Chapter Sixty - Five

161 19 1
                                    

"Yes kuma zan sanar da ita cewa kana kokarin ka tayata biyan bashin". Muhseen ya fada yana hucci.

"ba sai ka gaya mata ba, wanan tsakanina ne dakai. Kuma bari na fada maka Muhseen, right from time ba kai ya kamata ka dau nauyinta ba, don Huda ba taka bace!"

Ran Muhseen ne ya bace ya soma magana cikin kakausan murya yace"haka zalika kaima Huda ba taka bace Ashraf! Stop overreacting please!"

"I will overreact Muhseen! kaima kasan by chance ne ka samu kayi picking wanan kiran nata da har ya kaiga ka biya musu kudin asibi, shiyasa nace ka bari zan biyaka kudin!"

"Wai Ashraf meke damunka ne wai? What's happening to you?! Kana neman ka haukace akan wanan yarinyar!"

"What's happening is what i'm telling you Muhseen! I'm getting out of my mind because of her! I can't think straight! Bazan iya magana daya biyu akanta ba tare da raina ya bace ba!" Gabadaya hankalin Ashraf a tashe yake.

Muhseen tsorata yayi da yaga yanda Ashraf yake tada jijiyoyin wuyarsa yace "no Ash, you can't continue like this, ka bari....."

Muryan Ashraf na rawa yace "na bar me?! ya kakeso nayi da rayuwata Muhseen?! Kasan yanda nakeji kuwa?! It hurts... it hurts so much to even talk about her, I can't help it!".

Shiru Muhseen yayi ya bude baki yana kallon yanda abokin nasa duk yabi ya sauya kamar bashi ba. Bai taba ganin Ashraf cikin tashin hankali irin na yau ba. shi daya sanshi as a very reserved person mara son hayaniya sai yau gashi mace daya tak tana neman zautar dashi.

Shiru yayi tunani kala kala na masa yawo a ka daga bisani yace "Huda tace tanaso tayi aiki tare dani a kamfanin Daddy".

Zaro ido Ashraf yayi, zuciyarsa na masa wani irin mahaukacin bugu tamkar zata huda kirjinsa ta fito yace "what?! Tanaso tayi aiki tare da kai?" Dariyan takaici ya sake sa'anan ya cigaba da fadin " I can't believe this! Tanan kuma ta bullo?"

"Ashraf nifa ban yarda da wanan maganar taka ba, don nasan Huda ba haka take ba, she's nothing like you described, da tanada son abun duniya bazata zo ta tunkareni tace zata biyani kudin dana kashe musu a asibiti ba".

"Lallai Muhseen baka san dawa kake dealing ba, ni na fika sanin wacece Huda! Yanzu ma so nake nasan dalilin da yasa tace zatayi aiki da kai. Meyasa take so ta samu kusanci dakai?"

Wani irin kallo Muhseen ya watsa mishi sa'anan yace "ban gane wanan tambayar taka ba, kishi kake kokarin yi dani ne ko me? You need to calm down Ashraf and accept what happened between you and Huda, ka sani cewa kai da ita kun rabu, baku tare kuma!".

"Ba haka bane Muhseen, har yanzu ka kasa gane abunda nake kokarin fahimtar dakai a game da Huda".

A fusace Muhseen ya mike ya dauki makulin motarsa yana fadin "kaga i've heard enough, banida wanan lokacin daman zuwa nayi na canza kayan jikina, already shamsu yazo yana jirana zamuje ya gaisa da matar da zan aura, idan ka gama wanan haukan naka ka nutsu muayi magana". Yana gama fadin haka a fusace ya fice ya bar masa parlourn da gidan ma gabadaya yana hucci.

Hannu Ashraf yasa ya dafe kansa da yake masa wani irin sara tamkar zata rabe gida biyu, gabadaya tunaninsa a hargitse yake ya rasa inda zai saka ransa ya samu saukin radadin da yake ji.

**************************

Bangaren gidansu Huda kuwa, Ammabuwa ce zaune tana kokarin hada takardun da suke zube a gabanta tana fadin "amma dai wanda yake taya dr Abdul tsara accounts dinshi baiyi ba, kwata kwata baiyi filling documents din da kyau ba."

Ammi dake zaune a gefenta tana kokarin hura turaren wuta a kasko tace "toh barka dai tunda kin iya, sai ki samu ki gyagyra masa".

"Ai shi nake kokarin yi tun dazun Ammi, duk na gyagyara masa, ai dr Abdul yanada kirki sosai, abunda yafi wanan ma in har baifi karfina ba zan iya taimaka masa dashi".

🔥Huda🔥💄Donde viven las historias. Descúbrelo ahora