Chapter Nine

498 34 1
                                    

Ba jima ba summy ta shigo dakin hanunta rike da wata hadadiyar jaka. Ta karaso tana tambayar huda ko jakar tayi mata, huda cike da murna ta karba jakar tana mata godiya. Ba'a jima ba suka gama shiri suka fito suka dauki hanyar murtala Muhammad international airport.

Bayan barin su summy gidan, su nani da sauran ma'aikatan gidan suka fara gyare gyaren ko ina a gidan. Sai faman goge goge da share share aketayi. Alhaji lawal ya dawo daga meeting din dayaje ya shigo yaga ko ina sai daukan ido yakeyi. Nani ya tadda wacce sai kaiwa da dawowa takeyi " toh fa hajajju wanan gyare gyaren danaga anata faman yi fa?"

Nani tayi murmushi cike da girmamawa ta gaishe shi, suma sauran ma'aikatan gidan suka gaida shi. Alhaji ya ansa musu gaisuwarsu cike da fara'a.

"Summaya fa?" Ya tambayi nani

" summaya bata nan dazu ita da kawarta huda suka tafi airport, yau muhseen zai dawo daga kasar waje"

"Oh hakane fa, jiya dadare ta soma fada mun sai kuma na manta. Toh shikenan Allah ya kawo su lafiya. Da fatan dai babu wata matsala?" Alhaji lawal ya tambayeta.

Shiru tayi na dan lokaci sa'ana tace "eh toh Alhaji, na tabbata komai zai tafi daidai in badai wancen kawartata huda zata bata mata komai ba, wlh alhaji jikina na bani cewa yarinyar nan ba tsakani da Allah take tare da mimi ba, gabadaya ban yarda da yarinyar nan ba ko kadan". Ta karasa maganar cike da damuwa.

Alhaji lawal yayi shuru daga bisani ya soma fadin " a tunanina dai babu wata damuwa don naga alamun huda tanada kirki, kuma kinga yanda summaya take sonta, kinfi kowa sanin halin summaya cewa bata cika shiga cikin mutane ba kuma bata abota da kowa saboda lalurarta. Huda kuma bata duba wanan, tana kula da ita kuma tana bata goyon baya dari bisa dari.

Nani ta dan nesa sa'anan tace "Alhaji na lura da yanayin hudan nan fa tanada son kai dayawa. Mimi ce har yanzu bata fahimce hakan ba".

Dariya kawai alhaji yayi yace "keh dai kiyi kokari ki fahimce huda don nasan yarinyar Batada matsala, ta mayar da summy tamkar yar'uwarta da suka fito ciki daya. Kuma ina jin dadin yanda sumaya take abota da ita.

Nani ta dago tana dubansa daga bisani tayi ajiyar zuciya tace " toh shikenan alhaji, Allah yasa hakan ne, kuma Allah ya tabbatar da Alkhair".

"Ameen, ki kwantar da hankalinki nani insha Allah babu abunda zai faru. Yana gama fadin haka ya haura sama.

Bangaren su summy kuwa, tun a cikin mota summy take ta faman fargaba, hankalinta duk a tashe.  Wurin arrival inda ake jiran masu tafiya suka je suka zauna suna jiran a fada isowar jirgin su muhseen daga japan. Huda ta lura da yanayin summy taga duk jikinta sai faman rawa yakeyi ta soma kokarin kwantar mata da hankali " summy karki damu, ki kwantar da hankalinki, ba abunda zai faru, kinsan muhseen yana sonki".

Summy ta dago tana duban huda cike da damuwa tace "huda kinsan har yanzu na kasa sanar da muhseen batun matsalar kafata na rasa ta yanda za ayi na fada mishi".

Huda ta zaro ido tana dubanta " ban gane ba, kina nufin har yanzu baki fada mishi ba? Meyasa summy?"

Summy ta sunkuyar da kanta tace " wlh huda bazan iya bane, manta kawai in ma mun hadu ya ganni a hakan yace baya sona, babu matsala at least dai na samu na ganshi a zahiri".

"Toh shikenan summy, Allah ya bada sa'a, zan barku ku samu kuyi magana bari naje na jiraku wajen mota. Ta fada tana kokarin mikewa.

Summy ta kamo hanunta hankalinta a tashe tana fadin"'A'a huda dan Allah karki tafi ki barni haka, kin san me, why not ki fara haduwa dashi tukuna sai ki fada mishi."

Huda tayi shuru tana dubanta " anya kuwa summy? Ayi haka?"

Summy ta gyada mata kai tace "dan Allah huda ki taimaka kinji. In kin mishi bayani ya fahimce ki, sai kuzo tare".

🔥Huda🔥💄Où les histoires vivent. Découvrez maintenant