana more, shine irin kallan namijin daya dace dani." Ajiyar zuciya ta sauke tana cizan lips dinta na kasa tace "Gaskiya Summy sai dai kiyi hakuri amma Muhseen ya rigada ya zama nawa yanzu".

🔥Huda🔥💄Kde žijí příběhy. Začni objevovat